AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Suna isa tin daga yanayin asibitin jikin Jamaal ya fara sanyi sbd bayajin zai iya awa ko daya a asibitin sbd cuta zata iya kamasa Dan haka nosemask siddeeq ya dauko musu daga mota suka Saka kafin suka kutsa Kai tsaye inda zaa kaisu dakin Mam.
Tin kafin su isa dakin hankalin Jamaal ya tashi zuciyarsa tafara tsinkewa sbd ganin balain da suke dosa da sunan dakin da mahaifinsa yake Ciki.
Suna tsayuwa kofar dakin kafin a Bude Wani Azababben wari me Saka ciwon Ciki ya tirniqesu
Siddeeq ya Kalli Jamaal da sauri sbd shi kansa Jin yayi zuciyarsa na Neman karyewa bare Jamaal din.
Ana budewa kallo daya Jamaal yayiwa Dan qaramin qazamin zanin dayake rufe da Dad dinsa daya koma kaman skeleton sbd rama da azabar Ciwo daya gama cinyesa take qafafunsa sukai Wani irin mummunan sanyin daya kasa dagasu siddeeq ne yayi karfin halin zuwa har gaban Mam din ya miqa hannunsa ya yaye rufarsa take ya fashe da wani irin Kuka duk jarumtarsa baisan lokacin da kukan ya taho masa ba sbd idan ba ance Maka Mam dinne ba bazaka tana cewa shi din bane sbd wannan Yama tashi daga mutum ya koma wata halittar.
JAMAAL da zuciyarsa ta gama karyewa akan mahaifin nasa Shima takowa yayi ya durqusa gabansa.
Qamshinsa ne ya shiga hancin Mam din da Baya iya komai bayan kallo da Idanuwansa da idan suka kalleka zaka iya firgita sbd tsoro.
Qamshin Jamaal ne daya shiga hancinsa ya sakasa Bude Idonsa daya dayake rage masa ya zubawa fuskan Jamaal din Yana tantance kamannin ran dayafi so a duniya fiyeda komai Kuma duk tsawon wannan lokacin Babu wanda yake cikeda kewa da tsananin son Gani kaman Jamaal da ‘dansa dayake son Gani ko so daya ne ya tabasa kafin ransa yabar jikinsa.
Jamaal na hada Idanuwansa da mahaifinsa hawayensa gangarowa sukai batareda ya iya riqesuba duk jarumtarsa Dan haka hannuwansa na rawa ya Saka batareda qyama ko shakkar komaiba ya dago Dad din ya rungumosa jikinsa Yana rintse Idanuwansa da sukai tsananin ja hawaye na qara saukowa daga cikinsu.
Bai iya cewa komaiba daukansa yayi cak tareda miqewa tsaye dashi take suka fito siddeeq kuwa da Shima Idanuwansa suka sauya sbd Kuka sosai shikam yayi.
Da ambulance akai gaggawar barin asibitin da Mam Wanda Bayan hawayen Dake gangarowa daga gefen idonsa Babu abinda yakeyi sai Kuma kallan Jamaal bayason ko kyaftawa sbd Bai taba tinanin zai sake samun cikar burinsa ba a duniya na ganin Jamaal dayeke tsananin fata kafin barinsa duniya.
Duk halinda yake Bai taba Jin tsana ko zafin ‘dan nasa ba sbd ya tabbatarda tsananin son Jamaal shine kaddararsa da jarabawansa wadda yake rungume da ita har Lokacin hannu bibbiyu sbd Bai taba Dana sanin sonsaba fiyeda kansa ba har yanzu din.
Qazantar Dake tattare da Mam din wadda ta gama cinye fatarsa da Naman jikinsa ya Saka Saida aka fara tsaftacesa sosai kafin akai dakin taimakon gaggawa dashi duk da ba a gigice yake ba kawai a Cikin asalin ciwon dayake cinye namansa ahankali yake wanda ruwa kawai da sauran abubuwa sukai masa sbd fita dashi Cikin gaggawa Jamaal din zaiyi.
Zaunawa yayi gaban Dad din lokacinda kowa ya fice ya dago jajayen Idanuwansa ya zubawa Dad din wanda Idanuwansa suke rufe Cikin tsananin azabar da shi kadai yake jinta Cikin jikinsa tana cinsa.
Hannu Jamaal ya Dora akan na dad din dayake rufe gabaki dayansa sbd Sam bazaa so kowa ya gansa a hakan ba sbd ya nade ya koma kaman Dan shekara goma Sha biyar sbd qanqatarsa.
Cikin wata irin murya Dake rawa da tsanani tausayi da kewa ya furta
“Dad Allah ya yafe duka kura kurenka ya dawo da haske rayuwarka da lafiya tareda tuba me tsarki”
Ahankali Mam ya Bude Idanuwansa ya Kalli Jamaal din Jin adduar da yayi masa har Cikin ransa ya lumshe Ido da sanyi alaman Ameen.
Kafin Jamaal ya sake magana Dad Omar ya shigo dakin Cikin hali na tsananin damuwa da Wani Azababben quncin daya nauyaya zuciyarsa da Kiran Jamaal din ya samesa akan Mam jikin Mam din sbd duk abinda yake tsakaninsu akwai wata irin kaunar asali tin ta quruciya a tsakaninsu dasukewa junansu.
Kallo daya yayiwa Mam ya kasa qarasowa gurinsa duk manyancinsa Shima Kuka ne ya kufce masa Mai tsananin Ciwo da radadin gaske.
Jamaal ma qasa yayi da kansa tareda miqewa daga inda yake ya bawa Dad din guri ya qaraso gurin Dan uwansa ya zauna ya Dora hannunsa akan na Mam tareda sake fashewa da Wani kukan.
Mam da zuciyarsa ta gama mutuwa ahankali ya motsa hannunsa ya kama na Omar din dayake Cikin nasa hawaye masu dumi na gangaro masa kaman a mafarki Allah ya basa iKon Bude Baki ahankali ya furta
“Omar idan na rasu Nima ka kaini gefen sauran yan uwanmu ka rufeni”
Omar sake damqe hannun Mam din yayi Yana kasa cewa komai sai jajir da Idanuwansa sukai yanajin Wani irin nauyi a zuciyarsa gameda Yan uwansa da suka barsa daya bayan daya.
Jamaal Mam din ya kalla kafin ya Kalli Omar ya sake Maida kallansa kan Jamaal ya Bude Baki a wahalance da sauti mara fita yace
“Jamaal na yafe Maka komai kada Allah ya kamaka da komai akaina na yafe Maka Allah ya shirya Maka zuri’arka ya musu albarka”
Dago jajayen Idanuwansa Jamaal yayi ya Kalli Dad din nasa Yana kasa cewa komai bayan adduar dayake masa Shima na allahyya yafe masa.
Omar ma da Mam din ya kasa kallansa ya Nemi gafararsa sbd yasan cun cutatar dashi mafi cutarwa ajiyan zuciya me zafi da qunci ya sauke ya Kalli Mam din ya Bude Baki yace
“Na yafe Maka Mam duka ku dukan Allah ya yafe Muku ya karbi tubanku Kuma”
Hawaye masu Ciwo ya sake gangaro masa Yana kasa kallan Omar din.
Dr Aleena ce ta shigo dakin sai Ameenatou me tsahon Ciki Dake bayanta sai babbah da dadah tareda Arfat sai Kuma hafiz wanda shine ya kawosu,
Bayan shigowansu maman fadeela ce da Ayesha da siyam Wanda itama ta warware fes ya dawo tana hannun Dad Omar din kaman yarsa.
Kallansu yayi bayan dayan ciwonsa na tsananta sbd zuciyarsa data kasa daukan kallansu sbd a Cikinsu kaf Babu wanda Bai Raba da masoyansa ba Dan haka Bai iya cewa komai bayan ciwonsa dayake Neman rikicewa.
Arfat ya qurawa Idanuwansa Wanda Jamaal ya kamo hannunsa ya kawo masa gabansa tareda kamo hannunsa ya Dora masa Akansa Cikin sanyi murya a shaqe yace
“ARFAT SEELAH”
Wani irin Kuka mara sauti Mam ya sake Yana riqe Arfat din wadda yake kallansa kafin ahankali ya Bude Baki yace “grandpa” kaman yanda Mommah dinsa ta sanar masa gurin grandpa dinsa zasu.
Wannan kalman ta Saka zuciyar Mam kasa dauka take ya rikice gabaki daya Yana kallansu daya bayan daya kafin ya tsayar da Idanuwansa akan Jamaal Wanda ya rungumosa jikinsa Dad Omar Yana karanta masa kalman shahada Yana karba kafin rai yayi halinsa agaban kowa take dakin yayi tsit jikin kowa a mace cikeda tsananin tausayin Jamaal Wanda ya rungume Dad din nasa da kyau Yana rintse Idanuwansa dake radadi sbd rashin kukan daya kasa fitowa daga cikinsu.
Babu wanda a dakin Cikin mata hawaye Bai zubo masa ba a mazan ma Dad Omar Kuka yakeyi sosai sbd ya koma shi kadai ya rage a Yan uwansa duk sun tafi sun barsa Shima Yana fatar idan lokacinsa yayi akaisa kusa da Yan uwansa a rufesa.
****Rasuwar Mam seelah Babu Bata lokaci ta yadu Dan haka Babu Bata lokaci Aka tafi da gawarsa Ashlawa kaman yanda yaso acan Akai janazah dinsa aka rufesa Omar ya zauna gaban kabarin su hudu a jere yayi kukan da kusan ya sakar masa ciwon kirji,