AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Sir Omar Kaine???

Wani kukan da Babu Shiri na farin ciki ya fashe dashi Yana sauka kan mashin din ya koma gefe tareda sunkuyar da kan Yana kuka Mai ratsa zuciya Dan kashe wayar ma yayi Dan bazai iya kukan a kunnen Omar ba.

Sake Kiransa Omar din yayi sai alokacin yaga numbern Nigeria ce take ya qarasa rudewa kukansa na qaruwa ya amsa.

“Hafiz Address naku kadai zaka tiro yanzu zan sameku aduk inda kuke indai a Nigeria ne,
Sbd sakonka da muka samu a shekaran jiya yau dinnan na sauka Ina Nigeria da kaina zan daukeku dukanku mu tafi inda ya kamata.”

Hawayen Hafiz qaruwa sukai sbd harya cire tsammanin samowa yar uwarsa kudin da dole zaa buqata.

Hannuwansa har rawa sukeyi ya rubuta komai ya turawa Omar din tareda share hawayensa ya buga mashin da Dan abinda ya samu na cinikin dayayi ya buga wayar Babbah ya bisu zuwa asibiti.

Yana Isa asibitin ya tararda ance Aiko zaa yiwa Ameenatou din Dan haka hankalinsa yayi mummunan tashi take damuwansa da radadin zuciyansa suka ninku.

Dadah idanuwanta wata irin bushewa sukai hakama Babbah kowannensu kallo Daya zakai masa ka hango tsagwaron damuwa da qunci tattare dasu.

An samu anbata taimakon gaggawa nakudar ta Dan lafa Dan haka akace su tafi su Nemo kudin aikin kafin dare.

Babu zabin Daya wuce Babbah fita zuwa nema Shima Hafiz fita yayi cikin ruwan saman suka ringa yawon Neman kudi,

Dadah da aka bari kuwa zucuyarta sai tsinkewa takeyi sbd fargaba da tsoro tareda tashin hankali.

Duk ruwan saman da akeyi akan Babbah da Hafiz suka qare Dan haka tini Babbah ciwo yafara kokarin rufesa Amma ya danne yaci gaba da yawon daqyar ya hada dubu 7
Shikuwa Hafiz karshe dai guraren 9 na dare mashin din nasa ya siyar ya nufo asibitin hankali tashe jikinsa har wani rawa yakeyi sbd tashin hankali,yunwa kishirwa da zazzabin dukan ruwan Daya wuni yanasha.

Shigowansa asibitin yayi daidai da shigowan wata fitinanniyar motar da kaf asibitin Basu taba samun ziyarar Bako Mai irinta ba ta shigo asibitin tareda parking.

Ahmed ne ya Bude kofar gaba ya fito a natse cikin blue shaddda me tsananin tsada sai kofar Baya da aka Budewa farin kyakkyawan dattijon da kwatjinsa ya cike gurin gabaki Daya.

Babbah ne dayake zaune Yana rawar sanyi zuciya na cikin qunci yafara ganinsa bakinsa na rawa ya furta “OMAR”

dadah ce ta juya da sauri ta Kalli gurin hakama Hafiz cak ya tsaya daga inda yake tsaye cikin tsananin mamakin Daya Sakasa sakin ledojin hannunsa Yana kallan Omar din zuciyarsa na cika da dukkanin farin ciki.

Shi kansa Omar dukkaninsu yake kallo yanajin Kauna da tsananin tausayinsu Yana yanka koina nasa yanajin tabbas alkwarin daya daukarwa kansa na bazai sake rabuwa dasu ba har abada Yana sake ratsashi sbd lokaci yayi na ya bayyanawa duniya yarsa dasu Babbah a matsayin ahalinsa na jini Dan kuwa Dadah kamar jininsa take tinda kanwar kasim dinsa ce.

Tin kafin ya qaraso gurinsu wata nurse ta fito a masife tana cewa

“Ina iyayen Ameenatou Nuhu Babbah?
Kun shirya kokuwa haryanxu Baku samo kudinba mu kyaleku duk abinda ya sameta ko babyn laifinku ne,
Idan Kun samo kudin kuje ku biya komai Nan da awa Daya zaa shiga da ita tiyatar.”

Juyawa tayi ta shigewanta ciki.

Kasa motsi Omar yayi hakama Ahmed sbd Jin Abinda nurse din ta fada.

Babbah ne da tashin hankali da masifar tayi masa tareda tsananin ciwon dayaketa dannewa tin dazu suka Fi karfinsa ya yanke jiki ya Fadi a gurin.

Taimakon gaggawa aka fara basa batareda an tsaya zancen komaiba Kuma Ahmed take ya gabatar da komai suka dauke Ameenatou da cikinta ya Saka Dad dinta kusan yanke jikin Shima Amma ya daure suka kwashesu daga asibitin ko wata asibitin Basu tafi ba ticket kawai suka Siya suka wuce abuja direct dasu Hafiz kawai aka bari ya hado duka sauran takardunsu da abubuwan buqatansu ya biyo bayansu da tsakar dare Shima ta jirgin.

Suna Isa abuja Kai tsaye wata tsadaddiyar asibiti aka wuce da Ameenatou din wadda ta qarasa gabaicewa sosai,

Duba da yanayinta Babu bata lokaci aka shiga Cs da ita shikuma Babbah dubasa Akai tareda Kwantar dashi a Wani lafiyayyan daki acan sama Mai komai a tsare kaman ba asibiti ba.

 

*********
Anyi CS din Ameenatou lafiya an Ciro mata lafiyayyan baturen Babynta Namiji Wanda girmansa kadai zai sake tabbatar maka sa lafiyayye ne.

A hannun Alh Omar jden aka miqa babyn wanda yake kamanni Sak da Ameenatou din sedai haskensa yayi yawan da yazo a bature sosai sbd gashinsa ma ba kaman na babies dinmu bane.

Shiru yayi tareda zubawa babyn idanuwansa jikinsa na sanyi Amma Kuma har cikin ransa yakejin kaunar babyn tinda ya Riga ya kasance jinin Ameenatou dinsa Dan haka baida zabin Daya wuce ya kaunacesa koma waye ubansa Dan yaji bayanin komai a bakin dadah da Hafiz.

Babbah Yana Dan Jin jikin sosai Dan haka shi hutawa sosai aka barsa yayi ya samu ya warware.

Ameenatou ma Ko data farfado har lokacin Hawaye ne ke gangarowa daga jajayen idanuwanta da suka kasa komawa daidai Kuma har lokacin ta kasa iya furtawa kowa kalma ko Daya bayan hawayen datake sai Kuma lokacinda aka kawo mata babyn ta fashe da kuka me sanyi da daci.

Tsananin so da tsanar babyn takeji lokaci Daya sedai son Yana kokarin rinjayar qin shiyasa take Kukan tausayawa kanta da shi kansa babyn tareda babbahnta da Yaya Hafiz dinta da dadanta sbd tasan kaddararta tasu ce su dukan me dadi da mara dadi,ta farin ciki data baqin ciki.

Dad Omar ne yayiwa babyn huduba da sunan babbah wato NUHU OMAR JADEN,
Hafiz kuwa Daya karbesa duba da ayau ranar arfa ce sai kawai ya ambacesa da ARFAT.

Ahmed ma addua yayi masa sosai kafin Kuma yafara kokarin fara binciken asibitin da Ameenatou din tayi zama Dan Gano komai su dauki matakin daya kamata sai Dad Omar din ya dakatar dashi sbd yanason dukkaninsu su fara dawowa daidai tukuna Kuma tinda zasu dawo Nigeria ne kwata kwata da zama wannan Karan ba gudu ba ja da baya ya shiryawa su Mam tsaf to abari ya dawo din saisu bi komai a yanda yake amma yanzu yana buqatan tafiya dasu Ameenatou din gabaki dayansu saisun huta sun samu sauyin daya kamata tukuna so afara yi musu komai na buqatan tafiya a cikin satin nan nakeson mu wuce.

***Hakan kuwa Akai a cikin abinda Bai gaza sati biyu ba kafin ma kowa yasan da Yana qasar aka gama musu komai cikin sati na uku suka tattara gabaki dayansu suka bar qasar gabaki Daya zuwa France tin daga Babbah har Dadah da Hafiz Babu Wanda aka bari tareda Sabon hasken idaniyar dukkaninsu waton baby ARFAT.

Isarsu sosai Mum Noor tareda Aunt Didi sukai mamaki tareda farin ciki Mai tsananin gaske na ganinsu musamman Mum Noor datasan yanda Omar yake azabtuwa da rashin Ameenatou ‘yarsa.

Basuyi mamakin ganin Arfat ba sbd tin a waya sunji komai Dan Haka Babu Bata lokaci aka fara bawa Ameenatou da har lokacin bata cikin walwala ko farin ciki ko kadan kulawa.

Babbah ma asibitin da zaa sake dubasa da kyau kafin ya zauna gida aka Kaisa Saiya kwana biyu acan ya warke sumul kafin a dawo dashi gida.

Hafiz kuwa Jin yayi Allah ya karbi adduarsa ya kawo musu agajin gaggawa da Basu taba tsammani ba daga inda basa zato.

Dadah ma ganin Babu sarki sai Allah Babu wata dubara bayan karban sabuwar rayuwar da suka tsinci kansu aciki ta dangana ta karba sbd ko a zance batajin ana ma fadar ga ranar da zasu koma gashi ita rayuwar Mansion dinma kaman bazata iya ba dan duka ahalin gidan basa wani jin hausa daga Ahmed Se mai gidan sa kansa kawai suke jin hausan data kamata itama duk dai ba irin yansa kowa ya iyaba harshensu ya juye da yawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected