AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Yasani akwai abinda Mam yake masa wanda yake Hanasa tashi bare iya magana Yakoma kaman Wani nakasashe,
Bazai yadda Mam yayi ajalinsaba sedai suyi n juna Amma kafin Nan kaman yanda haryanzu Bai nuna masa komaiba Shima zai tashi ya illatosa ta inda Bai taba tinanin ba Amma dai kafin Nan zuciyarsa kullum Cikin matsananincin tsoro me firgitarwa yake akan bayyanar Ameeenatou jden sbd baisan wace Ameeenatou dinne a asibitin d suke kokarin kashewa ba gashi su BB na can suna kokarin kasheta baida ko lafiyar kiransu yace su dakata a dubo masa sbd yasan waye Mam…da wannan tsoron me tsananin gaske yake kwana yake tashi Kuma akansa yake son tashi ko iya magana a dubo masa idan ba Aliyansa bane.

 

********Sanin zuwan baqin ya Saka Dad Omar ya bada umarnin Arfat yayi dinner dinsa da wuri a kaisa sama bedroom dinsa yayi zamansa Sarrah tayi masa karatun storybook haryayi bacci amma Kar a fito dashi.

A ransa yafi kowa sanin waye Mam sbd ko a kallo zai iya gane Arfat ‘dan AM ne kokuma jikinsa ne daganan basusan abinda zai iya Yi ba Dan ya lalata musu Suna ko Bata rayuwar Arfat din Shikuma hakan ne abinda bazai taba iya dauka ba sbd Bai hada Arfat din da komaiba a yanzu.

Babbah ma AM ce da Hafiz ne suka rarrashesa ya fuske Shima ya fito a shirye Cikin wata danyar sky blue tsadaddiyar yadi me taushin gaske wanda Suma Suma su Dad din da uncle Ahmed harma da Arry duka kaftans dinne a jikinsu masu tsadan gaske da taushin.

Hafiz ma Wani farin yadin ne a jikinsa harda hulars Akai yayo saida safe da ‘dansa ya fito itama AM daidai lokacin ta fito daga bedroom dinta a shirye Cikin fitted doguwan rigan Alliams Black Da koina take shining din black crystals ta kwanta jikinta daidai sai veil black da Shima yake daure a kanta.

Sanyin qamshinta ya Saka Hafiz tsaya mata suka sauko tare daidai shigowan su SEELAHs din palon.

Idanuwan Mam akan Hafiz da AM din suka fara sauka hakama siddeeq da Mum.

Dukkaninsu dawo da kallansu kan Jamaal sukai sedai wanda kallo daya yayi musu ya dauke Kai zuwa kan Dad Omar daya dauko Shima Yana musu barka da zuwa Cikin nutsuwa da farin Ciki.

Rungume Jamaal yayi Yana ambatar sunan daya saba kiransa dashi kafin ya sakesa ya Kalli Mam wanda Shima shi yake kalla kowa da abinda yake juyi da tsalle Cikin ransa gurin yayi tsit kafin Mam y sake dariyar farin Ciki me tsanani da sakewa ya ware hannu Ya rungume Omar din Yana cewa

“Har abada mu ‘yan uwan jini ne koba da auren dayake tsakanin Yayanmu,
Jinin SEELAHs daya ne ko mun zama maqiya mu din Yan uwan jini ne.

Shiru kowa yayi har Saida Dad Omar ya sake Wani lafiyayyan murmushi Shima Yana rungume Mam din yace

“Har Abada SEELAHs daya ne”

Sakin juna sukai sai a Lokacin AM ta iso gurin tana tsayuwa gefen Dad dinta lokacinda yake gaisawa da Dr Aleena Cikin tsananin kewan juna da sukai.

Qamshinta me sanyi ne ya shiga hancinsa duk da qamshin kowa dake gurin daban ne ya gauraya amma nata din ya shigesa ya dago Fararen Idanuwansa da suka sauya ya mata Wani kallan data jisa a jikinta Amma Bata Kalli inda yake din ba ta Dan sake fuska tana gaida gaida Dad dinsa wanda ya washe bakinsa sosai Cikin nutsuwa yace

“Finally na hadu da ‘yata Kuma sirikata matar ‘dana”

Cak kowa ya tsaya da abinda yakeyi Banda Jamaal daya rintse Idanuwansa ya Bude Suna sake sauyawa ya matso zaiyi magana Mum dinsa ta riqesa da hannunta daya tana Dan girgixa masa Kai.

Su siddeeq kuwa tsit sukai.

Babbah da shigowansa kenan zancen ya sauka kunnensa ya katse Mam din da cewa

“Wadda ta tashi zama matar mataccen ‘dan ka dai Amma Bata zaman ba..””

Mum ya kalla yace

‘yi hakuri madam” sbd zagin Danta da yayi gabanta.

Wani lafiyayyan murmushi Mam yai batareda Jin zafin zancen babbah ba sbd yafi kowa sanin Dan ta’adda ne babbah me zaman kansa
Yace

“Ba mataccen nake nufi ba rayayyen nake nufi gashinan a tsaye igiyoyin aurensa uku ne cif akan Lady AM jden”

Zare hannunsa daga na mum dinsa yayi ya dakatar da dad din ta hanyar Kiran sunansa Cikin dacin zuciya sedai kafin yace komai Dad Omar ya dago Idanuwansa da suka sauya ya zubawa Jamaal din wanda kusan kowa ma tsit yayi tareda zubawa Jamaal din Ido musamman ita da Zuciyarta tafara daukan nauyi.
##MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019 we473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
110

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**********
JAMAAL din take Idanuwansa suka sake sauyawa sbd tsananin zafin da kansa ya dauka da bacin ran abinda Dad din nasa yayi take wanda lalata masa komai sbd Magana ce daya kamata a zauna ayita sbd Abu ne da akai batareda yarda ko sanin kowa ba bayan shi da Siddeeq sai dan uwan Uwan maman fadeela da yayi waliyin Am din,

Hadiye bacin Rai da tsananin zafin da zuciyarsa keyi yayi ya Kalli Dad din nasa Cikin sautin Kai tsaye yace

“Do you really have to do this Dad?
Shine abinda ya Saka ka taho?
Ka shirya hakan ne daman?

Mum dinsa ce ta katsesa Cikin sanyi da rashin son ayi tashin hankali da cewa

“Son please kabar maganar,
you talk to Omar first sbd ya Riga ya bayyana zancen.” Ta qarasa zancen tana juyowa ta Kalli Omar wanda yake kallansu batareda ya motsa ba sbd a rayuwa yasan Mam baya haukan zance komai lissafinsa yake yinsa.

Babbah dayaji baya gane komai sbd kansa Dake Neman juyewa katse Dr Aleena yayi da cewa

“Wane zancen ya Riga ya fada?
Ai Babu ma wanda ya kama zancensa anan bare fahimtar abinda yake fada
Ni dai abu daya na sani ‘yata Allah yasa Bata auri ‘dansa ba to Ina fatan hakan ta zauna har abada kaman yanda Haroon ya tafi har abada”

Uncle Ahmed dasu Didi da Fatmah da duka suka iso Suna tsaye rasa abin fada sukai sai Uncle Ahmed dinne ya iso zaiyi magana Dad Omar ya daga masa hannu ahankali Idanuwansa na sauyawa annurin fuskarsa ya dauke dip ya Kalli Jamaal da Shima dagowa yayi ya Kallesa Idanuwansa na sauyawa Amma sedai Kuma ganin kowa yayi tsit sun zuba masa ido Babu wanda gabansa baya mugun bugawa da shirun nasa tareda jiran abinda zai fada sbd Dad Omar maganar bakin Jamaal din kadai yakeson ji bana kowa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected