AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Cikin zafin zuciya hannuwansa na sake rawa ya kalleta yace
“Meyasa Kuka boye min?
Kin bawa Jamaal shawaran a boyemun ne sbd daman kin shirya auren Omar din?
Waye ya bawa Omar daman auren matar datake uwar yayana Matata….
Cikin baqin Ciki da Jin zafi ta katsesa da cewa
“Mam Babu ranar da bana baqin Ciki da Danasanin auren daya taba shiga tsakanina dakai,
Badan su Jamaal ba wlh tallahi da tini na Dade da miqaka hannun hukumar qasar Poland sbd acan kaje ka kashe rayuka fiyeda biyar ka tsallake ka tahowarka,
Babu wanda yake tareda SEELAHs yayi mutuwar Allah batareda kune Kuka kashesa ba,
Me zaka fadawa Allah a ranar daya tadaka ya tsayar dakai a tsakiyar wainda kukai sanadin rayukansu?
Kasan meyasa ‘danka ma daka Haifa ya tsaneka baya kaunarka sbd kawai ka kasance mara Imani ko digo daya acikin ranka Mam,
Babu ran dayakeda Mahimmanci a gurinka bayan naka,.wace rayuwa ce wannan??
Kanta yayo koina jikinsa Yana rawa sbd Abu biyu Dake Neman kashesa da ransa kallanta amatsayin matar Omar da Kuma boye masa jikansa da daya sani da yanzu Wani labarin akeyi ha wannan ba Dan Babu wanda a duniya zai Hanasa karbansa Koda kaf ahalin jdens da seelahs zasu mutu ne.
Sake shaqeta yayi Cikin tsananin zafi zuciya da tiriri Yana cewa
“Wallhi tallahi alqawarine nayi har abada Babu namijin da zai aureki Banga bayansa Dan haka wlh Omar idan ban kawar dashi akan dukiyarmu da itace silar komai to tabbas tabbas zan kawar dashi daga duniyar gaba dayanta sbd aurenki da Kuma jikana Arfat daya rabani dashi ya boyesa.
Cikin azaban datake ji tace
“Mam Babu wanda bazaka iya kashewaba na sani tinda ka kashe ‘dan uwanka Rabin jikinta lameenu da iyalinsa kaf tareda matarsa Ateeka to Amma ka sani nikuma idan Ina Raye inshallah bazaka taba Omar ba sbd bazan barka kayi hakan ba sbd Son danake masa shine Asalin son daka rabani dashi tin lokacin kuruciyat……
Wani Azababben Mari ya sauke mata Yana Jin kansa na Neman kamawa da wuta sbd abinda yakeji Dan gaba daya zarewa yake neman Yi,
Baida komai a Lokaci daya matarta ta aure amininsa Kuma Dan uwansa hakama yanada jinin dayake tsananin so an boyesa hakama baida kowa ko gurin zuwa sannan tana Dora masa da asalin son gaskiya datakewa Omar.
Shaqeta yayi da karfi Yana marinta Yana cewa
“Idan bazan iya kashe Omar sbd Raba wannan auren ba mutuwarki itace zata Raba auren wanda wlh bazan barsaba”
Bakinta ne yafara fidda jinin Marin qarfin dayake mata Yana sake shaqeta numfashinta na kokarin barin jikinta sbd tsananin azabar da bata taba jintaba a duniya.
Hawaye masu zafin gaske ne suka gangaro mata gefen Idanuwanta tana Bude Idanuwanta daqyar ta kallesa Shima wasu irin hawayen ne masu tsananin zafi da Ciwo suke taruwa a Idanuwansa sbd radadin dayake ji a zuciyarsa Amma ya zabi tabar duniyar gabaki daya ya huta..
Ayesha datake bakin kofar tin lokacinda suke magana sbd ganin shigowansa gidan ya sakata fitowa Dan rabonta dashi tin lokacin rasuwar hakama Bata taba waya dashi ba sbd Bata samunsa ba Dan haka ayau din Cikin Jin sanyi da farin Cikin ganinsa tinda shine matsayin mahaifinta ta fito Kai tsaye sbd farin Ciki da tsautsayi batai tinanin komaiba ta bisa saman bayan siddeeq ya fice kenan sedai abubuwan dataji ne suka sumar da ita tsaye bakin kofar palon tana kallansu da jinsu Cikin mummunan shock da masifar datafi karfin hankali da tinaninta.
Ganin Dr Aleena na kokarin mutuwa a hannunsa da Kuma hayyacinta data Dade da ficewa sbd tashin hankalin da firgicin abinda taji
Ko Gani Batayi ta miqa hannunta kan console Dake gurin ta dauki wata qatuwar crystal me tsananin nauyi da tsinin shape din Kibiya ta daga da karfi zata kwada masa Jin motsi bayansa ya sakasa juyowa batareda ta saki Aleena dinba daidai juyowansa daidai Ayesha din na cakowa da karfi take gabaki daya tsinin ya ratsa tsakiyar idonsa na Dama take ya sake Aleena da qargi Yana yin baya jini na Wani irin bartsi daga idonsa.
Ayesha na ganin hakan ta buga Wani irin ihun tashin hankali da tsoro jikinta na jijjiga.
Aleena datake zube a qasa kasa motsawa tayi sai kokarin fidda numfashi takeyi Cikin tsananin azaban gaske.
Maman fadeela da Siddeeq dayake shigowa palon qasa lokacin sbd ya damu Damar magana dasu Jamaal take sukai saman da mugun gudu hankalinsu tashe.
Suna shiga da jinin Mam Dake bartsi suka fara cin karo take maman fadeela tayi baya tana buga Wani ihun itama siddeeq kuwa da tsananin gudu ya isa gurin Mum Yana kokarin kamota sedai Bata iya ko motsawa sosai ga jini bakinta sosai.
Daukanta yayi da sauki gabaki dayanta tareda saukowa da ita daidai Nan su babbah da Hafiz suka shigo gidan sbd dabai samu Jamaal ya dauka ba da Dad Omar Hafiz ya kira sbd tinanin Yana office din Shima sedai Yana gida tareda babbah Suna Jin abinda yake faruwa take babbah ya fito sbd yasan waye Mam da abinda zai iya Yi.
Siyam datake gurin dadah zaune a kujera tanajin sunan Mam take ta sauke ajiyan zuciya me sanyi tareda rufe Idanuwanta Wanda ya Saka dadah kallanta cikeda mamaki sedai Gani Bata motsaba ya sakata tashi tabi bayan Hafiz tana cewa ya kula sbd kada zuciya ta dibi babbah yayi Wani abin.
Babbah na shigowa gidan ganin halinda Dr Aleena take Ciki Cikin tsananin tashin hankali da mamaki ya Kalli Mam Dake fitowa Cikin mummunan hali kafin kowa ya Ankara tini babbah yayi saman ba tausayi ko kadan a ransa Shima ya Saka qafa ya shuro Mam din qasa take yafara gangarowa idonsa na qarasa tsiyayewa Cikin tsananin azaba.
Daidai Nan Jamaal ya fara shigowa gidan kafin Dad Omar sedai kusan a tare suka iso Cikin palon suka hade da Siddeeq Dake dauke da Mum Bata Wani dogo motsi.
Hannuwan Jamaal ya miqa zai karbeta daidai Nan Omar ma ya miqa nasa hannuwan Siddeeq ya miqawa Omar din ita Suna juyawa zuwa mota.
Cikin gaggawa duka motacin kusan guda uku suka fice zuwa asibitin gabaki dayansu.
Suna fita gidan Siyam Data biyo hanyar gidan itama ta iso gidan tana shigowa Cikin saa Babu kowa San sun manta da Mam din Dake yashe Cikin jini Yana kokarin tashi zuciyarsa na kokarin bugawa da baqin Ciki me tsananin gaske.
Kansa ta tsaya ahankali tareda zuba masa Idanuwanta da sukai Wani irin Jan gaske hannuwanta na rawa ta dago syringe din dayake hannunta na alluran dabbobi me karfin gaske ta kalla tareda kallansa.
Shima Cikin tsananin azaba da rashin Gani sosai da idonsa daya ya dago ya kalleta Yakuma tabbatarda Siyam dince sedai Bai iya cewa komaiba.
Daga syringe din tayi tareda saka masa a wuya ta tsiyaye masa ruwan hawayen masu zafin gaske na tsiyayo mata.
Wata mummunan fizga yayi tareda fizgota ya shaqe a tsakiyar hannunsa Yana Shure Shure itama fizge fizgen tafara a jikinsa sbd shaqura.
Daidai nan siddeeq da maman fadeela da Ayesha suka dawo Cikin gidan Suna Gani da gudu siddeeq ya iso ya cire Siyam daga jikin Mam din sedai kaman Babu Rai a jikinta Dan haka ya dauketa da gdu ya fice
Sbd tsoro su Maman fadeela ma binsa sukai daidai Nan Ahmed ya shigo gidan Shima da jamian tsaron da take suka kwashe Mam din sedai jinin dayake fiddawa daga bakinsa da hancinsa ya Saka dole asibitis
Shima aka wuce dashi sbd yanayinsa ba kyan Gani.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
141
Bayan barinsu gidan Jamaal Kai tsaye asibitin jdens aka nufa da ita Omar zuciyarsa kaman zata fashe sedai shiru Bai iya cewa komaiba bayan kallan fuskan Aleena din datai tsananin laushi.