AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Tana zuwa daki toilet ta wuce tayi brush tareda wanke fuska da hannuwa ta fito tana goge fuskanta da towel ta sauya kaya zuwa kayan bacci masu kauri Riga da wando sbd tana wanka ne ta sauka dinner,

Face dinta ta zauna gaban mirror ta goge da cleanser din La Roche posay tana gamawa ta haye lafiyayyan gadonta tareda kashe wuta ta shige bargon da Arfat yake Ciki Yana baccinsa Cikin nutsuwa Yana fidda Wani sayayyan kamshi me dadi Dan baa masa wasa da qamshi ko kadan.

Addua tayi musu tareda shigewa jikin ‘danta tana lumshe Idanuwanta.

Washe gari tin a gurin breakfast kowa na kan table Dad ya sanarda kowa yafara shirinsa sbd sati uku masu zuwa zasu tafi Nigeria din Dan haka kowa saiya fara tattara shirinsa da ayyukan gabansa.

Hakan shine ya Saka zuciyar AM shiga Wani irin sanyi da daci lokaci daya sbd abubuwa datake son ta isa Nigeria din tayi da kanta wanda ba komai bane Neman sister Ashley.

Hafiz ma hakan Yana daya daga Cikin burikansa na son komawa Nigeria Dan haka yaji dadin hakan sbd a yanzu basuda Wani fargaba ko shiga damuwan komawa Nigeria sbd sunyi tsayuwan da bazasu taba tabuwa ga kowa ba,

Shi kansa babbah daman hakan yake jira a koma Nigeria din su huta da Wani boye boye ko yawon gudun kowanne Jan wuyan.

Dadah kuwa tafi kowa ma farin Ciki Dan ita Kam daman koyaushe fatanta yaushe zasu Nigeria din.

Mum Nur ce ma ta Dan ji kaman bazata iya zaman Nigeria din na Amma Kuma duban familyn nasu duka Suna tare zasu zauna a guri daya ne kaman Nan din sai taji qwarin gwiwa da nutsuwan tafiyan.

Fatmah kuwa so tayi abarta ta koma Poland da karatu sbd abinda yake maqale a zuciyarta na ganin wanda zata iya rabuwa da gidansu da qasarta ta koma qasarsa karatu Dan kawai samarwa zuciyarta nutsuwa da ganinsa kadaima.

Dad Omar ne Kai tsaye da kansa ya Hana hakan yace duka Nigeria zasu dawo bazai taba barinta zuwa Poland ba Wani Sabon karatun itama suje kawai aikin zata fara gaba dayansu har AM da Hafiz da ita tare zasu fara shiga office kowa da babban matsayinsa.

Wannan hukuncin na Dad Omar ya Saka zuciyar Fatmah din shiga damuwa Mai tsananin gaske da shakkar ta inda zata fara Amma koma dai yayane Taga Dr JAMAAL SEELAH din datake ji a bakinsu Dad din Kuma a kallo daya ta mace akansa Dan haka bazata iya auren kowanne namiji a rayuwanta ba idan ba JEEY SEELAH ba a duk inda take kuwa.

Shirin dawowa duk wanda yake gidan yafara kowa na kokarin kammala ayyukan dayake dasu a qasar da huldodinsa,
Fatmah ma shirinta takeyi tareda fita kullum Bata wuni gida tana tareda wasu friends dinta guda biyu da koyaushe Suna tare Suna yawon bankwana duk da bawai an rabu dinne ba Dan zata ringa yawon kasashe kaman yanda ta Saba.

AM school dinsu Arfat ta tafi da Dad dinta da kansa sukai bayanin komai tareda karban masa takardunsa via email suka baro school din.

Tin kafin su isa aka Saka a samarwa Arfat best school a Lagos da tsarin gidansu ma dayake kwata kwata ba anguwa daya da seelahs ba tini aka hai gyaransa da tsarinsa kaman na turai daidai da yanda aka San zasu iya rayuwa aciki musamman sbd Arfat da Mum Nur da Arry sai Fatmah da kwata kwata Basu taba sabawa da Nigeria ba bare Arfat da baima San inane hakan ba, Arry ma rayuwarsa kaf so daya aka taba zuwa dashi lokacin auren AM da Haroon hakama Fatmah shine zuwanta na farko da wayonta dai sedai lokacinda tana baby da iyayenta suka taho da ita dangin daddynta,
Mum Nur kuwa itama zata iya kirga zuwanta qasar sbd asalinta ba anan take ba itama,

Irin mahaukacin mansion din da aka Gina din da tsarinsa da uwar Tarin dukiyar da aka zubawa mansion din kaman baa qasarmu ba ya Saka mutane fara yada dawowan tasa Nigeria da iyalinsa,

Mam kuwa ajiyan zuciya kadai ya sauke Yana tabbtarda idan Bai mallaki dukiyar Omar ba kenan dai sunzo a asara sun koma a asara,
Sun dauki rayukan su kasim da Jameelu a banza,

Me hakan ke nufi?
Omar yafisu Kuma ahakan zaici gaba da finsu??
Meye amfanin rayuwar da suka zaba sbd dukiyar da haryanzu ta gagara shigowa hannunsu?
Meye sunan wannan asarar da suke kokarin tafkawa?

Ajiyan zuciya ya sauke Yana sake kallan hotinan mansion din da kudin dayake rubuce na adadin uban millions of dollars din da ake tinanin an kashe a tsarin mansion din a kiyasi ma batareda an tabbatarba Dan da alama ma sunfi hakan

Lameenu ne ya taba Tako Ina Dan kuwa shi Bai taba yadda ya tabe,
Idan dukiyar ta gagara shigowa hannunsa ta hanyar dasuka fi iyawa to kuwa zasu shiga hannunsa ta hanyar zumunci da jinin da zasu hada Dan kuwa lokaci yayi da zai bayyanarwa da duniya AM jden sirikirarsa ce ‘dan cikinsa take aure,

Idan Omar ya nunawa duniya su ba jininsa bane to Shikuma zai nunawa duniya sun sake hada Wani Jinin yanzu Kuma na gasken zbd maganar ‘yar Cikin Omar akeyi da nasa ‘dan Cikin,
Dan haka Yana zaune hankali kwance Yana jiran saukan jdens din qasar ya Basu surprise din dayafi wanda Omar din yake Basu daya bayan daya Dan kuwa yayi alkwarin a ranar da suka iso zai tabbatarda duniya tasan da ‘Dan Mam seelah Dr Jamaal Seelah ‘yar Omar jden take aure igiya uku da sai mutuwa.

********Tinda suka fara Shirin dawowa Arfat yafara rashin lafiyan zazzabin kaida kawon da Bai sababa Dan haka hankalinta Dana kowama ya Rabu sbd yanayin jikin nasa ga Kuma tafiyan Tama qarato.

26 ga watan April jirginsu ya sauka Lagos Nigeria gabaki dayansu ahankalin jdens,

Babu wanda baa gajiye yake a cikinsu ba Dan haka Arfat Yana jikin Hafiz wanda yake daukedashi rungume a jikinsa,ita Kuma tana gefen Dad dinta sanye da Riga da wandon Reiss peach color da snickers din Balenciaga fuskanta sanyeda facemask da rolling din Versace silk veil dukda Gajiye take Wani irin lafiyayyan sanyin kyau tayi kana ganinsu kaga wainda suka fito daga turai sbd Dad dinta Yana riqe da hannunta daya kaman yanda ita take riqe dashi din hannunta daya Kuma handbag din tomford ne a hannunta tana qin dagowa ta Kalli Yan jaridar daketa daukan hotinant Dan Dad dinta tareda duka familyn nasu.

Hafiz haya daban yabi sbd Arfat dayake jikinsa daman basa barin a dauko hotinansa ko kadan bare a Wani San dashi.

Uncle Ahmed ma hannun matarsa Dana Fatmah ne a Cikin nasa kaman yanda Dad Omar yake riqe da hannun yarsa sai Mum Nur Dake gefensa.

Motoci kusan hudu ne suka zo daukansu tareda securities masu tsauri
Tin kafin su iso Akai saurin Bude musu kofar motacin
Kai tsaye kowannensu ya shige suka nufa gida.

Koda suka isa gida securities dinsu na mansion din sunkai guda bakwai sai masu aikin Cikin zasu Kai bakwai din Suma daya ta bangaren su babbah wanda gate dinsu daban amma ta Cikin mansion dinma akwai kofar data hade gidansu din wanda hakan shine farin Cikinsu babbah din sbd daman yafi San gidansa ya kasance daban.

Sauran masu aikin duka nasu ne,masu aikin abinci ne da masu aikin tsaftace gida sai wadda take ta AM ce duk da sun taho da Sarrah sbd daman itama ba asalin yar can bace asalin yar Kumasi Ghana ce Amma ta Dade acan Dan itama acan ta tashi,
Ta biyosu ne sbd Arfat bazai yadda da kowacce yar Aiki ba a yanzu dazai taho inda Bai taba ba zaiga rayuwar da ba inda ya Sababa Dan haka tsaf zaiqi yadda da kowacce yar Aiki musamman sbd bai Saba daman can da mutanen waje ba idan ba na gida ba,
Ita kanta Sarrah daman batada niyar qin biyosu din sbd 3 years data fara Aiki a Cikin jdens din ta Tara abinda duka yawon aikinta Bata taba hadasa ba,
Ba qaramin arziki take samu ba Mai girma da albarka ga Sabon datai da Arfat Shima Yana son Sarrah yake fada koyaushe Dan haka ta aminta da biyosu take Babu tsayawa wasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected