AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Thank you for being okay”

Jin tayi zuciyarta na narkewa da kalmansa Dan haka Idanuwanta suka ciko da hawaye sedai Bai bari sun saukoba ya janyota jikinsa ahankali ya shigar da ita tareda rungumeta Yana sauke ajiyan zuciyan data itama hawayenta suka sauko tana sake lafewa jikinsa.

Shiru sukai tsawon mintina ahakan kafin ta Bude Baki Cikin sanyi da nutsuwa tafara fada masa abinda yafaru komai da komai tanajin Yana sake qanqameta alaman yankar zuciyarsa zancen yake Dan haka ta qarasa da rarrashinsa tareda nuna masa komai ya wuce inshallah.

Bayan radadin abinda Mam din yayi mata babban shock dinsa shine yanda sukasan waye Arfat Amma sukai shiru tsawon lokaci batareda tada hankalin komai ba ko rigima wanda yasan itada Jamaal din sunyi hakan ne sbd tsananin respect dinsa dasukeyi da Kuma son bawa Arfat din da AM tsaro Amma duk da hakan sun basa tsananin mamakin daya sakasa Jin jikinsa yayi sanyi Dan baisan Jamaal zai iya masa hakan ba bayan ya Gano Arfat jininsa ne tsatsonsa ne Kuma ya zabi janyewa daga auren ya hakura yayi shiru sbd tsananin biyayya da bin dokar maganarsa.

Itace mara lafiyar Amma kusan itace take rarrashin sbd yanda tasan shi da Jamaal Babu abinda zai hanasu daukan mummunan mataki.

A tasa zuciyar kuwa bazai bari Jamaal ya taba Mam ba sbd mahaifine koman zamansa Shedan Dan haka shine dayake daidai dashi zai dauki matakin akansa daidai yanda ya dace sbd zai nuna masa Shima jinin SEELAHs dinne idan sun manta hakama akwai sirkin Ashlawa a jikinsa.

Babu jimawa doctors suka sallameta suka fito hannunta Yana Cikin na Omar Amma jikinta Yana Dan hade Dana Jamaal suka nufo mota tana tafiya ahankali.

A motar Jamaal zata koma gidan Dan haka Siddeeq ne ya Bude mata motar Yana komawa gefe.

Hannunta dayake Cikin na Dad Omar ya kalla kafin ta dago ta kallesa Shima ita ya kallan cikin kulawa da nutsuwa yace “its okay Babu abinda zai faru bazamuyi abinda Bai kamataba, Jamaal ma is out of it,be okay.”

Gyada Kai tayi ahankali sbd batason daga Jamaal din har Omar suyi abinda zai Bata imaninsu ko halinsu akan Mam Dan haka ta sake sauke ajiyan zuciya tana cewa “thank you” da qaramin sauti tukuna ta shige motar.

Jamaal ne ya rufe mata kofar tareda juyowa ya Kalli Dad din shi har Lokacin Idanuwansa Basu dawo daidai ba shi kadai yasan abinda yakeji.

Dad Omar rungumesa yayi Cikin tsananin kauna da sanyi Yana cewa

“Karka damu zanji da komai karka tabasa ko kadan
Abinda kayi masa na Rabasa da komai ma yayi sbd shine Abu mafi Ciwo da karya rayuwa hakama hakan ne ya tabasa yayi wannan zarewan daya aikata hakan so ka cire komai ka Kula da Mum dinka.”

“Thank you Dad” Jamaal din ya furta Yana Jin zuciyarsa na Dan sanyaya wanda ayanzu ‘yar Dad dince kadai ganinta zai qarasa wargaza nauyi da zafin dayake rage a Cikin zuciyar tasa.

Motar suka shiga siddeeq ya tada suka bar asibitin
Shima Omar din Ahmed ne ya dawo da motarsu gabansa aka Bude masa ya shige take suka bar asibitin Suma.

Hanyar gida suka kama Omar na shiga tinani kala kala masu zafi da Ciwo da masu sanyi da nutsuwa.

Koda suka isa gida babbah ya sanarwa dasu dadah abinda ya faru Dan haka hankalinsu Mum Nur da Didi harma da dadah din ya tashi sai a Lokacin dadah ta hau sama gurinsu Ameenatou Dake fama da kansu ta samu Ameenatou din ta Dan samu sauki tana zaune Ashley na yanka mata apple da watermelon tanaci ahankali ta qara haske sosai tareda yin bulbul sai alokacin dadah take sake lura da hakan sedai ganin batajin Dadi sai Bata Wani Yi musu dogon bayaniba ta Dan fada musu sama sama tana zaunawa gefen Ameenatou din Dan sake dubata.
#MAMUH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
142
Cikin kulawa Dadah take kallanta tana tambayar menene yake damunta ne?

Numfashi Ameenatou din ta sauke ahankali tana kasa kallan dadah.

Ashley dadah din ta kalla tareda sake tambayarta Cikin kulawa tana shafa wuyan Ameenatou din dayake dan sauran zafi.

Cikin sanyi Ashley tace

“Dadah zazzabi ne yake damunta na yawan Aiki sbd Bata son hutawa”

Kallan Ameenatou dadah ta dawo tayi tana cewa

“Budurwan Babbah gaskia Nima na lura da bakyason hutawa,
Meyasa kikeson takura kanki tinda Babu me Miki fada Koda Baki tafiba,
Kinga gashinan yanzu kina fama da zazzabi,
Dan Allah ki kiyaye kinji,
Banason wannan zazzabin sbd Abu kadan yake sakaki Ciwo sosai ayita fama kibi ki galabaita.”

Sai alokacin ta dago ta Kalli dadah da Idanuwanta da suke son cikowa da hawayen tausayin dadah da batasan komaiba kafin ta zame ta kwanta jikin dadah din tana lumshe Idanuwanta.

Dadah cikeda kauna da kulawa ta gyara mata kwanciyar a jikinta tana Jin tsananin kaunar ‘yarta na qaruwar mata.

Koda su Dad suka dawo kawai sama sama aka sake tattaunawa tukuna aka bar maganar sbd batada dadin cigaba da tattaunawa sedai Mum Nur tace anjima zasu tafi gabaki dayansu su dubo Dr Aleena din da daddare.

Dad Omar ne ya bada umarnin a bari sai zuwa gobe gabaki dayansu saisu tafi dubota din sbd yau dai Kam akwai sauran shock a tattareda SEELAHs din.

Haka suka bari zuwa goben wanda Hafiz uncle Ahmed ya Saka ya sanarwa SEELAHs din Jadens na Nan zuwa gidansu dubiya acan zasuyi dinner.

Mum Aleena sosai ta ringa rarrashin Jamaal tareda nuna masa samun saukinta kafin ya sake Dan dawowa daidai,
Siddeeq ma Saida Mum din tayi da gaske kafin ya Dena blaming kansa akan hakan duk da Jamaal yace karya sake Jin ya fada hakan sbd yasan idan Siddeeq zai bari a dauki ransa to sedai a dauka Amma idan Yana kusa bazai bari ayiwa Mum dinsa hakan ba Dan haka ko a tinani bayason Siddeeq din na fadar hakan.

Maman fadeela ma Ayesha data rikice gabaki daya take kulawa da ita haka dai suka samu gari ya waye suka tashi da nutsuwa da kwanciyar hankalin ajiye komai kaman yanda Mum din ta fada Dan haka Mum ita farin Cikin ma zuwansu da akace takeyi sbd zata ga Arfat wanda ta kwanaki da yawa Bata sakasa a idonta ba.

Maman fadeela ma haka ta ajiye Ayesha tayi mata nasihar data Saka jikinta mutuwa ta rungumi qaddara ta barwa Allah komai tinda Jamaal da Mum Aleena sun karbeta da dukkanin zuciyarsu ta godewa Allah badan hakan ba Allah kadai yasan gantalin rayuwar da zai sameta Amma gashi tana Cikin rufin asiri da kauna da kulawa kaman wadda takeda uwa da uba a duniya.

Hakan ya Saka itama Ayeshan rungumar kaddara ta barwa Allah ta ‘dan sake,

Maman fadeela kitchen ta shiga Cikin masu Aikin gidan Dan kulawa da girke girken da zaayi na baqin sbd sanin daga Nan gidan har jdens din lafiyayyar cima suke ci Mai tsari da kyau.

Ameenatou dole ta tattaro karfi da kuzari ta warware sbd kada a gane halinda take Ciki sbd babbah daya fara mitar rashin lafiyanta tasan baya wasa da lafiyarta ko kadan.

Dad dinta ma Cikin kulawa ya sanar da ita fitar tasu bayan ya sanar da kowa maganar aurensa da Dr Aleena wanda ya Saka kusan kowa shock bayan wainda suka san da auren sedai Babu wanda yayi Wani magana bayan ta congratulating Dad din da sakawa auren albarka sbd Basu dauka hakan Wani damuwa ba Ameenatou ce kawai ta tafi gurin Mum Nur har bedroom dinta tana isa ta rungumeta ahankali Cikin sanyi da tsananin kulawa batareda tace komaiba ta nuna rarrashinta da jinjina mata kaunarta na sake cike zuciyarta sosai sbd Mum Nur takai uwa ta Dade da wuce matar uba a gareta shiyasa take jinta har Cikin ranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected