AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Gaba tayi ta Dan Bari suyi bankwana sai alokacin ya sake dawo da ita jikinsa ya Dora bakinsa kan lips dinta ya Dan tsotsa kafin rungumeta Yana cewa

“You’re warm baby,Yaya dai??

“I don’t know Amma inajin bacci ne sosai”

Sakinta yayi tareda kama hannunta suka wuce har palonsu ya kaita na qasa kafin ya juya ya fice.

Koda ya isa gida siddeeq bayanan Yana gurin hada kan motacin kaf SEELAHs da Akai gwanjonsu a ranar.

Zaunawa yayi da Mum dinsa Shima tareda rungumeta jikinsa Suna maganar Arfat datai missing sosai Kai tsaye ya sanar da ita zai kawo mata shi har gida shida Ameeenatou din ta gansu.

Taji dadin hakan matiqa Dan haka ta cire damuwan rashin ganinsu din.

Yauma kwata kwata kasa Wani baccin kirki tayi har safe ta daure ta lallaba tayo a fita Aiki sai yamma ta dawo.

A daren ranar ma Batai baccin ba Saida ta fito dakinta ta koma dakin Arfat tukuna ta samu baccin me karfi ya dauketa take ta fahimci dakinta ne yanzu Bata iya bacci sedai Wani dakin Dan haka ta Dena bacci dakinta se dakin Arfat ko na Ashley taje ta shige bargo sbd Ashley na son sanyi sosai ita Kuma Bata Wani son sanyin.

Rage fita Aiki tayi sbd yawan kasala da rashin dadin kanta datake ji idan baa gida take ba Dan haka fitarta Aiki yafara qaranci wanda ya Saka Ashley shiga fargaba sbd hasken Data qara sosai hakama Bata Wani cin abinci sosai sedai kayan ruwa ko fruits kaman lokacin Cikin Arfat Dan haka take Ashley taji hankalinta na Neman tashi.

Ita Kanta Ameeenatou din rasa gane kanta din datai ya sakata damuwa sedai Babu tinanin dayaxo kanta irin ko yanayin sauyi. Weather ne yake tabata.

Ranar da Dad dinta suka dawo tareda uncle Ahmed farin Ciki sosai suke Ciki Dan haka da dare tare gaba daya aka zauna cin abinci sedai Babu abinda ta iya ci bayan samosas din da Ashley tayi wanda Shima Dan Taga tacisa sosai ranar datai Wani Dan haka tayisa me yawa dashi aka jera a dining din.

Mum Nur dataga yanda Ameeenatou din taci samosas din da yawa batareda taci komaiba kallanta tayi tana cewa

“Am bazaki ci komaiba sai samosas dinne da kikacisa da yawa haka??

Murmushin karfin hali tayi sbd qamshin abincin dasuka hau kanta gaba daya daurewa kawai takeyi.

Apple Ashley ta miqa mata sbd Danne abinda takeji sedai tana fara ci Wani amai me qarfin ya taso mata ta miqe da sauri tabar dining din tareda ficewa da gudu sedai tana fitowa palon daidai shigowansa tareda Siddeeq.

Ashley ce ta biyo bayanta bayan ta Kalli su babbah da Dad da kowa yayi tsit Cikin mamaki da tausayin menene ya samu am din tace musu zazzabin gajiyar Aiki Ameeenatou din ke fama dashi kwana biyu.

Fitowan Ashley tabi bayan Ameeenatou din sama ya Saka Jamaal binsu Kai tsaye Yana shigowa palon Ashley ta fasa shiga bedroom din Ameeenatou din ta barsa ya shige ita Kuma sai daga baya ta bisa.

Amai takeyi sosai jikinta yayi zafi take.

Rungumeta ta baya yayi ba sosaiba Yana shafa bayanta tareda gefen fuskanta harta samu ta gama aman Cikin Jin sassauci sosai sbd yanda yake shafa bayanta da gefen fuskanta.

Wanke fuskanta sukai a tare kafin ya zubawa fuskanta Idanuwansa Yana kallanta cikeda qwarewansa a amtsayinsa na likita.

Towel ya Saka Yana goge mata fuskanta Yana Jin kaman zai hadiyeta sbd so da kauna tareda abinda yake ji.

Baice komaiba ya kama hannunta suka fito yabarwa Ashley ita ta tayata gyarawa ta kwanta kawai.

Yana saukowa siddeeq dayake zaune a palon kadai ya tarar Yana yiwa Siyam da aka fito da ita palon zaune kan wheelchair Bata iya magana bare dogon motsi sbd kanta daya juye sama sama take sedai juyewan kanta bana hauka bane tuburan idanma batai magana kaji yarinta ko shirme aciki ba bazaka ce kanta ya juyeba.

Nurse dinta ce ta fiddota palon daga bedroom dinta Dan Tasha iska.

Jamaal na ganinta dakatawa yayi tareda qarasowa gurinta zuciyarsa cikeda tausayinta da kaunarta a matsayinta na yar uwarsa.

Itama zuba masa Idanuwanta tayi bat ko kyaftawa kaman zata tinasa Amma Kuma Bata gane komaiba sai kawai ta Maida kallanta kan siddeeq daya ambaci sunanta lokacinda aka fito da ita cikeda kulawa da tausayinta Shima.

Jin tayi zuciyarta yafi kaunar siddeeq din Dan haka ahankali ta Bude Baki tana kallansa tace

“My name is Siyam Seelah,
Did you know my Dad??
Please take me ta him…..

Hawaye tafara tana qanqame kujeran datake Kai tana Neman jiwa hannuwanta Ciwo da sauri Jamaal ya miqa hannu zai cire mata sedai Yana matsowa ta fasa Kuka da ihu me qarfi.

Dakatawa yayi siddeeq yayi saurin isa ya zare mata hannuwan sbd har farcenta data kafe a jikin karfen kujeran sun fara jini.

Ga mamakin kowa daya fito palon sbd ihunta Siddeeq suke kalla sbd Bata taba yadda da kowa ba ihu takewa kowa Ameeenatou kawai takeso sai Dadah sai Kuma siddeeq din wanda Shima tsayawa yayi kallanta.

Babbah na Bude Baki sai cewa yayi shikenan an samu wanda zai fanshi Dadah a gurinta.

Maganarsa ta Saka Didi da Mum darawa sedai Kuma Jamaal sosai yanayinta ya tabasa sbd Ameeenatou dinsa ce ta fado masa arai alokacinda itama ta samu kanta a wannan yanayin.

Dad Omar ma koyaushe ya Kalli halinda Siyam din take Ciki zuciyarsa Ciwo takeyi sbd Siyam tamkar yarsace daya Haifa hakama Shima yarsa tayi wannan rayuwar a baya Dan haka yakejin radadin ganinta hakan.

Dadah ce ta qaraso ta kama hannuwan Siyam din cikeda kulawa tana share mata hawayenta tace

“Siyam Din dadah Yaya dai?
Bakyason yayanki yazo ya ganki ne?
JAMAAL ne fa,yayanki”

Qanqame Dadan tayi tana rufe Idanuwanta batason ganin kowa.

Janta dadah tayi tai Ciki da ita shi kuwa babbah akan tasa yar hankalinsa ya koma.

Jamaal da Dad Omar dinsa kuwa sbd kewan juna da sukai rungumesa Dad yayi kafin sukai sama Shima hankalinsa na rabuwa zuwa ga ‘yarsa da batajin Dadi.

 

Ashley data Cikin mummunan fargaba kallan Ameeenatou tayi Cikin sanyin murya tace

“Am nidai Ina zargin Ciki a jikinki…..

Wani aman ne ya sake tasowa Ameeenatou din sbd dukan da maganar tai mata.

Toilet ta koma ta ringa Wani Aman jikinta na rawa.

Tana gamawa zazzafan zazzabi me qarfi Mai hade da mummunan tashin hankali suka rufeta.

Ashley ma tsinkewa tayi sbd tsoron ma babbah taji Yana shigarta da Kuma kunyar kowama duk da ba itace me cikinba Amma kusan lefin nasu ne su duka ga Jamaal gefe daya da Yana Jin Cikin idan akwai ko a jikinsa zai iya fitowa ya fada Kai tsaye.

Cikin tsoro da fargaba duka su biyun suka samu suka ga safiya ta waye Dan haka yau da wuri sukai Shirin Aiki su dukan duk da Ameeenatou har lokacin tanajin jikin Amma haka ta Danne ta daure tai Shirin Aiki suka fita a motar Ashley sbd bazata iya tuqi ba.

Fatmah data ga fitarsu take tayi zargin akwai abinda suke boyewa da alama sbd fitarsu a taren Kuma tinda sassafe Dan haka itama data fito zata fitan binsu tayi da motarta Dan saita ga ko menene sbd duk abinda zai Saka ta tona kowanne asirin Ameeenatou shi takeso sbd Jamaal ya rabu da auren Nan kowa ya huta itama zuciyarta ta huta.

Wata asibitin daban suka nufa ba tasu ba sbd tasu ansan waye Ameeenatou Kuma aga sunzo awon Ciki.

Dan haka Wani tsadaddiyar private asibiti suka nufa Suna zuwa Kai tsaye scanning ma suka buqata kowannensu zuciyarsa kaman zata fado.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
139
Ameenatou tafi Ashley shiga tashin hankali sbd harda Wani tsoro taji Yana kamata idan ta Tina babbah sbd batajin Dad dinta kaman yanda tajejin babbah sedai Kuma kunyar Dad dinta itace take sakata Jin kaman zata zare a asibitin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected