AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
***********
Shorts kaya Hafiz ya Saka masa tareda kamo hannunsa suka fito zuwa qasan Dadah ma Nan ta sake biyosa da fruits din suna isowa dining ya manta da fushi yakeyi da Mommansa yazo da gudu Yana cewa
“Mommah”
Ajiye cup din hannunta tayi tana juyowa cikeda tsananin son babyn nata tayi kissing kumatunsa tana cewa
“My love”
Dariya Dadah take musu tana sake lallabasa itama ta samu suka shirya suka zauna dining din zata basa nasa abincin a Baki,
Fatmah CE ta fito daga hanyar dayar saman ta bedrooms dinta Dana iyayenta ta nufo dining din ko zama bataiba saiga Arry qaninta Wanda yafara zama Dan saurayi.
Gaida Dadah sukai ta amsa cikeda kulawa kaman yayanta suka fara breakfast din kowa da abinda yake ci.
Basu gamaba Didi ta fito ta zauna itama tana Kiran sunan ARFAT zuwa gareta wanda ya saka Fatmah yin shiru har suka gama sbd kowa a table din Arfat ko AM.
Am dince tafara gamawa ta zari tissue ta goge bakinta tareda miqewa ta Isa gurin Arfat ta sake kissing dinsa tana cewa
“Bye sweetie”
Bye Dadah,
Aunt Didi bye”
Qamshinta ne tabarsu dashi ta wuce Arfat na cewa
“Bye Mommah”
Driver ne zai kaita Dan haka tana fitowa Kai tsaye mota ta nufa ta Bude ta shiga Baya Daman Yana ciki yin dazu Yana jiranta Kuma Yana ganin zuwanta ya tada motar Dan haka tana shiga yaja suka bar harabar mansion din.
Wayarta ta fiddo daga handbag dinta Dake ajiye gefenta ta Nemo numbern Dad dinta ta Saka Kiransa cikin sa’a ya tashi kuwa Nan suka fara magana bayan ta gaidasa.
Har suka Isa wayar sukeyi sai da zata shiga exam sukai sallama bayan ya mata adduoi sosai,
Babbah ta kira Shima Amma har lokacin Bai tashiba Dan haka ta shiga exam dinta kawai.
Acan gida ma Hafiz na gamawa dayake shi ya gama nasa karatun na 2yrs ne yayi tini ya fara aiki da babban matsayin dana Ameenatou dinne yake Kai kafin ta gama duk da matsayi daya zasu hau a kamfanin.
Tareda Arfat ya fita zuwa office sbd yau ba Wani aiki ne dashi sosaiba,
Suna fita Dadah ma ta koma bangarensu har lokacin Babbah Bai tashiba Dan haka a dining din palonsu ake jere masa nasa abincin Dan Daman can su basa joining Jamaar gidan cin abinci a table musamman idan Omar Yana gari.
*****Karfe biyu ta dawo gida ta tarar da kowa Yana jiranta cikin farin ciki da murnan gamawanta suka fara murna suna tayata murna sosai,
Mum Nur ce ta rungumeta tana cewa
“Congrats my girl”
“Thank you Mum Nur”
Didi ma rungumeta tayi cikin farin ciki Da Jin dadi kafin Fatmah ma datake gida ta miqa hannu ta tayata murna fuska a sake.
Daidai lokacin ne Hafiz da Arfat suka dawo fa gudu yayo gurinta yana nuna mata abinda yake hannunta ta dagasa daqyar sbd yanada nauyi tana kallan Yaya Hafiz Dayake kallanta Yana cewa
“Finally Lady AM budurwan Babbah ta gama karatu, congrats Lady Jden”
Dariya tayi sbd a yanzu duk lokacinda aka ambaceta da sunan budurwan Babbah farin cikine ya ke rufeta sbd haryanxu duk yanda ta samu sauyin da wayewan ita dai dince budurwan Babbah da haryanxu yake jinta kaman yar jaririya Baya ganin girmanta duk da lafiyayyan jikan data dire masa.
“Yaya Hafiz thank you,Amma ka Tina alkawarinmu right??
Dariya yayi Yana wucewa hanyar dakinsa Dake gefensa shi Daya Yana cewa
“Ban manta ba”
Yana wucewa Kai tsaye palon Babbah ta nufa daidai Yana fitowa zai tafi makarantar tata da kansa su dawo tare sbd farin cikinsa Baya misaltuwa kaman yanda Omar yake can farin cikinsa a bayyane na ganin wannan Rana.
Hannu Babbah ya miqa mata daidai lokacinda suka Hade a tsakiyar palon fuskansa a washe da farin ciki yayi Wani irin haske Shima ya sauya sosai Hutu ya ratsesa daidai gwargwado.
“Budurwata ayau ta zama mace itama ta tashi daga yarinya yar makaranta ko?”
Dariya tayi tana kama hannunsa cikin nata tace
“Babbah ai kullum ni baby ce a gabanka,
Thank you.”
Dadah data qaraso ciki itama zaunawa tayi tana kallan yanda Ameenatou din ke narkewa a gabansu kaman dai koyaushe yanda suka Saba abunsu tafara sakawa karatun da rayuwarta albarka harma da Arfat da babusa a zancen.
Bata Wani zauna sosai ba ta miqe ta fita ta haye Samanta inda dakinta Dana ARFAT ne kadai a saman sai Palo wadatacce sai kofar da zata sadar da ita zuwa palon Dad dinta.
Dayan bangaren saman shine na Uncle Ahmed da matarsa aunt Didi sai dakin Fatmah itama a saman,Hafiz Kuma bangarensa daban.
Komai na Ameenatou da Arfat a gidan ya banbanta Dana kowa duk da na kowa dinma duniya ce me zaman kanta Dan kuwa kaf gidan baka gane waye Asalin ‘dan me gidan waye bare,
Rayuwar Hutu da daula kawai sukeyi da wayewa da zallan ilimi sbd ko Babbah yanzu yana shiga mutane ba laifi sbd tini yayi abokin hira Wani dattijo Dan boko dayake zaune kasar da yayansa da matarsa yayi retire tini zaune yake a gida Yana hutawa Kuma me kudi sosai Amma kasancewan baida matsala ba ruwansa sosai yake buqatan Abokin hira da tattauna tsufa da lokaci tini suka dinke da Babbah dayake a kusa suke Dan Hakan kusan koyaushe suna tare kodai anan gidan can bangaren hutawar Omar ko a gidan shi Alh Al’ameen din.
Bedroom dinta ta Isa Kai tsaye Arfat Yana biye da ita Yana rigimar a cire masa kayansa damunsa sukeyi.
Tana shiga bedroom din qamshin turarenta na Rasasi Daya kama dakin da sanyin AC suka buso mata lumshe idanuwanta farare tana qarasawa ciki ta ajiye wayarta dake hannunta sbd handbag dinta tana shigowa sarrah ta karba ta hawo sama da ita.
Kayan jikinta ta zare ta janyo bathrobe ta wanka ta Saka jikinta gajera fararen dogaye cinyoyinta Dan bayyane ta nufo inda Arfat yake zaune a couch Yana Shan smoothie Daya shigo dashi Yana Sha Yana rigima.
Zaunawa tayi gefensa tana cewa
“My blue eyed champ zaqin ya Isa haka zo Mommah tai Maka wanka.,
Karban abinda yake hannunsa tayi ta ajiye kan table tareda zaran tissue ta goge masa bakinsa tana kallan fuskansa cikeda tsananin so da kauna tareda tinani da burinta Daya da a duniya takeson cimmasa fiyeda komai akan ‘danta,
Lokuta da dama ARFAT Yana mata yanayi da Haroon Wanda tinanin hakan kadai Sai Yana bata tsoro da fargaban idan b ciwonta ne ke Neman dawowa ba sbd Babu ta yanda zaayi ‘danta yayi kama da Wanda bayama duniyar,
Ta bangaren Daya kuma tsoro da mamakinta shine ta yanda babynta yazo a bature tamkar ba itace ta haifesa ba Kuma Tako ina bata hada jini da turawaba,
Kakanninta na asalin Jadens Kuma da ake fada basu hada jini ba bare tace daga can ta debo jini haihuwar baturen baby.
Babban burinta a dunuya yanzu shine idan ta tsayu a Kan kujeranta datake Kai yanzu shine neman sister Ashley da Hafiz ya tabbatar mata da ita ce kadai zata iya sanin waye uban cikin sbd a yanda bincikensa yazo itakadaice tasan yanda Ameenatou tayi rayuwa a asibitin tin daga ranar data shiga har ranar da suka rabu babu abinda ba itace take kulawa dashi ba na Ameenatou.
Basa Nigeria Amma duk wani bincikensu akan Neman sister Ashley Hafiz Yana gudanar dashi daga Nan din batareda sanin kowa ba daga shi sai Ameenatou din,
Bata San kamannin sister Ashley ba a idanuwanta Amma yanda take samun bayanan da ake samowa da yanda Suke fada mata yanda taso ta ko bayan dawowanta hannunsu batada abin fada sai sunanta ya saka takejin kaunarta da tsananin son ganinta da son sanin waye uban ‘danta sanyin idanuwansu.