AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Hafiz Daya gama aka sallamesu sbd maigidan nasu Daya wuce kama hannunta yayi yaja suka bar gurin Saida sukai Nisa ta kwace hannunta tana matsowa kusa dashi sosai tace
“Yaya Hafiz Yaya sunansa?
Bature ne ko balarabe?
Suna Isa gida ta bawa babba da dadah labarin Taga irin Wanda zasu Nemo mata a matsayin miji idan zasu mata aure.
Tin daga wannan ranar Ameenatou Babu ranar da Bata maganar baturen ogansu Yaya Hafiz,
Kaf gidan saida suka gaji da Jin kalan kyansa datake fadan kaman Rana zata konasa yanata kyalli.
Haka zalika tin daga lokacin Yaya Abdul ko Babbah suna daukota daga makaranta gurin Hafiz suke ajiyeta shikuma daga Nan yaje da ita gida duk Dan sbd tagansa Amma kuma abin mamaki tin daga ranar Bai sake zuwa ba bare ma ta gansa daga qarshema sai gashi anrufe site din gaba Daya tareda aikin dole suka koma Neman wasu ayyukan kafin idan Allah yasa zaa dawo da aikin sai gashi kuwa kwatsam ance su shirya su koma bakin aikinsu Kuma me gidanma yananan tafe da kansa.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#THE SEELAHS
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
30
Washe gari Tin 7 na safe Yaya Abdul ya shirya fita aiki ya tsaya jiran Budurwar babban Amma dai lokacin ma dadah ke tadata bacci cikin lallabawa da tausayinta akan tashin safen Wanda yake kular da Hafiz Dake tsakar gidan Yana wankin kayansa Dana Ameenatou din.
Brush tafara kafin Tayo wanka ta fito ta nufi daki Dadah haryanxu data girma tayata shiri takeyi.
Sai kusan takwas saura ta gama shiryawa ta fito tsakar gidan ta zauna gefen Babbah dake zaune kan tabarma.
Farin Koko me kyau da aka zuba mata zuma aciki ta dauka a cup da fanke manya manya da zafinsu sun soyu tafara Sha tana fadawa Babbah gobe bazata je makaranta ba duk idanuwanta rage girma sukeyi Bata samun bacci gashi da Rana ma Bata samu.
Cikin kulawa da yadda da abinda ta fada din Babbah ya gyada Kai Yana cewa
“Na lura da Hakan sarai ‘yar budurwata magana ce kawai banba sbd Yan Saka idon gidan Nan Amma gobe Babu inda Zaki ai ana son Rai da hutawa”
Juyowa Hafiz yayi sbd ya Dena mamakin lamarin babbah da budurwan tasa Amma takaici Baya barinsa yin shiru Dan haka Baki sake yace
“Wlh duk ranar da kika sake tsallaken zuwa makaranta bazaki sake zuwa site ba ko oga yafara zuwa aiki kuwa,
Sai naga karshen rashin bacci.”
Kallan babbah ta dago tayi da idanuwanta da suka narke tana masa alaman yayi magana.
Inda yake babbah ya juya ya kalla Yana jifansa da wani mugun kallo yace
“Nine nace bazata goben ba sai naga abinda zakayi”
Yaya Abdul da hakurinsa ya fara karewa sbd yayi masifan lattin Danma Babu ranar da Baya latti sbd ita cikin kulewa yace
“Zan tafiyata idan Baki nutsu kin gama abinda yake gabanki ba Kokuma ki tashi mu tafi hakanan Baki gama cin abincin ba.”
Dadah Daketa Kaida kawon hada mata jakarta da ruwanta a sabuwar roban ruwa me tsafta sosai da Yaya Abdul ya sake siyo mata miqawa Abdul din dayake tsaye Yana harare harare tayi tana cewa
“Dan taimaka riqe mata kafin ku Isa”
Baida lokacin batawa na musu Dan haka ya karba kawai zai sake magana Dadah ta rigasa da cewa
“Yi hkr saura kadan fa ta gama karta qware duk Kuna Neman rikitata”
Hafiz ajiye wankinsa yayi Yana nufota Babbah ya jefesa da wani kallan daya sakashi tsayawa Yana cewa
“Babbah wai meyasa kakemun hakane duk lokacinda naso gyarawa wannan yarinyar zama duk ta renani ko abokaina fa sunsan ta renani a gabansu Babu kalan sakarcin da batamin gudun nakeyi wataran na harzika na babbalata jinin mutane yayita Hawa”
“Karka wani Sakaya fito fili kace jinina Dana uwarku ya hau,
Zaka koma aikin gabanka kokuwa saina ce Abdul din ya tafiyarsa ka aje wankin ka Kaita”
Ball yayi da takarmanta Dake gabansa Yana juyawa ya koma aikinsa Dan ba qaramin aikinsu Babbah dinne ba ace ya aje wankinsa ko wanka beyiba ya Rakata makarantar.
Miqewa tsaye tayi bayan ta gama tana goge bakinta da tsaftacciyar kyallen sabuwar atampa da Dadah ta miqo mata ta Saka takarmanta masu kyau Wanda suka Hafiz dinne ya siyo mata Dan komai nata Hafiz da Yaya Abdul ne ke Siya
Babba kuwa a siya mata kayan ciye ciye da kwalama Yan canjinsa suke karewa sai fura da asalin Madaran fulani me kyau dayake siyo mata duk dare Wanda yawanci ita take Sha Bata cika cin abinci ba sai idan Yaya Abdul ya siyo mata kwai zuwa makaranta take ci da dare.
Suna fita tana gefensa tana masa surutu suka kama hanyar makarantar Yana amsata sama sama sbd hankalinsa na kan gurin aikinsa dayayi latti gashi Basu yadda da kowaba akanta da tini mashin zai ringa Bata kudi tana Hawa Amma kwata kwata Basu yadda da kowaba akanta shiyasa duk tsananin latti da rashin jinta basa iya barinta taje ita kadai makaranta kuma itama kanta sbd sabo da Hakan Bata iya tafiya koina batareda dayansu ya Kaita ba tsoro ma takeji na bin hanya ita kadai.
Suna Isa gate din makarantar ya miqa mata kayan ciye ciyen Daya Siya mata na break Dan basa Bata kudi kwata kwata.
Karba tayi tana masa Godia da fuska a cakude sbd lattin datai tasan Kuma Yaya Abdul din Babu rokon dazaije yayi mata Dan haka ta juya ta shige tana ciko idanuwa da hawaye Dan a tausaya mata.
Cikin babbar sa’arta malamin data tarar Yana Taron lattin Baya ko kallan inda take kwata kwata sbd tashin hankalin Daya taba Sha shida Babbah da Hafiz akan dukanta Daya taba yi
Babbah yazo makarantar ya rufe ido ya zuba musu tsiya rigima har gaban shugaban makarantar kawu yayi mirsisi ya nuna Yar budewarsa Bata da laifi shine Babu lafiya shiyasa batazo da wuri ba.
Dayake sunsan ba yadda zeyiba daga Nan har hukuma Dan haka suka basa hakuri aka rufe maganar,
Tin daga lokacin da yawa malamai basa taba Ameenatoun sbd Babu me buqatan rigima kowa na fama da kansa.
Simi Simi kaman munafuka ta wuce ciki tana Jin dadi a zuciyarta Dan idan akwai abinda ta tsana a duniya shine a taba lafiyar jikinta,
Bata kaunar abinda ya taba jikinta shiyasa Sam batason duka ko faduwa bare Jin ciwo.
Idan kuwa taji ciwo a gidan jinya zata kwanta a ringa fama,kafin ta warke zuciyar Hafiz saita kumbura ta huce yafi so a kirga sbd yanafin kowa Shan wuya da takaici Dan a kansa sakarcin yake karewa.
Farin jini datake dashine ya Saka yakeda kawaye masu tsananin son binta koina Amma da Aminiyarta Daya Khadija.
Karfe biyu saura Yaya Abdul yazo ya dauketa Kai tsaye gida suka nufa ko shiga beyiba ya juya ya koma gurin aikinsa ita Kuma ta shige a gajiye duk da Yaya Abdul din ya Siya mata yoghurt me sanyi sosai yazo mata dashi Amma dai batasha ba tana shigowa ta miqawa Dadah hadda Jakarta da komai ta tube a tsakar gidan ta daura zani ta nufi bandaki Tayo wanka tana fitowa abinci kawai taci Tayi sallah ta share dakinta dana Dadah duk da fes suke Dan Dadah akwai tsafta.
Tana gamawa bacci kawai ta kwanta abinta.
Sai kusan hudu ta tashi tayi Shirin makaranta dayake Hafiz yasan lokacin gama shirinta tana gamawa Yana dawowa yace ta fito su tafi yakaita sauri yakeyi akwai inda zashi.