AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Fatmah kuwa zufane sharaf ya jiqa doguwan rigan jikinta a take hakama zuciyarta Wani harbawan wuce lafiya takeyi ta Tako daqyar ta sake matsowa gap da AM ta tsaye sbd taji abinda zai fada din daidai.

AM din kuwa fuskanta itama hadewa tayi ba rahama ko daya a Cikinta sbd Batama San me suke kokarin fada ba tinda dai ba hauka akeyiba zaace ita matar Wani ce batareda ko mutum daya a Yan uwanta ko iyayenta sun sani ba,hakama aure da wanda Bata taba sani ba,
Dan uwansa ta sani shine masoyinta Kuma ya rasu to tayaya zaa fara wannan soki burutsun zancen.

Juyawa tayi zata bar gurin sbd numfashinta ma dayake Neman tsayawa da yanda zuciyarta ke bugawa daga Cikin kirjinta.

Tako daya tayi ya miqa hannunsa daya ya kamo nata tareda dawo da ita gabansa ya Kalli Cikin tsakiyar Idanuwanta kafin ya dawo da ita gefensa ya dago ya Kalli Dad Omar da har lokacin shi yake jira Kai tsaye Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yace

“I’m sorry Dad Omar,
Amma Ameeenatou is my wife,
Aurena yana kanta tsawon shekarun Nan,
A ranar da Kuka bar Nigeria a wancan lokaci a ranar na daura aure da ita,
I paid for her sadaki, Matatace, my halal…….

Numfashi me zafin gaske Dad Omar ya sauke Cikin nutsuwa Amma Wani irin tafasa jininsa keyi da zuciyarsa,

Babbah kuwa Jiri ne ya dibesa Amma dadah da jikinta itama yake rawa tayi saurin riqesa tareda Hafiz da Shima jirin da tafasar jini da zuciya yake Ciki Dan har Idanuwansa sunyi Wani irin jajir take.

Uncle Ahmed ma nauyi yaji jikinsa yai masa ya silale ya zauna kujeran dayake kusa dashi.

Fatmah kuwa da sauri Didi tayi saurin matsawa kusa da ita Dan tareta batareda kowa yaga halin Data shiga ba na Wani irin rawar jiki da zufa.

Mam Wani sabon farin Cikin ne ya sake mamayesa sbd maganar Jamaal din Kai tsaye ya sake tabbatar masa da Jamaal jininsa ne yake yawo a jikinsa.

Dad Omar dayaketa kokarin hadiye abinda yakejin kallan Jamaal yayi da jajayen Idanuwansa tsawon seconds kafin ya Bude Baki a shaqe ya furta

“A Ina?
Waye shedan hakan?
Meye dalilinka na yin hakan?
A bisa wane hujja?
Da izinin waye?

Siddeeq dayake a shiryensa dan jiran hakan matsowa yayi ya zai miqawa Dad Omar din ipad dinsa Mam ya taresa da cewa

“Muna buqatan zama sbd zance irin wannan Yana buqatan nutsuwa a tattaunasa”

Kaman wainda duka akaiwa Baki zaunawa kowa yayi Banda Ameeenatou data fizge hannunta daga Cikin nasa tana matsawa nesa dashi cikeda radadi da nauyin zuciya Dan har yanzu ta kasa yadda da abinda suke fada shi da Dad din nasa.

Babbah miqewa yayi wuf ya kamota ya riqe hannunta tareda dawowa da ita gefensa sbd da alama a Cikin daren yau idan har maganar auren Nan ta tabbata akwai to guduwa zaiyi da yarsa bazai taba bawa jinin Mam ‘yarsa ba,
Yafison su komawa talaucin da suka fito da wannan mummunan kaddarar ta tabbata a kan idonsa ace ya hada zuria da Mam.

Dadah ma riqe Ameeenatou din tayi kaman yanda Hafiz ya dawo Shima gefensu babban suka sakata a tsakiyarsu Dan Babu maganar aure tsakaninta da JAMAAL har abada.

Ipad din Siddeeq ya ajiye gabansu wadda take dauke da video din saurin auren tsaf tin daga farkonsa har qarshensa wanda shine da hannunsa ya dauka sbd yasan wannan ranar zata taho tinda basuda shedan daurin auren,

Video din na gama playing Mam ya daga wayarsa ya kira bullet Dake wajen mansion din Cikin mota tareda baqo yace su shigo.

Securities Saida uncle Ahmed ya kirasu a waya suka bari bakon ya shigo mai Aiki taje har gate ta shigo dashi har palon.

Siddeeq na ganinsa saurin kallan Jamaal yayi sbd limamin daya daura auren ne sun nemesa kaman me Basu iya samunsa ba.

Jamaal bayansa ya jingina jikin kujera ahankali Yana Dan rufe Idanuwansa da sukai jajir ya Bude yasan Dad dinsa zaiyi fiyeda hakan akan cikar burinsa.

Kowa palon kallo daya yayiwa mutumin ya gane shine madaurin auren Dan haka take Fatmah ta fasa Wani irin Kuka me cin Rai daya kasa dannuwa duk yanda taso ta dannesa tin dazu.

Didi ce tayi saurin Janta suka bar palon Mum Nur ma ita tsoro ne takeji Tako Ina Yana shigarta Dan kuwa ziyara gidan Mam batajin zata iya kaiwa bare zaman dindindin a Cikin familynsa.

Bayani daya bayan daya a tsare mutumin ya jero tareda Basu tabbacin aure Kam akwaisa shine ya daura a bisa ga bayanin komai da Jamaal yayi masa na halinda ake Ciki Kuma Shima yayi Naam da hakan ya daura auren.

Uncle Ahmed ne kadai yakeda karfin halin tambayoyi da duba komai daki daki ya tabbatarda dai aure akwaisa Ameeenatou matar JAMAAL ce his halal kaman yanda ya fada.

Nauyi kirjin babbah yayi ya zubawa Jamaal din Idanuwansa yanajin yanason yayi masa tsanar dayakewa mahaifinsa Amma hakan Bai samu ba sedai Kuma tsanar auren dayake ji daidai take da tsanar dayakewa Mam Dan haka ya miqe daqyar dadah ba riqe hannunsa ya Kalli Omar muryansa na rawa yace

“Indai nine uban Ameeenatou ban karba wannan auren ba wlh tallahi a warwaresa”

Ameeenatou dinma data kasa motsi sbd tsananin shock da baqin ciki tareda tashin hankali me tsanani dago jajayen Idanuwanta ta Kalli Dad dinta da Idanuwansa suka kada sukai jajir sbd tabbas Mam ya shammacesa ya bullo masa a hanya mafi kaifi garesa sbd ‘yarsa itace kaifinda kadai yake iya hudasa,
Aure masa ‘ya da sukai tabbas sun masa mummunan shammata tareda kutsen da ya tarwatsa zuciyarsa,

A binciken dayake Yi na asibitin datai zama an tabbatar masa da akwai baturen da yayi Aiki a asibitin na Dan lokaci Amma ankasa samun wanda zai fada sunansa,

Tabbas Arfat koma waye ubansa to jinin Tarawa ne sbd komai nasa a bayyane yake na jinin turawa dayake jikinsa,

Aleena ce wadda Arfat yake kama da ita sai yau Yana ganinta komai ya bayyanar masa ya gane fuskarta ce yake Gani a fuskan Arfat
Me hakan ke nufi??
Badai Jamaal ne mahaifin Arfat dinsu ba??
Mam yasan da hakan kuwa??
Idan wanna tinanin da abinda yake Gani gaskiya ne ba Ameeenatou ce kadai a hadarin ba Arfat ne,
Daga lokacinda Mam yasan yanada jininsa dayake yawo da Rai a gidan Nan komai yazama babba,
Barin Mam yasan ya hada jinin gasken Dani to tabbas burinsa girmama da karfafa zaiyi da komai zai iya lalacewa kowa.

Duk rintsi duk wuya Shima bazai yadda da auren Nan ba sbd Tako Ina Babu alkhairi a cikinsa fitinar shekaru ce zata qara habbakuwa ta girmama Kuma a yanzu babu wanda ya isa ya basa tsoro ko barazana sbd yarsa da jikarsa a hannunsa suke,
Shine uban daya haifi yarsa Dan haka Babu wanda zaiyi auren manufa ko jari da ita.

Kai tsaye ta Bude bakinta tana kallan Dad dinta ta murya a shaqe tace

“Dad bana buqatan auren kowa a kaina yanzu Dan haka Nima Nan aminta da aurenba a warwaresa sbd Babu buqatan auren da Babu wanda yakeso Kuma anyi ne Dan Neman mafita mafitan ta samu so I am out.”

Miqewa tayi tabar gurin tabi ta gefen kujeran dayake zaune ta wuce iskan qamshinta y shiga hancinsa ya shaqa a natse tareda lumshe Ido Dan shi zancentama babu gurin shugarsa kwata kwata a kunnensa
Siddeeq ma daya San da hakan Satan kallan Jamaal din yayi Yana Dan shafa kansa,
Tinda sai sun sauke nauyin dayake zuciyarsu kowa yasan da auren angama me wuyar aminta da auren ko rashinta raayi ne na kowa wannan.

Dad Omar ma dagowa yayi ya Kalli Jamaal kafin ya Maida kallansa kan Mam Dake zaune a natse Yana jiran abinda zai fada din ya mayar da bayansa a hankali ya jingina tareda sauke numfashi me zafi ya Bude Baki Kai tsaye Babu batawa Kai lokaci yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected