AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ayau ace shi Mam seelah ne qananun barayi masu Satan kaya suke shigowa gidansa Suna yiwa kayansa dauki daddaya.

Bedroom dinsa ya Bude anan ya tararda Wani mummunan shock din sbd suturar sakawa ko daya baa bar masa da zai Saka komai an kwashe hattada takardunsa da komai da komai na rayuwarsa masu Mahimmanci da marasa Mahimmancin ma an dauke duka.

Bangon dayake gefensa ya dafa Yana Jin Wani zafi da radadin gaske na ratsa zuciyarsa.

Wayarsa ma da zaiyi waya Babu sbd ranar daya bar gidan Bai fita da itaba anan yabarta Dan Bata Cikin motarsa da aka kamasa da ita tinda da ita aka dawo dashi Kuma Babu aciki.

Jan jikinsa yayi kaman me ciwon laka ya nufi bathroom din dakinsa ya shiga abin baqin Ciki hadda Kashi anyi an cika toilet seat din dashi.

Wanke toilet din yayi da hannuwansa da basusan aikin komaiba bayan Hutu da kisan ruwan sanyi.

Yana gama wankewa wanka yayi ya fito kayansa daya cire su ya kalla ya kakkabe ya sake mayarwa ya fito.

Motarsa ya shiga Kai tsaye Bank ya nufa Dan cire kudi sedai Kai tsaye aka sanar dashi Babu abinda yake bankinsa bayan 100k.

Yanke jiki yayi ya Fadi Cikin bankin Yana Neman kamuwa da ciwon zuciya.

Taimaka masa Akai aka kaisa har office din manager tinda ansansa babba ne sune wainda suke da manyan kudin da babu me irinsu a bankin Dan haka Ciki kulawa da girmamawa manager yayi masa bayanin da wayarsa Akai amfani aka cire kudin bankin gabaki daya zuwa bankin ‘dansa Jamaal Seelah manyan Kuma da basa fita shine da kansa yazo ya cire sbd shine magajinsa dayake rubuce wanda kadai zai iya cire kudinsa bayanshi wanda tin farko shi Mam din ya saka Jamaal dinne a matsayin wanda kadai zai iya cire kudin dayake accounts dinsa na Nigeria Dana waje sbd yasan har abada Jamaal Babu abinda zaiyi da ko qwandala a Cikin kudinsa sbd tsanar da yayiwa dukiyarsu da Kuma tasa dayake da ita baya buqatan qarin.

Cikin mutuntawa aka Ciro masa sauran kudinsa aka basa Wanda yana fitowa motarsa ya shiga baya Gani sosai ya nufa Wani boutique ya Siya ready made masu yar kudi sbd ya Saba Saka masu tsadar.

Kaftan ne na 80k ya Siya ya sauya kayan jikinsa kafin ya wuce Kai tsaye gidan drivernsa da shine yasan dukiyarsa ta boye.

Yana isa ya tararda labarin shida matarsa sun bar qasar gaba daya zuwa south Africa.

Daga Nan Kai tsaye gidan Jamaal ya nufa zuciyarsa na gap da bugawa Amma bazai taba yadda yayi qasa ba sbd haryanzu Yana power da zai iya illata Omar da ita tinda ‘yarsa itace abinda yafi so to tabbas zai dandana masa radadi da ciwon rasa abinda kakeso sbd Jamaal bazai taba masa hakan ba batareda Saka bakin Omar.

Hakama Aleena zata zama matarsa ne kadai a lahira idan sun hadu acan Amma badai idan shi Mam Yana Raye ba.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
140
Dr Aleena zaune take ita kadai a palon Jamaal dayake Sama tana magana da Siddeeq wanda ta Kira zasuyi magana tinda a palonta ko palon qasan maman fadeela zata iya ji ko Ayesha Kuma batason ko kadan su San asalin waye Mam bare Jin abinda zasu fada gashi Jamaal baya Nan ya fita tin safe Yana tareda Dad Omar gurin Wani Mahimmin meeting.

Jamaal baisan Dad dinsa ya dawo ba a ranar
Shikuwa Dad Omar Bai dauka an Riga an saki Mam dinba sbd ya dauka sai bayan sun dawo Ahmed zai isar da sakon Dan haka Babu wani special tsaro a gidan ranar sai iya securities na gidan Dan haka Mam na isowa Babu musun komai suka Bude masa gate kaman yanda suka Saba ya shigo fa motarsa.

Mum Aleena kuwa tana sama da Siddeeq ta kallesa tace

“Siddeeq Omar ya fadamun zaa Sako Mam yau Kuma a yanzu idan ya fito kowama Yana Cikin hadari musamman Ameenatou da Arfat sbd Mam bazai taba iya rayuwa Babu dukiyarsa da Bai hada da komai da kowaba,
So tinda Omar haryanzu Bai fada mana ARFAT ‘dan JAMAAL bane Nima bazan masa maganar mun sani dinba Dan haka ba Damar ce masa a kula fiyeda tinani akan Arfat sbd Mam a yanzu kaman a haukace zai fito inason ne kawai kayiwa Ashley magana koina Kar asake fita da Arfat yanzu sai komai ya lafa”

Numfashi siddeeq ya sauke Yana kallan Mum yace

“Mum karki damu babban tsaron da Arfat yake Ciki ayanzu shine rashin saninsa da Dad Mam din yai wanda hakan ma Wani tsaron ne am ce kadai a Dan hadarin Amma itama Jamaal zai iya komai akan tsaronta.”

“No siddeeq nidai hankalina ya kasa kwanciya kwata kwata akan Arfat da Ameenatou din”

“Tayaya hankalinki zai kwanta Aleena? Mam Dake tsaye kofar palon ne ya Fadi hakan Idanuwansa na sake rinewa zuwa Wani irin Jan dayafi na farko jikinsa har Wani rawa yakeyi sbd abinda yaji.

Siddeeq ne da Aleena din sukai saurin juyawa cikeda mummunan firgita da tsinkewan zuciya.

Siddeeq daya Kalli mum din Yana riqe hannunta Dan ganin yanda jikinta ya Dan dauki rawa Cikin nutsuwa da kulawa Dan kada ta rikice yace

“It’s ok Mum,karki damu”

Mam da zuciya ta gama cinyesa kallo daya yayiwa siddeeq yace ya fita ya basa guri magana zaiyi da Aleena din.

Kame fuska dakyau siddeeq yayi zai Kalli Mam din yayi masa maganar da zata kashesa sai Kuma ya fasa sbd tinawa da komai lalacewansa mahaifin Jamaal ne,
Kaunar dayakewa Jamaal da abinda yake tsakaninsu akwai abinda bazai taba yiwa mahaifinsa ba duk lalacewansa Dan haka ya hadiye fushinsa da bacin ransa sbd akwai halas da ake bari sosai Dan kunya.

Ficewa yayi daga palon ya sauko qasa Yana barin palon gaba daya Yana v
Ciro wayarsa Dan Kiran Jamaal Wanda Shikuma acan wayarsa take silent kaman yanda ta Dad Omar take silent din.

Dagowa Aleena tayi ta kallesa Idanuwanta na sauyawa sbd damuwan rashin sanin abinda yake sakawa a ransa da Kuma yanda jikinsa ke rawa.

Shima zuba mata Idanuwansa yayi Wani irin radadin gaske da jininsa dayake Kuna Suna qara masa azabar zafin dayake ji a zuciyarsa.

Takowa yayi ya iso gabanta Bai tsaye komaiba ya Saka hannuwansa biyu ya kamo wuyanta ya shaqeta da karfin gaske jikinsa na sake daukan rawa yace

“ARFAT din Dana samu hotinansa tareda Omar daga bincikena wanda baya barin kwata kwata ana samun hoton fuskansa da kyau shine ‘dan Jamaal?
Jinina??
Tayaya Jamaal zai Haifa Dan kansa jinina Yana yawo a jikinsa ku Taru ku boyemun?
Yaron da ban taba sake bi takan jefa bincikena akansa ba sbd ban taba tinanin akwai Wani jinina Dake duniyar ba bayan Jamaal Ashe jikana ne????

Cikin tsananin azaba ta fara kokarin cire hannunsa daga wuyanta tana cewa

“Daman nasan dawowanka ba alkhairi bane sbd har abada Babu tsarki ko Imani a zuciyarka,

Meyasa bazaa boye Maka ARFAT dinba tinda Babu wanda bazaka iya cutarwa akan burinka da qazantacciyar kwadayin duniyarkaba”

Sakinta yayi da qarfi Yana tureta har Saida ta Fadi ta bugu da table ta dago Idanuwanta da sukai jajir sbd sbd shaqan datasha ta kallesa zuciyrta na radadin yanda ya kasance mahaifin ‘yayanta wanda har abada bazata Dena Dana sani da radadi tareda baqin Cikin hakan ba.

Hannuwansa rawa sukeyi sosai sbd abinda yakeji a zuciyarsa Dake Jin azabar radadin boye masa yanada Wani jinin Wanda ya fito daga ‘dansa mafi soyuwa a garesa,.
Hakam ‘da ne da zai kasance qarshen cikar burinsa sbd samun Arfat shine qarshen hada irinsa da Omar wanda ko a so ko Babu dole sai sun zama daya hakama dukiya dole ta zama yanada haqqi da sake cikakkiyar iKon mallakanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected