AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Da farko Dr Adams baiyi tinani ko zargin komai ba Dan haka ya tattara duka files nasu Dake office dinsa ya fito dasu da kansa yakai har office din Dr Dee din sbd Daman zasu tattauna matsalan wata sabuwan patient dinsu dake jiwa kanta rauni sosai Dan nata ciwon yayi tsananin gaske gashi itama special patient ce sbd matar babban mutum ce itama.
Ajiye files din yayi akan desk tareda zama Yana sake gaida Dr Dee cikin sakewa
Shima cikin sakewan yake amsawa suna fira cikin sabo da girmamawa kafin Dr Adams yafara jero masa bayanin patient din Yana nuna masa file dinta.
Amsawa Dr Dee keyi Yana duba files din Daya bayan Daya a tsanake har ya gama Babu file din dayake tsananin buqatan ganin Dan haka ya dago ya Kalli Dr Dee din batareda nuna komaiba da kulawa yace
“Duka duka iya patients din special block A kenan?Coz Nan duka 8 files ne and a record Kuma munada 9 patients a block din so meya samu Dayan file din ko patient din zance???
Dagowa yayi ya zubawa Dr Adams idanuwansa Yana jiran qarin bayani batareda tsaurarawa ba.
Numfashi Dr Adams ya sauke Shima batareda nuna fargaba ko Wani damuwa ba yace
“Dayan patient din is my patient, she’s family,
Case nata Yans hannuna ne tin kafin Nan so file nata Yana office nawa”
Numfashi Dr Dee ya sauke Yana gyara zamansa yace
“Ok ba damuwa but dole zaka barwa Wani case dinta tinda kace she’s family Kuma kasan me Hakan ke nufi so idan ka koma office ka Aiko min file dinta zan bawa Wani kwararren likitan case dinta.”
Dagowa Dr Adams yayi da sauri ya Kalli Dr Dee din zuciyarsa na shiga shakka da fargaba tareda tinanin ta yadda zai iya yarda case din Ameenatou ya koma hannun Wani bayan yasan komai zai iya lalacewa hakama tayaya zai iya bari JEEY ya dawo ya tararda matarsa ba a yanda ya bar masa ita ba tinda idan har tabar hannunsa to tabbas zasu iya dorata akan drugs Wanda ba Bata time zai juyar da ita da gasken ba kaman wannan dayake temporary ba tinda wata na qarewa zata saketa ta koma daidai gashima duka duka a wannan lokacin baifi 6days watan ya qare ba.
Ganin yanayin Dr Adams ya Saka Dr Dee Dan sake fuska cikeda kulawa da nuna kaidar aikinsu kenan ya sani dole Wani likitan ne zai kula da Wanda yake family gunka sedai bazaa yi Maka iyaka da shiga case dinba kaima Amma dai Kuma bazaka karba ace Kai kadai ba.
Sanin Dr Adams ma yanada matsayi babba Kuma mugun kwararre ne a aikinsa ya saka Dr Dee kwantar da Kai cikin nuna kulawa Kai tsaye yace,
“Ka Aiko file din zan dubasa a Daren Nan zan karba case din nata da kaina yanda hankalinka zaifi Kwanciya coz zan iya cewa Ina ganin mahimmancinta gareka tin yanzu din.”
Babbar matsalan dayake gudu kenan Dr Adams ta fitar Ameenatou hannunsa duk tsawon wannan lokacin daga zuwanta,
Sanin zata iya cike kwanakinta ta dawo daidai kaman yanda JEEY ya buqata ya sakashi karban case dinta gashi Kuma a yanzu datake gab da dawowan daidai ana Neman samun matsala haka zalika Kuma bazai taba iya Hana Dr Dee karban case dinba tinda aka Riga da aka fara maganar.,
Shi kansa Yana cikin manyan Dake karfafa girman dokan da Dr Dee ke magana,
Me zai fadawa Dr Dee idan yashiga file din ya tararda Babu komai face information da Dan sauran tests da ba’a rasa ba na lafiyanta da Basu ma shafi hauka ba kwata kwata na tabbacin lafiyan jiki da jininta ne da suke fes ba cutar komai a tattare da ita.
Hakama me zai fada akan patient din zaman asibitin kawai takeyi Bata kan kowanne drug,
Bugu da qarin matsalan shine idan suka San alluran da Akai mata shi kansa laifi ne Mai girman gaske Dan kuwa shi kansa yayi mamakin Fitaccen kwararran likitan Poland ace da kansa yayiwa macen datake dauke da igiyoyin aurensa irin wannan alluran duk da baisan dalilinsa ba Amma yasan koma menene dalili ne me Girma kadai zai Saka JEEY SEELAH yin Hakan.
Jin shirunsa ya sake Saka Dr Dee maimaita abinda ya fada din tareda basa tabbacin inshallah zai duba lamarinta yanda ya kamata Dan haka ya kawo masa file dinta kafin gobe.
Baiyi dogon musu ba sbd babu abinda zai iya fada a lokacin bayan cewa ok kawai ya miqe ya fice daga office din.
Dr Adams baiyi niyar bayarda file dinta ga kowaba Kuma baida niyar bayarwa din Dan haka dole ya nema JAMAAL akan ya dawo da gaggawa ya karba patient dinsa daga asibitin gabaki daya kafin tabar hannunsa barinta asibitin yayi wahala.
Duk yanda Dr Dee yaso tsanantawa ya karba file din a Daren dole hakura yayi sbd kada Dr Adams ya fahimci zalamarsa ga Hakan Dan haka ya bari sai washe gari yabar asibitin gabaki Daya.
Dr Adams kuwa kasa ma barin asibitin yayi yafara kokarin Neman JEEY sedai kwata kwata Baya samunsa,
Siddeeq ya kira ya sanar masa Yana son magana da JEEY akan kwanakin Ameenatou din sun kusa cika na Alluranta.
Siddeeq da tini ya kusan kammala komai na barin qasar da ita kaman yanda JEEY yabar masa komai zuwa lokacin Dan kowanne time ma zasu iya tafiya Dan haka sai Bai raba hankalin JEEY din da maganar ba ya sanar masa inshallah kafin lokacin ya cike zasubar kasar kawai so ma yakeyi kafin ta dawo daidai sun riga sun bar qasar dan tana dawowa daidai komai zai iya dawowa ‘danye.
Ganin siddeeq Basu fahimci abinda yakeson fahimtar dasu ba yasa Dr Dee cigaba da kokarin Neman JEEY din da kansa sedai ba wannan time din dan tini duk yanda yaso kaucewa dr Dee abin ya gagara dan shima dr Dee ganin duk yanda zaiyi ya karbe patient din daga hannun dr Adams yayi amma dr Adams yaqi yadda komai nata ya shiga hannun wani take abin yafara tsanani dan kuwa manyan asibitin kusan tini suka shigo zancen.
Qarfi da Iko aka nunawa Dr Adams Wanda ya tabbatar masa da akwai abinda yake faruwa Wanda shi Bai saniba sbd a cikin kankanin lokaci abubuwan sukai nauyi ba zato ba tsammani kwatsam aka daukesa daga asibitin gabaki Daya aka turasa wata qasar ma.
#MAMUH#
#BESTLOVESTOTY
#AMJEEY
#HOTLOVE
#ROMANCE
#BABY
#AMEENATOU
#JEEY SEELAH
#JDENS
#SEELAHS
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
61
Daukesa da Akai daga asibitin cikin kankanin lokacinda Baya yiyuwa ayi Hakan ya Sakashi shiga tashin hankali da damuwa ta bangaren Daya ma JEEY sai a lokacin yake samun bayanin komai Dan haka take ya bawa siddeeq din umarnin karban Ameenatou din daga asibitin su wuto sbd komai na tafiyansu ya kammala.
Ga sabon babban tashin hankalinsu shine case yabar hannun Dr Adams kwata kwata Dan haka ba shine me Iko ko Daman sallamarta ba komai ya dawo hannun Dr Dee.
Dr Adams yayi tashin hankali dasu sosai sedai Babu yanda ya iya sbd karfinsa da akafi Wanda akaso lalata career dinsa dole yanaji Yana Gani yabar qasar yabar Ameenatou a hannunsu wadda tin kafin tafiyarsa aka fara Banka mata allurai da magungunan daya Riga yasan juyewan hankali ya Riga ya zama dole gareta haukan gaske yanzu tariga ta tabbata gareta.