AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Infection flusher big 5k, small 3k
Breast firming sabaya 4k
Breast enlargement and hips sabaya 4k
Echoes of forever 3k
Her royal highness 2500
Milky vjay cake 3500
Ever bond 3k
Eternal flame 2k
Love nectar 2k
Cleanser pro 2500
Endless seduction 1500
Intensive love 1500
Swan 3k
Mowa’s secret 4k
Sugar queen 7k
Cloud9 4k
Sweet16 tightening gel 4k da sauransu. Muna da gumba kala-kala, tsumi kala-kala, muna dahuwar kaza, nama, tantabara, Ciccibi da sauransu. Muna da branches a garin Sokoto da Kano, sannan muna aike ko wani gari kowacce ‘kasa cikin amincin Allah, muna maraba da masu siyan daidai ko sari.
Za a iya tuntubarmu ta lambobi kamar haka
08167888934 ko
07026039714.
Ki yi ‘ko’karin ki tuntubemu don tabbas kukan damuwarki ta qare. Zaki iya tuntubarmu ta Instagram link dinmu kamar haka
https://www.instagram.com/honeydrops013?igsh=MW5saThrY3N0Z2Zjag%3D%3D&utm_source=qr

 

***********
Cikin sanyi Mum ta Kalli Dad Omar tace

“Ko Babu alkawari itama bazata taba yadda ta tafi gidan Mam aure ba,
Dan haka a janye maganar alkwarin Amma dai tasani Babu ta Babu familyn SEELAHs din.

Uncle Ahmed ma da zuciyarsa take cikeda nauyin Abubuwan da zasu iya biyowa baya wanda Shima Yana Cikin wainda suka sheda suka tabbatarda waye Mam akan abinda yakeso ya kuma San zai iya kawar da kowa da zai masa shamaki da abinda yakeso Dan haka wannan karan sun shirya masa ko Mai aikin Mansion din jdens bazai taba ba Kuma aure dai Kam basayi.

Girgixa Kai Dad Omar yayi tareda tabbatar musu da bayason maganar rikicin auren ya fita a duniya ta jisa duk da yasan Mam saiya yadawa duniya maganar auren Dan haka zasuyi shiru kawai bazasu daga tasu maganar kashe aurenba duniya ta sani sbd mutuncinsu dana yarsa harma maganganu zasuyi yawa akansu musamman ‘yarsa data taba ciwon hauka.

A Cikin tsakiyar daren uncle Ahmed ya kira Wani likita Hafiz ne ya fita tareda securities suka taho dashi ya duba Dad Omar din sbd sosai jikin yaso rikice musu.

Babbah ma ciwon zuciyarsa yaso Tashi Amma ya daure ya cirewa kansa quncin sbd bazaiso ya Kwanta Ciwo sbd Mam ba,

Abu daya ya sani shine Babu uban da zai Saka ya bawa JAMAAL SEELAH yarsa,
A halinda ake Ciki shi yanzu yafi son ma ayi tashin duniya kowa ya huta Dan wlh yaqi kawai yakeso ayi kowa ya dauko makami ayi yaqin tashin duniya,

Su Mam ba finsa iya taadanci sukai ba ko finsa iya daukan Rai kawai shi Bai taba bane Kuma baya fatan ya dauki ran kowa sbd imaninsa da nasu ba daya ba Amma da kisan ba laifi me girma bace da tini yayi gaba da gaba dasu Mam yasan ko Bai kashe su duka lokaci daya ba to zai kashe dayan qwallon Dan taadan daga baya yaji da Mam.

Kuma babbar Saar da akaci shine manyanci da tsufa daya Riga yazo masa Koda su mam sukai musu duka taadancin da sukai da a Lokacin kuruciya da samartakansa ne da wlh Shima ‘dan tawayen zai zama sai ayi kashe kashen da dalili.

Kwana babbah yayi a zaune Shima zuciyarsa na radadi da zafi cikeda masifu kala kala yanajin idan Mam ya kutsosa da yawa wannan karan zasu San nasa kalar taadancin yafi nasu,

Likitan ma bayan ya duba Dad Omar anyi anyi babbahn ya bari a dubasa yaqi bari qarshe Shima Ameeenatou din ya Saka tai masa alkawarin bama zata sake tada maganar auren uban kowa dayake kanta ba kodai a warwaresa ko ya dauketa su tafiyarsu inda idan Mam ya isa ya samesa acan ya nuna masa kalan nasa Shan jinin da zai iya Shima sbd shi bayama Saka baturen ‘dan nasa sbd kansa da gangar jikinsa bazai iya daukan abinda zaayita Yi dinba hakama haka kawai aure da turawan da kowanne lokaci zasu iya tattarawa suce sunbar qasar sun koma qasarsu Dan yasan JAMAAL da Dr Aleena bazasu taba iya zaman har abada anan ba har gwara Haroon shi ansan bazai taba rabuwa da mahaifinsa ba, Shikuma kafirin mahaifin nasa bazai taba iya barin qasarsa ba sbd anan yakeda power ta barnarsa ana Gani ko an Sani a rufe.

Acan bangaren Didi ma dakin Fatmah ta kwana tana lallabata sbd Kar asan abinda yake zuciyar Fatmah din sbd Kuka takeyi sosai kaman ranta zai fita sbd tashin hankali da baqin Cikin da Bata taba jinsa ba,

JAMAAL ake maganar igiyoyin aurensa Suna kan AM ba tin yanzu ba tin shekaru,

Ko wata macen akace Yana aure ko Shirin aure zuciyarta kusan bugawa zatai Amma ace Ameeenatou yake aure gaba daya,

Wace irin masifa ce wannan?
Meyasa AM koyaushe take shiga gabanta?
JAMAAL Seelah datake Jin komai zata iya zama ko Yi akansa.

Kuka takeyi sosai tana Jin zuciyarta na sake shiga zafi da tafasa harma da baqin Cikin kasancewar itace a qarqashin Ameeenatou sbd itace asalin ‘yar Omar ba ita ba duk a bayyane gurinsa ba banbanci.

Hafiz ma a zaune ya kwana Yana rasa lamarin kawama da tinanin kamawa ace kwatsam auren Wani ne akan AM batareda saninsuba tsawon shekaru,

Nauyi zuciyarsa tayi tana Dan daukan zafi da ciwon ace Ameeenatou aka daurawa aure Babu ko dayansu Babu saninsu sbd duka masifun rayuwar da aka jefasu,

Wani Ciwo yaji ya sake mamayesa
Rasuwar Yaya Abdul ta dawo masa sabuwa sbd Shima ayau da Yana Raye da ciwon da zaiji da radadin hakan zaiyi yawa sbd koyaushe shine me fadar shine zai zama waliyin auren Ameeenatou,
Shine zai aurar da ita ga duk wanda takeso yakaita gidan mijinta,
Yayi mata alkwarin aurar da ita ga wanda takeso Koda kowa bayaso ya Kuma miqa masa ita idan har baida kowacce irin illan da zata cutatar da ita ko illar da musulunci ya Hana.

Ayau da Abdul din baya Raye shine wannan Alkwarin ya dawo kansa na aurar da ita ga wanda takeso sedai Kuma kaddararta ta Hana hakan sbd auren ya Riga ya hau kanta Babu saninsu,

Kuma auren yaxo a inda Babu wanda ya aminta dashi bare karbansa,

Aure ne da babu me niyar karba har ita AM din,

Shi a nasa bangaren ya shiga shock da tashin hankali kaman kowa Kuma Bai aminta ba Shima Amma Kuma bayason ayi gaggawa ko tashin hankalinda zai Saka asan akwai abinda suke boyewa na AM din ta haifi babyn da basusan ubansa ba.

Duka duka shi wannan tashin a gurinsa Abu daya ne abinda AM keso shi zai tsaya akansa,
Idan tace batason auren Nan Babu wanda zai sakata yinsa kaman yanda idan tace tanason auren Koda kowa Bai yarda ba zai tsaya mata akan hakan.

A duka wannan tashin hankalin shi farin Cikinta shine nasa hakama abinda takeso shine raayinsa.

Dadah kuwa duk inda babbah ya tsaya a raayi anan ta tsaya hakama Kuma batason a daga hankalin AM da wannan zancen tafison Abi komai sannu.

Acan bangaren Mam kuwa hankalinsa kwance yake Babu damuwa ko fargaba komai
Mum Atee ma datason Jin komai Dake bakinsa Bai ce mata komaiba sbd daman Bata sanin duk Wani sirrinsa sbd Yana sane da hadin bakinta da lameenu da BB,kwanto yayi mata itama sbd daya bayan daya zai bisu bazaiyi garaje ba.

*******
Washe gari da safe gidajen tsit Babu Wani me doguwan walwala ko motsi kowa ransa Babu Dadi a hakan suka wuni
Dad Omar ma kwata kwata Bai saukoba sai dare bayan ya Dan warware ya sauko sukai sallah a masallacin Mansion din Dake daga waje suka dawo gabaki dayansu hadda babbah da Shima sai magrib ya samu fita sai Kuma yanzu ishai da suka hade gabaki dayansu.

Dinner suka zauna gabaki dayansu a babban dakin cin abincin gidan harda babbah da kowa da kowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected