AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Kaman kan nata yayi daidai da Bude idanuwan Ameenatou din tareda qwacewa da sauri tana tashi zaune sedai Bata Ankara ba tayo qasa sbd bakin gadon ne take..
Sister Ashley cikin tsananin sauri tayi saurin miqa hannuwanta zata Kamota sedai kafin nata hannun ya Isa Nurse Fahat ya tare Ameenatou din da hannuwansu duka biyun harma da jikinsa Wanda ya Saka Ameenatou shiga shock da tsoron da Bata taba shiga ba ta fasa ihu me qarfi tana kwacewa tana Kiran sunan Ashley da siddeeq.
Ihunta da fizge fizgenta cikin ruwan jiki me tsanani sbd Babu Wanda ya taba kusanto kusa da ita idan ba mutum biyun Nan ba ya bawa Nurse Fahat Daman Riqeta cikin jikinsa sosai Yana hada jikinta da nasa da kyau da sunan riqeta yayi ciwonta ya tashi sosai.
Sister Ashley da sauri ta sauko tana cewa ya saketa Bata yarda kwata kwata kowa na rabarta ciwon tsanani yakeyi.
Hannuwa takai tana cireta daga jikinsa shikuma yaki sakinta sbd zuwa lokacin ihunta da fizge fizgenta ya tsananta Wanda ya saka sauran nurses Dake kusa yowa dakin da sauri harma da likitan dayake block din sbd ihun dayake tsananta ba dadin ji.
Sister Ashley ma da Bata Saba ganin Hakan daga Ameenatou ba hankalinta tashi yayi sbd duk yanda wani zai rabeta tana ihu da wannan fisge fisgen Amma na yau din yayi tsanani.
Fahat kuwa kasa sakinta yayi ya sake qanwameta jikinsa Yana cewa ayi saurin kawo allura.
Ta bangare Daya Wani irin yanayi me zafin gaske yakeji Yana yawo jininsa da jikinta Dake cikin nasa Dan kuwa Bai taba tinanin akwai mahaukaciyar Da zai taba Jin Hakan Dan ya taba jikinta ko hada jikinsa da nata ba sai yau din gashi duk da tashin hankalin qamshi ne me sanyi mara karfi ke fitowa daga jikinta Yana shiga hancinsa Dan haka sauran nurses da likita na shigowa yayi saurin sakinta sbd Ashley data sake cigaba da banbareta daga jikinsa hakama yanayinsa ya fara bayyanuwa.
Sauran nurses dinne suka taru suka kamata tareda sister Ashley sbd zuwansu gabaki Daya ya qarasa juyar da kan Ameenatou din gaba Daya ta zare bayan ihu da fisge fisge Babu abinda takeyi.
Bata cika rikicewa ba Amma idan ta rikice Sam Babu sauki ko kyan Gani a lamarinta Dan haka tin lamarin na iya yiyuwa a iya dakin dole aka danneta akan gado aka daure da belt aka turata zuwa emergency dinsu hakama Dr Dee dole aka kira aka sanar dashi Dan case dinta a hannunsa yake Shima ana sanar masa cikin gaggawa ya taho sbd irin Hakan ne idan abin ya tashi sosai idan baa sake qarasa juye kanba ta hanyar allura to zata iya dawowa daidai idan tashin hankalin ya lafa shiyasa baiyi qasa a gwiwa ba yayo asibitin hankali tashe.
Koda ya iso lamarin ya gagara Dan kuwa du inda belt yake daure da ita ta jiwa kanta mummunan rauni Dan duk ya yankata tayi jajir Kuma har lokacin Bata Dena ihu da fisge fisgenba Wanda shine ya Sakata Jin raunikan sosai.
Cikin tashin hankali yake kallan jikinta da yanayinta da Shima ya Sakasa Neman rikicewa da sauri ya buqaci suyi sauri su kawo masa alluranta me karfin gaba Daya.
Da sauri aka kawo masa tareda alluran kashe mata radadin ciwukan Dan hadda jini sosai.,
Sister Ashley kuwa hannuwanta har rawa sukeyi gurin Saka gloves ta dauko cotton balls da magani ta hada Dan goge raunikan idan an gama.
Kusan kasa yiyuwa alluran tayi duk da tana daure Saida su Fahat suka danneta su dukansu kafin Dr Dee cikin rashin tinanin illan da alluran take qara mata a duk lokacinsa aka sake yi mata ita ya soka mata cikin qwarewa tareda danna ruwan ya tsiyaye mata cikin jijiyanta take tayi wani mummunan yunquri cikin tsananin azaba da gigitanwar alluran ta fara kokarin fisge fisge amma ba qaramin karfi ne da alluran ba take gabobinta da dukkanin duk wani abu dayake jikinta kasawa yana sakewa yana mutuwa sai Alokacin idanuwanra da sukai wani irin mummunan ja suka bude ahankali daqyar sedai babu abinda take iya gani bayan dishi dishi sai kuma wasu irin hawaye masu zafin gaske da suke gangarowa ta gefe.
Sai alokacin kowa ya janye hannunsa daga kanta sbd sunsan Babu wani abu da zata sake yi Kuma.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#THE SEELAHS
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
63
Akan gadon datake dauke aka gangarota aka dawo da ita dakinta har lokacin Fahat na gurin cikeda bayyanarda kulawa da damuwa akan Ameenatou din.
Shine ya warware daurinta tareda mayarda belt din inda suke boye jikin gadon kafin ya daura mata ruwa da sauran abubuwan da dole zaayi mata sbd yanzu saita kwana biyu ahakan Bata dawo daidaiba Dan ko ruwa a yanzu bazata iya Sha da kanta ba sai anbata.
Bayan ya gama komai cikin kulawa yayiwa sister Ashley sallama ya fice zuwa wani aikin yabar sister Ashley tana zare mata kayan jikinta ahankali sbd goge raunikanta da mata dressing dinsu.
Har lokacin idanuwan Ameenatou din a Bude suke Amma Bata ganin komai hakama Bata Jin komai bare Kuma motsawa sedai idanuwan sunyi jajir hawayen azaba ne kadai ke gangaro musu ahankali.
Ita kanta sister Ashley cikin damuwan da sanyin jikin take tana goge mata ciwukan da cottonwood.
Sai dare sosai kusan Daya saura kafin sister Ashley ta fito dakinta tareda rufe mata sbd doka ce Babu Wanda aka yadda bayan 1 na dare a gansa gurin patients idan ba Wanda babbar matsala ta tasowa ba sbd tsaro da kiyayewa Dan haka 1 nayi gurinsu tsit zaka jisa Dan yawanci da dare ana Basu maganin bacci ne.
Masifar Dake cikin alluran da akai mata Baya barinka kowanne irin Abu bayan komawanka kaman gawa da ido Bude Dan haka yanda ta barta haka ta taddata da asuba.
Daga Nan kwance ta goge mata jikinta Dan Babu maganar wanka sai tafara sakinka tukuna.
Tana gama goge mata jikinta ta Saka mata wasu uniform din daban ta mayar da ita ta kwantar,
Daga Nan kwancen ta zauna bakin gadon ta gyara mata gashinta tareda tattara mata ta Dan kama sama sama ba sosaiba sbd daman baa kamawa sosai ga wainda ma basuda gashin aske musu kawai sukeyi su huta sbd fisgan gashin sukeyi suna illata kansu kokuma qazantar tayi musu yawa amma ita datake dashi sosai gamawa takeyi da band mara karfi kuma sakwa sakwa baa kamewa sosai.
Harta Saka abin gyara gashi ta fece mata ta kame idanuwan Ameenatou din a Bude Amma har lokacin Bata gane waye a gabanta hakama Bata iya ko motsawa.
Tea ta hada mata me kauri sosai Wanda baida zafi ko kadan hakama baida sanyi me dumi kawai ta Saka spoon tafara Bata a baki bayan ta tayar da ita ta jinginar jikin gadon ta Saka napkin a wuyanta zuwa kirjinta sbd Rabi kusan duk dawowa yakeyi so zai lalata kayanta.
Tana gama Bata ta ajiye cup din tareda zare farin qaramin towel din ta goge mata Baki da fuskan gaba Daya ta mayar da ita ta kwantar ta fice bayan ta Saka mata ruwan alluran baccinta cikin drip data sake daura mata Babu Bata time idanuwanta suka rufe baccin wahala ya dauketa.