AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Tana jikin nasa ya janyo abin rufa ya rufeta tareda Dora hannunsa Daya a bayanta Dan zaman yayi daidai.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#HOTLOVE
#ROMANCE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
74
Yana rungume da ita idanuwansa a Dan rufe Amma Babu bacci ko kadan a tareda shi har Akai Kiran farko na asuba Akai na biyu ya zameta tareda gyara mata Kwanciya ya rufeta ya nufi toilet ya shige.
Alwala yayo ya fito ya Saka jacket me Dan kauri akan rigarsa ya fice zuwa Masallacin asibitin sallah.
Saida gari ya fara haske tukuna ya dawo har lokacin bacci takeyi sosai hankali kwance.
Time ya kalla kafin ya Dan sake dawowa da kallansa kanta,
Duk yanda take baccin dole tana buqatan komawa dakinta Dan haka wayarsa ya fidda Kai tsaye ya Saka Kiran sister Ashley wadda itama take a tsaye da jiran dawowan Ameenatou din kafin asan Bata dakinta.
Tana ganin Kiransa ta dauka da sauri cikin nutsuwa tace
“Barka da Safiya Dr”
“Barka,tana buqatan komawa dakinta” ya fada a taqaice Yana rasa ta yadda zai tayar da ita daga baccin.
Har sister Ashley ta iso office din tayi knocking kofar ahankali Bai tayar da Ameenatou din ba hakama itama Bata tashin ba Dan haka batareda tinani ko shakkan komaiba ya dauketa bayan ya saka mata farar shirt dinsa datai mata Fadi da yawa sosai a jikinta ya fito da ita.
Kofa ya Isa ya Bude sister Ashley Dake tsaye bakin Kofar da sauri ta dago ta kallesa tareda kallan Ameenatou din ta dauke kallanta akansu sedai bata matsa ba Dan bazai yiyu tabarsa ya tafi da ita a hakan ba kowa zai iya ganinsu kuma hakan bame yiyuwa bane dan haka ta dago ta rokesa akan ya jira takawo kujera ta turata da ita.
Kaman bazai iya jiran ba Amma Kuma Shima tinanin ba yanzu ne lokacinda ya kamata kowa yasan Yama San Ameenatou din ba Dan haka ya koma ciki da ita sedai Bai sauketaba tana jikinsa har lokacinda sister Ashley ta dawo da kansa ya Dorata Akai tareda gyara mata zama ya kwantar mata da kai kenan ta bude idanuwanta akansa.
Sister Ashley saurin zagayowa gabanta tayi sbd ta ganta kada tafara rikice musu akan bazata bita ba,
Shima kallan face dinta yakeyi Yana jiran Rigiman da zata fara akan tafiyan da zaayi da ita sai gashi bata ma motsa ba bare wata rigima sedai hannunsa daya data miqa nata ahankali ta kama tareda girgiza masa Kai alama batason tafiya.
Numfashi mara sauti ya sake tareda Dan dauke kansa tukuna ya dawo da kallansa kanta tareda Dan rankwafowa ahankali kan dole ya Kai hannunsa kan hannunta datake riqe dashi ya shafa cikin Wani lazy voice da rashin son maganar yace
“Please ki tafi da ita zan dawo anjima,
Ina buqatan tafiya gida Ina dawowa I promise zan taho gurinki okay???”
Girgiza Kai ta sake tana Dan sake riqe hannuwansu Dake hade.
Sister Ashley ce ta matso tareda dafa kanta tana shafawa cikin kulawa da lallabawa tace
“Babyn sister Ashley zatai brush da wanka harma da gyara Kai ko? Sai daga Baya Dr JEEY yazo ko???
Girgiza Kai tayi tana Bude Baki tace
“Haroon….
Dauke kallansa yayi daga bakinta Yana Dan zame hannunsa yace sister Ashley din ta tafi da ita kawai.
Janta sister Ashley tayi tana cewa bazataba tana kokarin tashi sister Ashley din ta danneta suka fice take tafara rigima harda fasa kukan da Yana jiyosa daga inda yake tsaye ya sauke numfashi ahankali Yana zuba hannuwansa biyu a aljihun wandonsa harya dena jiyo hayaniyarta da sister Ashley alaman sun shige block nasu.
Juyawa yayi ya dauki key na motansa da wayarsa sai jacket dinsa da laptop ya fito.
Motansa da ita kadaice ta banbanta da dukkanin tarin motocin asibitin na likitoci da nurses da duka staffs nasu dai ya nufa ya shige Babu Bata time ya fice daga asibitin fuskansa sanye da Prada goggles black sbd bayason Koda tsautsayi ya Hadu da Wanda zai ganesa har a sheda Yana Nan.
Gidansa ya nufa Kai tsaye sbd bacci yake buqata Dan kansa ya sake yanda ya kamata.
Yana Isa clearner dinsa na gama Aikinsa ya fice Dan haka bedroom dinsa ya nufa Kai tsaye ya tube ya fada toilet yayi wanka dasu brush da abubuwan daya Saba ya fito underwear da sweatshirt kawai ya Saka ya haye gado ya kwanta tareda lumshe idanuwansa take bacci yayi gaba dashi.
*****A asibiti da familyn Dr Dee kuwa harma da dukkanin ma’aikatan lafiyan na kusa kusa a cikin Lagos din sun wayi gari da baqin cikin mutuwarsa sakamakon kwayoyin Daya Sha da sukaiwa kwakwalwansa karfin gaske duk akan sauyin aikin Daya samu ya kasa yadda da kaddara yasha abinda ya kashesa a banza.
Tini media da sauran kafafen yada labarai suka ringa yada labarin mutuwar rasa da abinda ya kashe din Dan haka da yawan ma’aikatan asibitin musulmai suna gurin halartan jana’izansa da zaayi da yamma bayan angama aune aune da komai an bawa Yan uwansa shi.
****Mam seelah Dake zaune a cikin palonsa zaune cikin farar jallabiya lallausa me tsadan gaske Yana Shan tea mara zafi sosai Yana Dan duba sakwanni a wayarsa kai tsaye yaci Karo da labarin mutuwar Dr Dee wanda ya sakasa sauke numfashi ahankali a natse yana sake karanta Sunan likitan.
Labarin mutuwan Dr Dee din ya karanta tsaf a natse Yana kallan har hoton da aka Saka na gawar lokacinda aka samesa a cikin motansa.
Cup dinsa ya dauka ya qarasa shanye tea dinsa a natse kafin ya jingina bayansa jikin kujeran dayake zaune ya dauki waya ya Nemo sunan number da zai kira ya saka kira.
Ana daukan wayar daga can bangaren cikin tsananin girmamawa bullet yace
“Barka da Safiya Sir Mam”
Batareda ya amsa gaisuwanba Kai tsaye yace
“Ina buqatan ganinka batareda sanin ko Kai kanka ba”
Numfashi bullet ya sake Dan yasan me Hakan ke nufi Dan Hakan yace
“Angama ranka ya Dade”
Kashe waya bullet yayi Yana kallan budurwansa Dake gefensa tana bacci ya tabbatarda baccin takeyi kafin ya miqe ya fice.
Mam ma cigaba yayi da abinda yakeyi Yana amsa wayoyinsa wasu kuma ko ankira baya amsawa.
Karfe goma da kusan arbain Mam ya fito drivernsa Dake shirye Yana jiran fitowansa koyaushe ya taso da wuri ya Bude masa mota Yana masa barka da fitowa Hakama sauran securities din gidan duka sunzo sun masa barka da fitowa ya amsa Yana shigewa motan suka fice.
Yana barin gidan Shima Daddy lameenu ya fito da nasa drivern suka wuce Yana karanta labarin mutuwar Dr Dee din Shima hankalinsa kwance ransa fes.
Daddy lameenu Kai tsaye office ya nufa shikuwa Mam Kai tsaye Wani gurin ya nufa.
Kai tsaye gidan drivernsa suka nufa batareda yace komaiba sbd tin a waya Muji yasan inda zasu.
Suna Isa har cikin gate suka shige da motar inda suka tarar da bullet tsaye haraban gidan Yana jiransa.
Yana ganin motan Mam din ya qaraso da sauri Yana masa barka da zuwa cikeda girmamawa.
Mam din Bai fito motan ba ya dauke glass ahankali tareda dagowa ya Kalli bullet din kallan tsaf kafin ya Bude Baki yace
“Qwayar data kashe Wani likita a Daren jiya kwayarmu ce sbd itace kadai me Saka bleeding ta guraren Nan uku,hanci,kunne da Baki harma da idanuwa,
Babu Wanda yake Siya batareda saninku ba Dan kune Basu bayarwan,
Menene bayanin?
Meye dalilin Daya Saka Lameenu Baku aikin kashesa??
Menene a tsakaninsu?