AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Duk wayar Ashley tayi ringing hankalin Fatmah tashi yakeyi sbd kada Kiran Dad dinta ya shigo daidai babbah Yana kusa Dan haka yanzu ma da Kiran ya shigo sai dataga siddeeq ne taji nutsuwanta ya dawo daidai musamman da Ashley ta dauki wayar Dan haka take tafara adduar Allah yasa babbah ya dawo daidai lokacin ya samu tana wayar da Siddeeq tinda ba Wai girmansa tayi ba sedai suzo shekaru daidai da ita sbd Jamaal ya girmesu dukansu.

Tana daukan wayar ajiyar zuciya me qarfin gaske Siddeeq din ya sauke Yana ambatar sunanta Cikin sanyi sbd Bai dauka zata iya fushi haka sosai dasu ba tsawon kwanaki.

Amsawa tayi a sanyaye Cikin sanyin murya tana cewa

“Meyasa bazaka tsaya a iya txt din ba sbd kasan hukuncin da babbah yake jira?”

Ganin hakan Fatmah ma datakeson waya tini tana tsoro ta dauki wayarta ta turawa Hafiz txt din Dan Allah ya shigo mata da Maganin daya siyo mata last time na ciwon Kai datake tsananin fama dashi a kwanakin sbd Kuka data kasa denawa ya qare sbd itada Ashley suke Sha dan Ashely dince ma ta rubuta masa ya siyo musu shi.

Tana Tura masa txt din saiga kiransa ya shigo wayar kofa ta fara juyawa ta kalla batajin motsin dawowan babbah ba Dan haka ta dauki wayar tana sauke ajiyan zuciya.

Tambayarta yayi me zatai Kuma da maganin bayan dai komai ya Dan lafa gwara karta fiye shan magani musamman irin wannan zai iya zamar mata illa ta kasa Dena shansa.

Hawaye ne suka ciko Idanuwanta Cikin sanyi tace

“Nidai inaso zan Sha kaina sosai yake Ciwo ko bacci bana iyawa idan nasha zan samu saukin da zanyi baccin,ka siyo min kawai”

“To idan ban siyo bafa?”

“Nidai ka siyo wlh bana iya bacci duka kwanakin Nan,ka siyomin Dan Allah..” hawaye ta sake kaman Yana ganinta tana sake narke murya kaman zata fasa Kuka”

Shigowan babbah da Babu wanda ya lura sai Ameenatou wadda ba itace take wayar ba Amma Jin tayi gabanta yayi mummunan faduwa gashi da alama Yana tsaye hankali kwance Yana jinsu da kallan Ashley da Fatmah din wanda babu wadda ba a narke take magana ba musamman Fatmah da gata ya riga ya gama lalatata Ashley kuwa Cikin Wani Dan Jan aji da basarwa take maganar.

Ameenatou data gama shiga mutuwar jiki da tausayinsu duka biyun sbd ankarar dasu ta Bude Baki Cikin sanyi tace

“Babbah sannu da dawowa”

Fatmah Cikin tsananin tashin hankali ta juyo tana sakin wayarta batareda ta kashe ba hakama Hafiz ta can din yaji lokacin da Ameenatou ta ambaci sunan babbah din Dan haka tsit yayi zuciyarsa na Neman tsinkewan Shima Amma ya Dake sbd Fatmah ta sake ajiye wayar ba lallai yagane wayar takeyiba Dan haka ya Dan saurara yaji abinda babban zaice.

Ashley ma Jin maganar Ameenatou din Tayi saurin kife wayarta gefenta itama batareda ta kashe ba Kuma Shima siddeeq din a kunnensa am ta ambaci sunan babban Wanda ya sakasa kallan Jamaal Dake tareda shi ya Bude Baki a natse yace

“Babbah ne ya shigo”

Kallansa Jamaal yayi da fararen Idanuwansa Yana cigaba da karanta Mahimmin bayanin da aka turo masa ta iPad yace

“Allah yasa yaji dakai take wayar nakai masa sadakin auren kawai a daura ni na samu hanyar daukan tawa matar musan inda mukai Dan naga tsohon Nan nata so yake na Saka ayi kidnapping dinsa saina nabar qasar da Matata na Saka a sakesa.

Siddeeq dinma kallan Jamaal din yayi da fararen Idanuwansa Yana Saka maganarsa a zuciyarsa Dan bata matsuguni sbd Bai taba tinanin soyayya da Ashley ba bare ta aure sedai akwai wata irin shaquwa da kauna a tsakaninsu shi da ita harma da kusanci Bai taba kawo sonta a ransa ba sedai idan har aurenta zai Saka Jamaal ya samu Damar samun macensa ya dauketa su tafi to tabbas zaiso ace babban yajisu Shima Dan Babu abinda bazai iyaba sbd farin Ciki da samun abinda Jamaal ke so,
Take yaji ma fatarsa daya babbah yajisu ya Kuma tabbatarda shi dinne yake wayar da Ashley Dan haka daga wayar yayi ya sake Saka kiranta hankali kwance batareda Jamaal yasan ya sake Saka Kiran bane sbd bazai barsa ba tinda ya fada ne Amma shine farin Cikin siddeeq Yana Cikin abinda shine nasa farin Cikin.

Acan kuwa babbah takowa yayi Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Yana Jin nutsuwa da farin Cikin wannan lokaci Dan haka qarasowa yayi ya zauna kan kujeran zamansa ya dago ya kallesu cikeda nutsuwa farin cikinsa na bayyana.

Fatmah na Gani Hakan Cikin firgici da tashin hankali tareda son wanke kanta tace

“Babbah bada kowa nake waya ba ni da Hafiz ne wlh tallahi Kuma magani ne zai tahomin dashi sbd shi kadaine yasan Wanda nakeso…”

“Dakyau” babbah ya fada Yana kallanta Yana qara dorawa da

“Hafiz dai nawa na Nan gida kike magana ko??

“Gyada Kai tayi da sauri Dan sake wanke kanta tace

“Eh Hafiz ne Allah babbah ni kama duba wayar wlh Ba Wani bane”

“Ba saina duba ba ai Fatmah sbd kin Riga ke kinyi naki mijin Abu me sauki ma basai mun tsaya yiwa Yan Wani wajen bayanin mun tashi Yi Miki aurenba Kinga a Cikin gida ma zaa gama komai can ku qarata da maganin dayasan kinaso harma sa sauran duka abinda kikeso”

Zubewa qasa Fatmah din tayi da sauri gaban babban tana fasa Kuka me karfi da rokonsa ta tuba Dan Allah karya mata auren dole bataso Shima Hafiz din bayaso.

Hafiz dayake jinsu a wayar har Lokacin kashe wayarsa yayi zufa na feso masa Tako Ina Cikin motarsa hannunsa na rawa ya qarawa ac din motar karfi tareda juya kan motar zuwa gidan.

Ko kallanta babbah baiyiba daidai lokacinda dadah ta fito kitchen da sauri sbd kukan Fatmah din ya Maida kallansa kan Ashley data gama jiqewa da zufa sharkaf Cikin wide leg jeans din dayake jikinta da qaramar Riga mara nauyi Idanuwanta sun sauya tana Neman Hana hawayen Dake kokarin taruwa a idonta saukowa.

Kai tsaye babbah yace

“Kefa Ayshatu da wane gogan ne ake wayar??

Shiru Ashley din tayi tana sake jiqewa da zufa tana dagowa ta kallesa zata shimfida karyan da mace ne take wayar
take ya hango karyan zata shimfida masa Dan haka ya jefa mata maganar da zata sakata fadar gaskia yace

“Ko kema Hafiz dinne a hadaku ku biyu a aura masa duka ma Kun hutar damu saiku cigaba da……

Cikin tashin hankali Ashley din ta katse babban da cewa

“Wlh babbah ba Hafiz bane siddeeq n….

Rufe bakinta tayi da sauri tana kallan babban da sauri Cikin firgici
Ameenatou ma Cikin tashin hankalin ta rintse Idanuwanta tana ayyana shikenan.

Babbah kuwa sake cewa yayi

“Dakyau Ayshatu Allah dai ya biya Hafiz da Siddeeq yayi Muku albarka ku dukan”

Zamewa qasa Ashley din tayi itama da sauri hannuwanta na rawa tafara rokonsa tana fashewa da kukan itama sedai Baima tsaya sauraron su ba ya miqe yabar palon Yana duba kwanan wata a wayarsa Dan ko sati bayason su mayar batareda an daura auren ba sbd kada ma Wani lamarin ya gifto.

Ameenatou ma shiga tsananin tausayinsu ya sakata fara hawaye tana rungume Ashley dinta duk da tasan best candidate for aurenta sbd kusan komai na halayensa irin na Jamaal dinta ne so zata samu farin Ciki da kulawa sosai a hannun siddeeq da Jamaal.

Fatmah kuwa dole dadah ta janyota jikinta ta rungume tana rarrashinta da kokarin kwantar mata da hankali lokacin ne Hafiz ya shigo a natse Yana kallan yanda manyan Yan mata dasu masu ilimi da wayewa suke Kuka kaman gidan mutuwa.

Daidai Didi ma ta shigo palon ta tararda rikicin take taji Wani sanyi da farin Ciki a boye ya rufeta sbd Hafiz shine wanda hankalinta Yafi kwanciya dashi akan duk Wanda zaa samo a daurawa Fatmah din Dan haka ita Kam Bata ga abin Kuka ko tada hankali ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected