AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Wani yawu nurse Fahat ya sauke Yana kallan farar fatar Dr JEEY din dake bayyane tana daukan idanuwansa kaman Bai taba shiga Rana ba hakama ganin Ameenatou din jikinsa ya gigitasa gaba Daya Dan haka ya yunquro zaiyi magana Dr JEEY ya dago daidai Nan ya zuba masa idanuwansa take ya rude yafara kame Kame Yana Neman Isa bakin gadonta Dan dauko allura ya bawa Dr JEEY din yayi mata Amma Jin har lokacin idanuwan Dr JEEY din akansa suke tini ya nufi kofa batareda ya juyo ba sauran nurses dinma bayansa suka bi suka fice gabaki dayansu cikin mamaki da shakka harma da cigaba da Kiran Dr Dee.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#AMEENATOU SEELAH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
68
Sister Ashley kadai aka bari a dakin tana zare ido sbd ita kadai tace yanada alaqa da Ameenatou din to Amma itama batasan wace iri bace hakama kota sani batada niyar barin kowa ya sani Kaman yanda Bai nuna komaiba ba Shima Dan sanin cewan shidin akwai alaqa ko family nata ne to tabbas bazai samun Daman kulawa da ita yanda ya kamata ba.
Kasa kallansa sister Ashley tayi gashi har lokacin Ameenatou din sosai take kuka duk da ta Dena fizgewan hakama ko kadan Bata sakesa ba Kuma batada niyar sakin nasa.
Dan kallan gefen sister Ashley din yayi Kai tsaye ya buqaci data matso ta tafi da Ameenatou din.
Matsowa tayi a natse cikin sanyi da kulawa me tsanani da rarrashi ta miqa hannu tana cewa
“My sweet baby zo muje na ayi wanka ayi shirin bacci ko??
Hannunta na sauka kan jikin Ameenatou din ta turesa da jikinta batareda ta saki Jeey din ba saima sake shigewa jikinsa datai kukanta na raguwa sosai zuwa mara sauti.
Sake matsowa sister Ashley tayi tana ambatarta da sweet sweet sunayen data saba kiranta dasu da rarrashi da komai amma kwata kwata Ameenatou din taqi sauraronta saima Neman fasa sabon kukan datakeyi tana ambatan sunan Haroon din datake maqale dashi.
Ganin hakan shima ya sauke numfashi a hankali me dumi tareda kallan sister Ashley din a natse da sauti mara qara yace
“Its okay zanji da wannan din”
A natse ya daga hannuwansa ya Dora a kafadun Ameenatou ahankali
Tanajin Hakan ta sake qanqamesa har lokacin bori takeyi musu.
Shi kansa duk yanda yaso cireta daga jikinsa kasawa yayi idan har ba qarfi zai nuna mata Wanda bama me yiyu bane.
Sister Ashley ya sallama itama ta fice Koda ganin tafiyanta zai saka Ameenatou din ya sakesa Amma Hakan bai yiyuba sedai ta Dena kukan sedai Hawaye.
Ganin Babu kowa a dakin ya Sakata sassauta riqon datai masa tinda Babu Wanda zai raba dashi yanzu.
Bakin gadonta suka nufa tana gefen jikinsa maqale suna Isa ya nuna mata bakin gadon akan ta zauna da ido sbd baima da sauran energy na magana a yanzu.
Qin motsawa tayi daga jikin nasa San batada niyar barinsa bare zaunawa din.
Jikinsa gabaki Daya bayajin dadinsa sbd mutanen Daya tattaba da Kuma yanda itama ta tattabasan dan haka kwata kwata bayajin dadi da nutsuwan jikinsa.
Zareta yayi daga jikinsa tareda zuba idanuwa idanuwansa akan fuskanta datai ja itama sbd kukan datasha sosai da tashin hankalin da Akai.
Kasa ci gaba yayi da kallanta sbd rashin sabo da yawan kallan Dan haka a natse ya daure dole ya kamo hannuwanta duka biyu ya zagayo da ita gabansa da kyau suna fuskantar juna ahankali cikin wata miskilalliyar sauti me cike da nutsuwa yace
“AM….” Kasa qarasawa yayi sbd Baisan tayaya zai furta qarshen sunan ba a bakinsa Dan haka da idanuwansa da sukai ciki datake kalla da nata innocent idanuwan da sukai ja batareda tace komaiba Dan kuwa tsananin sonsa da son komai na halittan da Allah yayi masa kaman a jininta Allah ya halitta mata ko a daidanta tsananin sonsa takeyi daga ranar data fara dora idanuwanta akansa hakama a yanzu da bata daidai din a jinin dayake gauraye da zuciyanta take Jinsa.
“Sit” ya furta da muryansa Yana sake dagowa ya zuba mata idanuwansa itama sake zuba masa idanuwan tayi kafin tayi qasa dasu ahankali tayi cikinsa zata koma jikinsa yayi saurin yin Baya Yana dafe goshinsa kansa na kasa daukan wannan fitinar da Bai taba tinaninta ba.
Takowa tayi cikin sanyi zuwa garesa Yana ganin Hakan yaji kansa na sake sarawa Dan haka Kai tsaye ya juya ya miqa hannunsa Daya ya dauki maganinta da allura da aka bari ya nufi kofa yana kokarin ficewa ya sanar da nurse data kawo ta shiga ta kula da ita ayi mata Shirin bacci ta kwanta.
Nurse din na Sako Kai dakin Ameenatou din na kawowa kofan biye dashi
Nurse din saurin tareta tayi tareda riqota
Ihunta kawai yaji gabaki Daya block din ya dauka take Fahat Dake kusa Kuma yaga ficewan Dr JEEY din ya fito ya nufo dakin da sauri sedai kafin ya Isa ihun Ameenatou din da raunikan data fara jiwa kanta tini suka Saka sister Aisha Neman taimakon duk nurse Dake kusa da ward attendant da karfi da gaggawa.
Hakan ya Saka Fahat qara gudu sedai isansa yayi daidai da isowan Dr Dee Wanda ya rigasa Isa dakin Yana shiga Babu wata wata ya banka mata allura ya fito dakin kaman munafuki batareda ya tsaya komaiba ya silale yabar asibitin.
JEEY Daya kusa Isa office dinsa ihunta ne ya Sakasu kasa qarasawa ya juyo ya dawo sedai duk gaggawansa kafin ya iso Dr Dee yayi mata alluran harya fice sister Aisha kadai ya tadda a dakin sai Fahat da Yana ganinsa ya silale sbd hakanan yake Jin shakka Dan kishin ganin baturen likitan.
Gadonta ya Isa da sauri daidai lokacinda hawayen azabanta masu tsananin gaske suka gangaro idanuwanta a Bude Amma ya tabbatarda Bata ganin komai ko Jin komai.
Wani irin Abu me tsananin nauyin gaske da ‘dacin gasken suka tokare kirjinsa hakama idanuwansa sunyi jajir.
Sister Aisha na gama gyara mata Kwanciya ta fice daga dakin sbd lokacin barin staffs ward din yayi.
Rasa tinanin komai yayi sbd tafasa da qunan da zucuyarsa keyi kawai ya miqa hannuwansa biyu ya dauketa gaba dayanta kaman wadda Babu Rai a jikinta ya fice daga dakin.
Babu tinani ko shakka bare tinanin rules da qaidojin asibitin dama na aikinsa a matsayin likita sbd zuciyarsa Dake zafi tana bawa kansa zafin ya nufi office dinsa Kai tsaye Kuma dayake dare ne harya Isa Babu Wanda ya Hadu dasu koma ya hadun ayau din zai iya lalata licence na asibitin a rufeta gaba daya.
Yana Isa office din Kai tsaye ya Bude Yana shiga siddeeq Daya dawo kawo masa wasu abubuwan ganin Bai dawoba Kuma yanata Kiran waya baya dauka yasan Kila asibitin zai kwana Dan haka y dawo kawo masa wasu kayan.
Miqewa yayi daga zaunen dayake Yana amsa waya ganin Ameenatou din jikin JEEY din hakama jikin JEEY din dashi da Babu Kaya duk Daya sbd yanda rigarsa take a Bude gaba dayanta harma wasu guraren sun Dan barke.
Kallo Daya yayi musu ya dauke kansa daga kan ubangidan nasa yana basa tareda saurin Isa kofar dakin office din ya Bude masa da sauri JEEY ya shige Baice komaiba