AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Washe gari Saida yaje ya dubata kafin y daga asibitin zuwa gida.

A yau ne ya kamata ya wuce Greece din da aka gama komai na tafiyansa Amma Kuma bayajin zaiyi tafiyan a yanzu da sister Ashley bata asibitin hakama idan ya tafi yabar siddeeq ba amfanin Hakan tinda siddeeq Baya shiga bangaren marasa lafiya Dan haka Babu me iya kulawa da ita kenan.

A cikin qanqanin lokacin ya fasa tafiyarsa dole siddeeq ya Siya ticket a ranar ya tafi a maimakonsa shi Kuma ya tafi ya sakewa sister Ashley gaisuwa tareda Bata kudi masu yawan gaske.
#MAMUH
#EMJEEY

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
84
Karfe 9 na dare ya Isa asibitin sbd abubuwa da yawa da suka riqesa yau din sosai na tafiyansa data fasu zuwa ta wucewan siddeeq da sauyin abubuwan da aka samu.

Ameenatou a yau din a matiqar gabalaice take sbd azaban data Sha a hannun nurse din datake kulawa da ita,
Taqi cin komai taqi yadda dasu ko kadan Dan haka daureta Akai a gado aka Bata abinci wanda ya Sakata haukace musu gaba Daya ciwonta ya tashi sukai kaca kaca daga ita har nurses din Wanda ya Saka Akai mata alluran da aka Dade baayi mata ba sedai wannan Karan batai mata irin mugun kashewan datake mata ba Dan haka a kwance ta wuni Bata ko motsawa sai idanuwanta da sukai jajir.

Yana zuwa dakin abinda yafara Tararwa kenan a cikin Daren ya sauyawa nurses din biyu da suka wuni da ita gurin aiki batareda tsayawa komaiba.

Ita kuwa karfe goma Sha biyu da Mintina goma Sha hudu ya dawo dakin ya dauketa da kansa ya tafi da ita office dinsa.

Yana shiga Kai tsaye bedroom ya wuce ya kwantar da ita ahankali tareda gyara mata kanta a pillow.

Rufeta yayi ahankali tareda zuba mata idanuwansa Yana mata Wani sanyayyan kallo me nutsuwa.

Ya Dade a Hakan kafin ya sauke ajiyan zuciya tareda miqewa ya koma Office dinsa Yana waya a natse.

Aiki ne sosai a gabansa Wanda da shine zaiyi Amma yanzu siddeeq ne zaiyi Dan haka yake hada aikin ya tura email din siddeeq din kafin ya Isa zuwa gobe ya gabatar dashi.

A office din yake zaune hankalinsa gabaki daya akan aikin sedai duk bayan mintina Saiya miqe ya shiga bedroom din ya dubata ya dawo.

Ahaka ya raba Daren sosai Yana aikin da yawon dubata har kusan 4 tukuna bacci ya Dan fisgesa dayaso Sakasa latti Amma Kuma sbd sallah da samun maidata dakinta kan time ya Sakashi qin barin baccin yayi karfi.

Da asuba Yana dawowa sallah ya zauna bakin gadon ya janyota a hankali zuwa jikinsa ya rungumeta cikin sanyi da nutsuwa tareda ambatar sunanta da kulawa Dan tayar da ita.

Bata motsa ba sedai idanuwanta data Bude ahankali ta kallesa jiki a Sanyaye Babu karfi ko kadan.

Lumshe fararen idanuwanta tayi dake cike da nauyin bacci ta Bude Baki a Sanyaye tace

“Ameenatou Ashley takeso batason Haroon”

Lumshe idanuwansa yayi tareda karban zancen ta hanyar gyada mata kai cikin murya mara sautin Shima yace

“Yes Ameenatou batason Haroon”

Gyada Kai tayi itama ta sake maimaitawa tana motsawa ahankali.

Dagashi har ita kaman wainda Wani abin ya sama Babu me dogon karfi ya kamata da hannunsa suka nufi toilet yayi mata brush ya fito tayi fitsari da kanta ta jiqa jikinta kaman yanda ta Saba ya cire mata kayan Yana dauke kallansa daga gareta.

Da towel a jikinta suka fito ya Saka mata rigarsa ya zaunar da ita da kansa ya Bata tea da biscuits taci ta koshi ya kamata suka nufi dakinta hannunsa cikin nata hakama Dayan hannunsa dauke da apples guda biyu manya.

Suna is dakin ya cire rigarsa Dake jikinta ya Saka mata uniform dinta batareda ya Saka mata bra ba sbd Bai iya ba baisan Yaya zai Saka mata din ba.

Magani ya Bata da kansa ya Kuma rubuta a file nata tareda kwantar da ita take ta koma baccinta.

Rufeta yayi tareda shafa fuskanta ahankali ya furta

“Ameenatou na son Haroon”

Juyawa yayi ya fice Kai tsaye Bai wani Dade ba Shima ya tafi gida.

Bai Dade sosaiba ya dawo asibitin anan ya wuni Yana sintirin dakinta da office dinsa har yamma kafin ya tafi gida.

*****Haka ya ringa kulawa da ita shi kadai a cikin kwanakin,

Kullum kafin ya dawo da ita dakinta da safe Saiya Bata abinci taci tukuna yakaita dakinta ya tafi gida,
Da Rana shine yake sake Bata abinci hakama dare sbd kwata kwata Bata yadda da kowa Yana kusantarta,

Duk yanda take gudunsa da cewa Bata sonsa hakanan ta hakura sbd shi kadaine Wanda yafi mata sauran Dan haka ta hakura dashi din,

Tayi sanyi sosai kwata kwata ta Dena walwala batada kuzari ko Rigiman ma ta Dena sbd rashin ganin Ashley ya tabata sosai duk da wasu lokutan Saiya kira sister Ashley din a waya sunyi magana take yadda dashi shi kansa,

Shi kansa kusan komai nasa ya tsaya sbd kulawa da ita da hidimanta Dan haka a yanzu yaji Babu abinda yake buqata sama da komai bayan samun lafiyanta subar asibitin.

Sati uku da kwanaki Amma komai ya cake masa sbd hidimanta Dan kuwa a yanzu ankai lokacinda tsoronsa ma datake Jin ta Dena sbd ganin Babu Ashley dinta ba siddeeq..

Sister Ashley kuwa mijinta na cika sati ukun tafara kokarin dawowa aikinta sbd ba Wani sani take dashiba akan musiluncin tinda ba dadewa tayi da musuluntar ba ga rayuwar Lagos din data taso cikinta data shigeta batasan ma da zancen takaba ba dayake kanta.

Ta sanar da JAMAAL din zata dawo Aiki yace ba yanzu ba sai taji bazata iya zaman kadaicin rayuwar ba ita kadai ba kowa,
Kowa ya tafi ya barta kullum kaman Mayya ita kadai a gida damuwa na Neman illatata.

Karfe goma da Rabi y shigo asibitin cikin Gajerun kananan kayan Burberry milk da black yayi haske sosai sbd Raman Daya Dan yi na wahalan da Bai Saba ba a rayuwansa wadda yaketa yi a ayanzu gashi Siddeeq da shine komai nasa Bata tareda dashi hakama ba yanzu ne zai dawo ba Dan Hakan ne ma duk ya sake sanyi bayason hayaniya ko wata sabuwar damuwa da matsalan ko kadan ga jikin Mum dinsa kwanakin ya Dan tashi Dan haka Shima a cikin damuwan yake sosai dannewa kawai yakeyi.

Weekend ne Babu mutane sosai a asibitin hakama hadarin Daya Hadu me karfi ana iska sosai ya saka kowa kokarin shigewa da wuri.

Kai tsaye dakinta yafara zuwa ya dubata ya tararda ita jikinta yayi dumi alaman akwai dan zazzabi a jikinta.

Bude idanuwanta tayi itama ahankali ta zuba masa sbd kwance take cikin kadaici a dunqule guri Daya Bata motsin komai.

Shima Baya iya hayaniyan Dan haka hannunsa Daya ya Ciro daga aljihunsa ya miqa mata batareda yace komaiba.

Kaman bazata motsaba tayi shiru sai Kuma ta cira hannunta Daya ta kama nasa din ya tayar da ita zaune ya zira mata takarma a kafa ya janyota suka fito.

Office dinsa suka nufa kafin su Isa ruwa me karfin gaske ya barke
Take ta firgita ta qanqame hannunsa da gefen rigarsa shikuma yayi saurin janyeta jikinsa Yana qarasawa da gudu da ita suka shige ya rufe kofar.

Tsayuwa yayi tareda cirota Yana kallan jikinta Daya fara jiqewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected