AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Rokonta sister Ashley tafara yi sbd kanta zataje ta wanke mata kaman yanda ta Saba duk sati tana wanke mata Kai ta gyara mata farce harma da kunnuwanta duk sai an tsaftace mata.

Sanin ba zata sauko dinba ya Saka sister Ashley juyawa taje ta kirawo cleaner akazo da mopper dole aka hau mopping din dole Wanda babu ruwan komai aka ringa matsewa ana nuna mata.

Saida suka share Mintina sosai ana goge koina a dakin kafin sister Ashley ta kalleta cikeda kulawa tace

“Kingani an goge?
Zaki yadda yanzu muje ayi wankin kan??

Dago fararen idanuwanta ta dago daga kallan qasan ta zubawa sister Ashley din tareda gyada Kai ahankali tana miqa mata kafafunta tace

“Shoes”

Cikin Jin dadi da sakin fuska sosai sister Ashley ta Saka mata takarman tana cewa

“That’s my sweet girl”

Ana Saka takarman clearner ta fice daga dakin tana murmushin Rigiman Ameenatou da kusan ta banbanta data sauran Dan da patient din da dakinta yake kusa Dana Ameenatou dinne da yanzu ta ringa ihu tana tsalle da Watsi da pillow akan ruwa ya cika dakin zai kasheta.

Saukowa gadon tayi sister Ashley ta kama hannunta suka nufi toilet bayan ta dauki basket din da komai da zasuyi amfani dashi Yana cikin.

Normal shampoo ne ba Wani me tsadan ko kyau ba,

Kujera ta janyo mata ta Roba ta zaunar da ita tareda zare mata kayan jikinta ahankali ahankali ta barta daga ita sai halfvest me taushi data kwanta jikina sai qaramin wando gajere da Shima da baida nauyi.
#MAMUH#
#BEST LOVE
#AMEENATOU
#DR JEEY SEELAH
#ROMANCE
#THE SEELAHS
#THE JADENS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
62
Wanke mata kanta tayi fes batareda ta Bata matsala ba kaman yanda ta Saba sbd bataso Amma hakanan yau ta tsaya da lallabawa aka wanke ta taimaka akai wanka suka fito da ita ta dauro mata qatuwar towel.

Goge mata kan tayi da kyau tareda jikinta sai data fara shiryata tsaf cikin uniform dinta marasa nauyi kafin taci gaba da goge mata kan ahankali sbd Baa shigowa da duk wani electric Abu asibitin bangaren patients Dan haka duk sukai wankin sedai suyita gogewa tana fecewa da harya Bushe ta gyara mata shi.

Kafin su gama clearner din Dake mata wankin Ameenatou din ta kira tazo ta kwashi kayan da suka jiqa ta fice dasu Dan wankewa.

Duk abinda zai Saka a taba kan Ameenatoun Bata so Dan haka kwata kwata taqi yadda a gyara kan haka ta ringa fadan zafi take Ji tana qin tsayawa karshema guduwa tayi daga kan gadon Cikin sa’a kofar dakin a Bude take ta fice.

Sister Ashley tashi tayi tabi bayanta tana kiranta da sunayen datasan zasu Sakata dawowa masu dadi Amma Sam Bata tsaya ba saima hanyar dakin ziyaransu data nufa tinda can kadai ake tafiya da ita idonta a Bude idan siddeeq ze taho Amma idan zaa tafi dasu dakin checkups nasu rufe Idanuwansu akeyi sbd suna ganin an dosa hanyar zasu fara ihu da hauka suna qwacewa Basa son zuwa ko kadan Dan duk haukan patient akace dashi aka dawo dashi alluran da akeyi musu sai mutum ya kwana biyu jikinsa amace komai Baya iya yi bayan kallo da idanuwa sbd ba qaramin jigatasu takeyi ba duk karfin haukanka kuwa.

Sister Ashley da Taga inda Ameenatou ta dosa saita waske ta mayar da abin nasu wasa sbd zaa iya dauka jikinta ya rikice ne Dan haka dole ta Maida gudun nasu wasa suka ringa guje guje sai ga Ameenatou din na dariya a karo na farko bayan zuwanta asibitin Dan sedai ta Dan murmusa Shima kirgaggune murmushin nata.

Yanda Ameenatou ke dariya ne ya Saka sister Ashley tsayawa tana kallanta gashi Babu komai a kanta bayan uniform din jikinta hakama har lokacin kanta akwai sauran ruwan.

Farin ciki ne ya cika sister Ashley din Da ganinta a Hakan Dan haka ta fidda wayarta daga aljanunta ta fara yiwa Ameenatou din video da hotina Dan turawa siddeeq Daya kwana biyu batareda anbasa Daman ganinta ba.

Akwai sauran patients da yawa Dake filin wasan na marasa lafiyan sunata wasansu kowa da kalan wasan dayake yi kaman Yara wasu Kuma kwance kawai suke a qasa sunata juyi a a qasa suna dariya wasu kuwa maganace suketa yi ba kakkautawa su kadai suna dariya wasu kuwa zaune suke shiru kaman lafiyansu kalau,

Wasu kuwa masu gata kaman Ameenatou akwai nurses Dake tareda su suna tayasu wasan sbd lokuta da dama nurses harma da likitoci da clearners komawa sukeyi kamar basuda hankalin tukuna su samu Daman communicating dasu Kokuma su samu Daman Basu magani ko wani abin daban hakama a gurin tayasu wasan ma saika koma kamansu.

A yau ita kanta sister Ashley tayi mamakin yanda Ameenatou din tayi Kuma haka suka jima a filin da aka warewa marasa lafiyan Dan shaqatawan tana Taya Ameenatou duk abinda tayi cikeda farin ciki da kulawa sbd yaune kadai Ameenatou ta sake irin Hakan Dan su Basu ma taba zuwa filin ba koyaushe daga toilet sai dakinta sai idan siddeeq yazo sai Kuma idan zaa tafi da ita dakin checkup.

A Haka kanta ya bushe Kuma sai magrib suka koma daki Kuma still bayan sun koma qin yadda yayi a gyara gashin dole haka tabarta dashi ta tafi duba sauran patients din block din da itace zata dubasu.

Tana fita Ameenatou ta koma ta kwanta tareda lafewa kan shimfida kaman ba itace ta gama dariya ba dazu.

Tana Nan kwance Babu motsin komai bare Wani aikin har tsawon lokaci dare ma yayi kafin sister Ashley ta shigo Tama dauka tayi bacci Dan haka Kai tsaye kan ta nufa bayan ta shigo da maganinta da alluranta tareda Wani nurse namiji.

Kallansa tayi tana cewa

“Pls tinda tayi bacci bari na gyara kan na kame mata sai anata magani coz tana tashi bazata bariba”

Ameenatou din ya kalla kafin ya Kalli gashinta baqi sosai Dake kunce din har ya dan sauka kan pillow din da kan nata yake sai fuskanta ta sake haske sosai akan wanda take dashi sbd gashin Dake tsefe,

Gangarowa yayi da idanuwansa akan bakinta dayayi wani Dan ja sbd Shan lips dinta datakeyi tana cizonsu idan Babu kowa sbd ita kusan shine abinda yake bayyanarda juyewan kanta idan bawai Kai sani ba Kokuma tayi Wani abin da zaka ganta zaune to wannan shine abin farko da zai sanar da Akai ba lafiyayya bace.

Lips din nata ya zubawa idanuwansa zuciyarsa na bugawa Dan kuwa kaf asibitin yanaga ba shi kadai ba Babu Wanda ya taba Ganin Ameenatou a wannan yanayin sbd tsananin kiyayewan da sister Ashley keyi akanta ya Baci shiyasa kusan ta tare asibitin ko gida Bata wani zuwa sai dace ta koma kusan da ranar shift dinta da ba ranar ba koyaushe tana asibitin.

Baiji abinda sister Ashley ke fada ba sbd Nisan da yayi a tinanin da kallan halittar dabai taba tsayawa ya Gani a gurin mata da yawa ba sbd rashin time dinsa Shima sosai a waje kullum Yana asibiti.

Sister Ashley data hau gadon janyo Ameenatou tayi gabaki Daya jikinta ta Dora kanta akan kafafunta tareda daukan band mara matsewa zata kame mata kan kawai Dan tasan Babu Daman gyarawa yanzu dare yayi Dan kusan 9 ne na Daren.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected