AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
“To shi “Dan nata me yakeso ayi ne?
“Dad a tausayawa a basa abinda yake nasa?”
Sake kallansa Dad Omar yayi Yana sake Wani mugun murmushi yace
“Matar ‘dan tawa matar baa hannuna take ba,asali ma ba nine zancen yake hannuna ba idan zai iya da babanta ni Dan rakiya ne”
“Kallan Dad Jamaal yayi Yana satar kallan Ameenatou ya sake qasa da murya Yana cewa
“Bazan iya da tsohonta ba dan Allah Dad karka hadani dashi zai iya bacewa bat da itama gaba daya idan aka takurasa musamman yanzu Danai masa Wani laifin”
Juyowa Dad yayi ya Kallesa Kuma a Lokacin kowa yaji abinda ya fada sbd sautin ya Dan fita
Dad yace laifin me Kai masa kenan??
“Yar budurwansa is carrying my second child…..”
Ruwan da Fatmah da Mum Nur suka Saka a bakinsu lokaci daya suka dawo musu da mugun karfi.
Didi kuwa zubewa ruwan sukai a hannunta batareda takai bakinta.
Uncle Ahmed ajiye wayarsa datake hannunsa yayi Yana dagowa Cikin tsananin mamaki.
Siddeeq Wani iskan farin Ciki yaji yayi sama dashi
Ayesha da maman fadeela ma duka dagowan sukai.
Hafiz Ashley ya fara kalla Cikin mamaki da jinjinawa wannan babban barnan da sukai.
Ashley sunkuyar da kanta qasa tayi tana dafe goshinta jikinta na Wani irin mugun nauyi kaman Wadda aka danna Cikin ruwan zafi.
Ameenatou dagowa tayi da Wani irin tsananin mamaki da shock ta kallesa.
Dad Omar kuwa kasa yadda da abinda yaji yayi ya juyo ya zubawa Jamaal din Idanuwansa shikuwa Babu abinda yaji a abinda ya fada sbd baya buqatan jiran kowa ya sanar dashi ko sanar da kowa sbd abu ne daya rasa a Cikinsu na farko Dan haka a yanzu dayake tareda matarsa lokacinda take dauke da Wani Cikin nasa shine yakeda iKon sanarwa kowa.
Tsit palon yayi Banda Tarin Fatmah daya kasa tsayawa sbd muguwar sarkuwa tayi Idanuwanta take sukai jajir ta dago ta Kalli Jamaal din wanda Babu abinda yake shimfide a fuskansa bayan asalin farin Cikin dayake Cikin zuciyarsa bama wannan me yake nufi da second child dinsa??
Gabaki daya su mum Nur ma Cikin mamaki da shock basuma Tina da second child yace ba
Cikin mamaki Didi ta fara Bude Baki tace
“Who’s pregnant??
Ameeenatou qasa tayi da kanta wasu irin hawaye masu zafi na gangarowa daga Idanuwanta batareda ta dagoba Dan bazata iya kallan kowaba.
Dad Omar daya mutu a zaune ahankali ya mayar da numfashinsa kafin ya sake kallan Jamaal din ya juya ya Kalli Ameenatou da kanta ke qasa ya dawo da kallansa kan Jamaal yace
“Waye me Cikin??
Kallan Dad din Jamaal yayi Cikin kulawa yace
“Dad please”
Da tsananin mamakin gaske daya qarasa cinyesa daga zaune ya Jiyo yana kallan Ameenatou wadda ta fasa Kuka kawai ahankali tana sake cusa kanta Cikin kafafunta.
Dr Aleena ce ta Kalli Dad din tana cewa
“OMAR please”
Mayar da kallanta kan Jamaal tayi Wanda yakejin kukan Ameenatou din har tsakiyar kansa da zuciyarsa sedai wannan shine karshen abinda zai kawo masa karshen tasa matsalar da wainda suka Hanasa matarsa yaso ma babanta na gurin yaji idan yaso kafin safe idan ya tashi bacewansa ya bace bat shi kadai Dan ya fahimci sai sunyi rikicin gaske da babbah kafin abasa matarsa.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
144
Kowa kasa gasgata abinda yake faruwa yayi Dan haka har Lokacin tsit gurin yayi siddeeq ne ya taso daga inda yake kafin ya iso Jamaal ya miqe suka rungume juna siddeeq na cewa
“Congratulations to us Dr”
“Thank you Sir Siddeeq”
Dariya siddeeq din yayi zuciyarsa koina cikeda farin Ciki.
Uncle Ahmed ma dai daya tabbatarda zancen gaske ne kallan Jamaal din yayi Yana miqewa suka rungume juna Yana cewa
“Congratulations son”
“Thank you uncle”
Maman fadeela ma Cikin farin Cikin ta tayasa murna ta Taya Dr Aleena da Omar ta zubawa Idanuwanta tana karantar yanayinsa da kowa ya kasa ganewa duk da tasan bazai taba qin cikin daya kasance daga Ameenatou dinsa ne da Jamaal sedai labarin Cikin yazo ne Kai tsaye katsam sbd abune da Babu wanda ya taba tinani ko kawo tinanin hakan ma.
Mum Nur Ameenatou Dake Kuka ta kalla mamaki na kasheta duk Tama rikice sedai kukan nata ya sakata komawa gefenta ta janyota jikinta.
Fatmah Kuka kawai itama akaji ta fasa Wanda ya zaka kowa kallanta itama sedai Babu mema iya tambayar abinda ya sameta sbd har ga Allah mamaki kowa yake cikinsa sosai Didi da batasan ta sake jeho tambaya ba cewa tayi
“Garin Yaya ne wai aka samu Cikin bayan tana gida a gabanmu Bata tare koina ba.???
Wani kallan da uncle Ahmed yayi mata ne ya sakata rufe Baki da abinda ta fada sbd batamasan ta fada dinba sbd rikicewa da mamaki.
Hafiz ma Cikin farin Cikin ya Kalli Dad Omar yace
“Dad congratulations to us”
Maida kallansa kan Jamaal yayi Yana yar dariya yace
“You better be ready for whats coming sbd ba ruwana nima Dan kallo ne a gurin tsohonta,
Congratulations Allah ya kawo babies masu albarka”
Murmushi Jeey yayi Yana cewa
“Baban Nan nata Ina shakkar hukuncinsa duk da Nima na koya irin hukuncin nasa if Baku Saka Baki ya hakura ba bacewa zamuyi kawai”
Dariya Hafiz yayi Yana cewa
“Hmmmmn yafika qwarewa anan sbd kafin kayi tinanin bacewan harya Kai inda zai bacen shi,
Amma shawaran shawo kansa daya ne.,
Matso da fuskansa yayi kusa qasa qasa sbd kada su Dad su ji yace
“Ka tabbatarda ka qarasa gamawa da ‘yarsa duk fushinsa baya iya hanata abinda takeso”
Kallansa Jamaal yayi Yana Wani shegen murmushin ka tabbata hakan?
Murmushi Hafiz din yayi Yana cewa
“U welcome”
Kan Ameenatou JAMAAL ya Maida kallansa Yana mata Wani shegen kallo Mai sanyi da nutsuwa Yana Jin kukanta na sake ratsasa.
Dad Omar ganin kukanta da yayi tsanani Cikin tsananin qunci da kunya takeyinsa dole ya sauke numfashi ya Bude Baki Yana kallanta yace
“Ya isa hakan kada kukan ya Sako Miki Wani ciwon tinda kinsan yanayinki yanzu din”
Maganarsa ta Saka kowa sauke ajiyan zuciya Banda Jamaal Dake jiransa ya tayasa murna.
Juyowa yayi ya Kalli Jamaal din dayake murmushi Yana kallansa yace
“Ka shammaci babanta sbd bazan ce ni ka shammata ba so wannan ba ruwana ba layina bane so congratulations Son”
Rungumesa Jamaal yai yana cewa
“Thank you Dad,Allah ya qaro Nisan kwana da lafiya”
“Amin son Allah ya Muku albarka Kuma dukanku ya sakawa abinda zaa Haifa albarka”
Amin kowa ya amsa dashi Banda Ashley da kaman ruwa ya cinyeta satar kallan Dad din takeyi shi kuwa kallo daya yayi mata yasan tasan da komai.
Ameenatou dai dole Dr Aleena ta Janta zuwa bedroom dinta itada Mum Nur Suna rarrashinta sbd sosai take Kuka tana Jin zafin abinda JAMAAL din yai mata.
Ashley ma silalewa tayi ta bisu Dad da nace mata zaki hadu da Wanda yake daidai Dake ne Ashley.
Tana shiga dakin Ameenatou na ganinta ta sake fasa Wani kukan mara sauti sosai tana Jin fargaban yanda zasu hadu da babbah idan wannan zancen yaje kunnensa.
Mum Nur rarrashinta tayi tana nuna mata ba komai bane Kuma su Kam sunyi Marna da farin Cikin wannan Cikin.
Dr Aleena data rasa yanda zata rarrasheta shafa bayanta takeyi tana fada mata yanda suke kaunarta da duk abinda zata Haifa musu Babu abin damuwa ko Kuka Akai sbd abune da suke tsananin so sukam.
Bayan ta Dan dawo hayyacinta ta rage kukan sosai fita sukai suka barta da Ashley.
Suna fitowa JAMAAL ya Kalli Mum dinsa da Idanuwansa
ta gane abinda yakeson sani Dan haka a hankali tai kissing tsakiyar kansa dayeke zaune gefen Dad din Cikin sauti mara karfi tace