AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Kayan baby Ameenatou kuwa tin daga kayan sakawa har Madara da abubuwan buqatanta Babu abinda Bai siyo ba Dan haka dadah itama ta sake jikinta yanda ya kamata tana kulawa da ita tamkar ma itace ya haihu Dan duka makota da Wanda suka ringa shigowa suna gaisawa sun dauka itace ta haihu din itama Bata Musa din ba sai aketa mata barkan haihuwan ana tambayar sunan yar.

Dayake baai mata yankan suna ba sai da sukai kwana biyu sun gama hutawa da gyaran gidan kafin Babba ya yankawa Ameenatoun tasa rago Akaci Akai sadaka.

Tin dukkaninsu sunata fama da kadaici da bakunta har suka fara sabawa tini dadah tafara Yan sana’ointa data Saba Yara ma sun fara zuwa makaranta tini,

Babbah ma shago ya Bude a kusa ba nesa ba na siyarda hatsi Dan haka suka dauki hanyar zama Yan gari musamman Babbah Daya danne komai ya koma babbansa na Baya sbd kawai su zama cikin farin cikinda idan Ameenatou ta tashi itama zata tashi cikin farin ciki tsakanin iyayenta Dan baida niyar tasan basune asalin wainda suka haifetaba duk da sunyi mata tsufa a iyayen Amma dai sune suka haifetan kawai.

Dan haka ahankali suka nitsa rayuwa na tafiyar dasu cikin Kwanciyar hankali da amince Dan tini ya rufe Babin Omar a rayuwarsa data iyalinsa Dan kuwa bayajin har abada zai bari Omar ma yasan inda suke bare tinanin ma yanada ‘ya a hannunsu.

*******
Lagos

Zaune suke duk inda jini yake yawo a jikin Mam seelah tafasa yakeyi Yana Jin kaman kansa zai rabe sbd baqin ciki da damuwa.

Shikuwa lameenu tini yafara ficewa hayyacinsa sbd kansa Bai sake cikakkiyar lafiya ba tinda lamarin Nan ya faru sbd ya kasa tantance gaskiyar abinda yake gudana a Kai da zuciyar Omar Wanda har lokacin baida alaqa da kowa Babu labarinsa.

Ga dukiyar dai ya tafi yabarta kusan a hannunsu Dan duka kadarorinsa yanzu kusan a hannunsu suke amman Sam basuda nutsuwan cinsu tinda basuda tabbacin Shirun nasa na Menene,
Amma dai ko na Menene Abu Daya suka tabbatarda shi shine fitowarsa Koda zasuyi gaba da gaba ne saisun kar karshen matsalarsu Dan yanzu rayuwarsa ma itace abin buqatan tinda yasan Menene sukai masa.

Shigowar BB babban Dan hannun damarsu Mam dinne ya Saka Lameenu dagowa da idanuwansa dasukai ja ya kallesa kafin yayi magana cikin girmamawa BB ya Kalli Lameenun kafin ya Maida kallansa kan Mam Yana Dan sauke Kai cikin nasa zafin zuciyar da fargaban abinda zai fada yace

“Ranka ya Dade binciken da muketa son tabbatarwa akan gawawwakin da jamian tsaro suka fitar bayan kashe gobarar gidan gaskia ne gawa uku kadai aka samu daga cikin gida sai gawar security dinnan Daya daga waje bayan Kuma idan aka cire Sir Omar da Ahmed gawa BIYAR ya kamata a Gani a cikin gidan…….

Wani mugun zufa me zafin gaske ne ya tsinkowa lameenu kansa na sarawa
Shikuwa Mam wata mummunan sarawa kansa yayi ya dauki ruwan Dake gabansa yakai bakinsa Yana Sha sbd Jin koina jikinsa kaman Yana ci da wuta.

Dan gyara tsayuwa BB yayi Yana kallan Lameenu Daya zuba masa ido Yana jiran sauran bayanin yaji Shima wani zufa ya tsitsifo masa sbd abinda zai fada yace

“Cikin gawawwakin da aka samu an samu tantancewa da tabbacin akwai ta matar sir Omar din Amma Kuma Babu ciki a jikin gawar Wanda ni Kuma ta tabbatarda naga tsohon ciki a tareda ita a Daren……..

Ruwan da Mam ke Sha ne suka dawo ta hancinsa gaba Daya ba shiri sbd mummunan tashin hankalin da Bai taba Jin irinsa ba.

Lameenu kuwa take bugun zuciyarsa ya Nemi tsayawa cak sbd firgicin da Bai taba samun kansa ciki ba.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#DR J SEELAH
#DESTINED
#LOVE
#ROMANCE
#LIFE
#REVENGE
#HAROON SEELAH
#IDENTICAL TWINS
#ZAFIN KAI
#THE SEELAHS

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
17
Shi kansa BB zufan yaje hadawa zuciyarsa na tsalle Dan yasan ansamu babbar matsala data jawo musu wani Sabon aikin me girma daban.

Mam kuwa bayan ta hanci da ruwan suka biyo bar cikin kansa sukai yaji Yana Neman zaucewa da sauri ya dago idanuwansa da suka sauya take zuwa jajir ya Kalli BB dukkanin jikinsa na Neman sakewa daqyar ya hado kalmomi a bakinsa cikin sanyi da nutsuwan son fahimtar komai daki daki yace

“Wane ciki kake Bada tabbacin ka Gani a jikin matar Omar?
Na haihuwan Dan mutum kokuwa na samun qoshi datai a gidan??”.

Kansa ya saukar kasa bayan ya Kalli lameenu Wanda shi kwata kwata Neman rasa gane komai yakeyi
Ya Dan sake saukar da kansa qasa yace

“Tabbas cikin haihuwa ne a jikinta,
Kuma kaman yanda Daya daga cikin securities dinmu Dake ganin gidan ya tabbatar mana tabbas tana daukeda juna biyu tsoho matar Sir Omar din..

Hakama a Daren Koda muka shiga ni naga cikin da idanuwana sedai abinda yasa ban fada ba na dauka ba amfani tinda itada cikin sun tafi kenan sai gashi ance Babu ciki a jikin gawarta hakama baa samu gawar baby Koda konanniya ce a gidan,
Gashi Babu sauran mutum biyu Daya kamata Suma ace an samu gawarsu a gidan,
Dame aikinta Daya Wanda kowa ya tabbatarda masu aikinta biyu ne hakama a Daren ranar shi Sir Omar din yayi baqo Wanda bamusan ko wayeshi din ba a gun sir Omar din
a cikin gidan ya kwana muma da idonmu mun gansa mun sumar dashi Amma baa samu gawarsu ba…..

Jinin Mam da lameenu wata irin qunar masifaffen tashin hankali sukeyi musamman Lameenu da idanuwansa suka rufe baiga cikinba da Saiya tabbatarda a tsakiyar cikinta zai kutsa azabbiyar wuqarsa me barka kayan cikin mutum ya tabbatarda mutuwar haihuwar magaji ko magajiyar Omar jeden seelah.

Mam kuwa a Karan farko da zufar tashin hankali mara misaltuwa ta rufesa sbd babbar babbar uwar matsala da budaddiyar masifa ta riga ta fadowa rayuwarsu tinda Omar ya rufesu akan samun haihuwarsa hakama idan har Babu ciki a jikin gawa Kuma Babu gawar baby a gidan to ta tabbata Omar ya boye abinda aka haifar masa hakama idan ya boye abinda ya Haifa Hakan na nufin ya San wani abu Dan bazai yiyu Babu komaiba Omar ya boye musu haihuwarsa ta farko daya kamata ace sune sukaiwa abinda aka haifar huduba Dan shine kaf yakewa nasu yayan huduba.

Wace sabuwar masifar ce wannan ta bullo musu?
Me Lameenu yayi?
Tayaya zaace yaje yayi aiki irin wannan da kansa Amma ya kasa tantance ciki a jikin Amina..

Cikin wani irin mafi girman tashin hankali da sake jiquwa a zufan gaske duk ac Daya gama cika palon Lameenu yace

“Kenan nakudar haihuwa takeyi a Daren Kokuma wani abin na damunta sbd a dakinta me aikinta Daya take tareda ita hakama Shima Omar ya fito a cikin Daren har harabar gida…… innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected