AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Maganar Cikin tuni ta yadu kowa na murna anata kiransu ana mata ya jiki Cikin kulawa kaman ta dawo su kula da ita da kansu sukeji.
Fatmah da Babu Wani ci gaba a aurensu tana Jin hakan taji kaman itace a bayansu Ameenatou ko yaushe gashi zasu haihu abinsu su dukan su barta Dan haka itama ta fara shigar data fara karkato hankalin Hafiz gurinta daman Yanata kokarin tarairayanta kaman Baby haka yake biyewa shirmenta Amma tana zuba masa rashin ji Dan haka ya tattarata ya watsar ya fuskanci harkan gabansa Kuma tanajin zafin hakan sai gashi yanzu tazo tana masa shagwaba da tabara iri iri karshe ta kunnasa iya kunnuwan daya kasa riqe kansa ya maidata cikakkiyar macensa Shima Wanda taci uwar azabar data sakata kwanciya Ciwon kusan kwanaki itama Yana tarairayanta karshe qasar suma suka bari zuwa Cyprus Wanda acan yaci amarcinsa son ransa ya morewa matarsa yanda ya kamata itama tini ta basa hadin Kai ba sauki honeymoon kawai gashi batada Aiki sai narke masa duk ta sukurkutasa ya gama kamuwa da sonta Mai zafi Tako Ina kaman yanda itama Basu baro ba Saida ya gama koyar da ita sonsa Bata iya komai sai ajikinsa ko gurinsa Dan haka Koda suka dawo mamakinsu kowa ya ringa Yi Amma Kuma lura itama ta kwasa Cikin ya Saka aka ringa tarairayanta tinda itace a kusa har Lokacin su Ameenatou Basu dawoba Suna maganar share wata hudu acan.
Cikinta ya fito sosai Dan so sukeyi saita haihu su dawo.
Cikin Ashley ma yafara fitowa Kuma ita har Lokacin laulayinta sauki kawai yaji Amma Bata Dena gaba daya ba kaman yanda Ameenatou ita ta Dena laulayin komai.
Duk inda zasu gabaki dayansu suke fita Cikin qananun kayan da zaka dauka basusan ma Nigeria ba bare Hausa sbd a Cikin dukkaninsu hudun Babu baqi farare ne sosai Musamman oga kwata kwata Wanda shi kana kallansa zakasan baturen ne.
Suna cika wata biyar da sati daya zuciyarsa ta kasa nutsuwa kwata kwata a Yan kwanakin gameda mahaifinsa dayake yawan mafarki Dan haka yasa aka Nemo masa Wani daga asibitin nakasashin da dad dinsa yake ya kirasu Dan yanason Jin Wani Abu gameda Dad dinsa.
Bayanin da Akai masa akan sosai Dad dinsa baida lafiya yayi mugun Nisa ya sakasa Jin rashin nutsuwan zuciya idan ba zuwa yayi ya dubosa da kansa ba Dan haka Babu wanda ya sanarwa acan Nigeria suka shirya dawowa.
Yaso Halal dinsa ta zauna anan yaje ya dawo sbd yanason ta haihu a Costa Rica din Amma tace Sam bazata zaunaba zata bisa ta dubo Dad din itama tinda basusan yaya jikin nasa yakeba.
Siddeeq dai daman shine Mai riqeda ragamar tafiyar musamman daya fahimci akwai damuwa a tattareda Jamaal din Duk yanda yaso boyewa Dan haka suka shirya gabaki dayansu suka dawo.
Ranar da suka dawo Saida suka sauka a Nigeria akasan da zuwansu aka aika motoci daukansu.
Daga airport jden mansion suka fara nufa inda kowa yake jiransu cikeda farin Ciki da murnan dawowansu.
#MAMUH*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
151
Last chapter
Babbah dayayi tsananin kewan ‘yarsa Yana ganinta kallo daya yayi mata da tsohon Cikinta yaji duka zuciyarsa ta wanke fushinsa na yayewa Yana tsiyayewa musamman daya ga kwanciyar hankalin datake cikinsa da yanda Jamaal kwata kwata ko hannunta baya saki ya Saba duk inda zasu ko a gaban waye baya iya sake hannunta itama kusan ta Saba din Dan haka ko a gabansu Dad din bataji komaiba Saida tayi Ido biyu da babbanta ta zare hannunta daga nasa ta rungumesa tana ciko Idanuwanta da hawayen kewansa da tsananin kaunarsa.
Dadah ma Cikin farin Cikin ta rungume yarta tana godewa Allah daya nuna mata wannan ranar ga tsohon Cikinta da Wani irin kyau ya qara mata da lafiya.
Ashley ma tayi Wani irin kyau da fresh ga Cikinta a gabanta sedai ita Kam ba Wani lafiya ne da ita sosai sosai ba Dan haka lallabata aka fara ana tarairayanta.
Mum dinsa kuwa rumgumesa tayi tana sauke ajiyan zuciya sunfi nawa kafin ya dagota yayi kissing tsakiyar kanta da hannuwanta Yana cewa
“Mum I love you”
“I love you too My love” ta fada tana shafa fuskansa sbd haske da Wani kyau daya qara ga wata lafiyayyar gashin fuska daya kwanta masa luf daya Tara.
Dad Omar da bayanan suka iso Suna isowa Shima rungumesa yayi Yana fadan yanda yayi kewansu kafin ya sakesa ya rungume yarsa wadda itama kallo daya yayi mata yasan tana Cikin amincin Allah da nutsuwan rayuwa tareda kulawa sbd tana barin jikin Dad din hannunta ya koma cikin na mijinta.
Arfat na dawowa school yaga iyayensa tsalle da murna ya ringa Yi Yana fadawa jikinsu musamman ganin Mommah dinsa da aunt Ashley zasu basa babies masu kyau kamansa sukace.
Kaman zaa hadiyesu dukkaninsu haka aka ringa tarairayansu har zuwa dare suka tattara suka nufi gida.
Koda suka isa masu Aiki sun gama gyara koina bayan qamshi da sanyin AC Babu abinda yake tashi.
Maman fadeela da Ayesha kaman zasuyi me Suma sbd murnan dawowansu Dan haka take gida ya cike tinda sun dawo gashi da Arfat da nanny dinsa aka taho duk da daqyar babbah ya bawa Jamaal din shi Dan yace bazai taba Basu shi din ba ARFAT nasu ne bazai bar jden mansion ba.
Dukkaninsu a gajiye suke Dan haka wanka sukai kowa yayi Shirin bacci ya kashe wayoyinsa tareda nata suka shige gadonsu ya rungumeta Yan lumshe Idanuwansa d suke cikeda damuwar dayake boyewa sbd rashin sanin Yaya jikin Dad din nasa da suke maimaita masa irin Nisan d yayi Yan buqatan zuwa da gaggawa garesa.
Washe gari Koda suka fito masu Aiki tini suka gama gyare koina tareda cike dining da breakfast dinsu Wanda Saida aka tambaya wanne zasu ci tukuna aka girka verities daban daban.
Dr Aleena ce ta iso gidan sbd tayi kewansu ita Kam Dan haka tare zasuyi breakfast Dan 10 ma ta Dade da wucewa.
Cikin farin Ciki da tsananin kauna da kulawa hankali kwance sukai mata sannu da zuwa tana rungumesa Shima Cikin nutsuwa da sanyi ya rungumeta sbd gabaki daya ya koma Jamaal dinsa baya Cikin sakewa ko walwala.
Ameenatou ce ta shige jikinta ta rungumeta har zuka zauna kan dining tukuna sukai breakfast cikeda nutsuwa da kwanciyar hankali gabaki dayansu harda su Siddeeq da Ashley da Mum Aleena din duka Saida ta sake dubasu bayan breakfast din.
Suna gamawa ya shirya white Reiss sweatshirt da wide leg jeans da fcap ya fito.
Siddeeq ma off-white Ralph Lauren polo ce a jikinsa da jeans da farar hular Shima.
Black dolce and Gabbana vshape shades ne a fuskan Jamaal daya sake qure fitowan kyau da ajinsa tareda tsadarsa gashi fuskansa a kame take tsaf Babu sakewa ko kadan a Cikinta kana kallansa sai kaji zuciyarka ta narke sbd kwarjini da class.
Kissing lips din halal dinsa yayi tareda sake Dora mata a goshinta kafin ya Dan rungumeta Yana cewa
“Take care baby”
Gyada masa Kai tayi tana kallan Cikin Idanuwansa itama tace
“I love you,take care too love,
Allah yasa jikin nasa da sauki,
He’ll be okay inshallah”
Sake kissing lips dinta yayi Yana juyawa gurin Mum dinsa ya rungumeta itama tace masa Allah yasa ba sosai bane jikin na Mam.
Ashley Dake jikin siddeeq janyewa tayi tana zare hannunta daga nasa yayi kissing hannuwanta Shima tukuna suka juya suka fice.
Kai tsaye asibitin da Mam yake suka nufa Babu me cewa komai sai siddeeq daya fara Shirin fitar da Mam din da kawai zasuyi waje duk da Basu ga halinda yake Ciki ba Amma dai hakan shine abinda zaayi din daman komai nasa na hannunsu tin daga Id cards da passport da sauran abubuwansa masu Mahimmanci.