AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ahmed bangarensa daban a gidan Dan haka Shima a nasa bangaren ya sauka hankalinsa kwance.

JAMAAL ma dashi a Cikin Manyan likitocin da aka gayyata Dan daga sunan Mum dinsa sai nasa Dan haka Yana Abujan sedai bama tare suka taho ba Dan yaso tahowa da tasa halal din Amma Sam ko muryanta taqi barin ya sake ji daga ranar bare ganin fuskanta Dan ba qaramin fushi da zafi ta dauka dashi ba Dan haka duka yake Cikin dacin zuciya.

Siddeeq ma duk yanda yaso magana da Ashley ta samu Damar fitowa da am din Dan su dauketa kawai su tahowarsu ya kasa samun Damar wannan maganar da ita sbd babbah daya Saka musu mugun Ido musamman Ashley din dan yafi qin yadda da ita akan kowa ma Dan haka ya Saka mata Ido tareda rantsewa akan duk Wanda ya kamata tana waya dashi shi zai aura mata ko waye sbd maganinsu.

Fatmah ma hakan ya fada mata hakama gabaki dayansu ya sakasu dawowa sashensa ya Kuma hadesu a daki daya sbd su duk abinda zasuyi su shirya Babu shegen da zai zauna zaman shiryasu tinda ba Wanda ya hadasu fadan da hassadar tareda qyashin da zage zagen.

Fatmah kusan zaucewa take Neman Yi sbd ganin su Dad Omar da Dad dinta ko ta kan zancensu Basu sake bi ba alaman hukuncin babban yayi musu daidai Dan haka ta sake dagewa da rokon babbah tana Neman tuba da bazata sakeba Amma ko bi ta kan tubanta baibiba.

Ameenatou dai batada ta cewa bayan komawa salihar gaske sbd Cikin kaman Yana jiran asan dashi sai laulayinta ya dauke tsaf Bata Ciwon komai ko Wani amai saima fitowa dayek kokarin farawa sbd tasowa da mararta tafara Yi hakama fushin datake cikinsa akan Jamaal din Bai saukoba ko kadan sbd kunce mata zani a kasuwa ne yayi duk da tasan a gunsa shi ba komai bane tinda bature ne Amma meyasa baima fara fada mata yasan tana dauke da Cikin nasa ba Wanda itama harga Allah taji tana tsananin son Cikinsu yanzu sbd na Arfat Bata hankalinta ta dauki Cikin ya Renu a Cikinta har haihuwansa.

Ashley dai itama taitayinta ta shiga ta Dena waya da kowa se babbah baya gidan dan sanin rantsuwarsa akan duk Wanda ya kamasu Suna waya shi zai aura musu indai auren ya halasta tsakaninsu.

Hafiz da dadah ne ke tausaya musu matiqa musamman Fatmah data kasa Dena Kuka haryanzu gaba daya ta shiga Wani mummunan hali akan abubuwa da yawa Ciki harda Dad Omar data batawa Dan tasan zuciyarsa ta sosu ko yayane da jin abinda tayi hakama iyayenta fushi sukeyi sosai da ita ga Ameenatou da batajin zata sake ganin mutuncinta ga Jamaal din datai abin akansa ma Ashe mahaukaciya ya dauketa ga Babbah da dauren sadakansa gabaki daya ta rasa inda zata Saka kanta a Cikin dakin ma Ashley da Ameenatou Babu me mata magana mugun zama ne sukeyi gashi kowannensu bai Saba da kwanciyar qasa ba idan ma ka Saba sanyin AC kadai da tiles ya dauka zai iya illata rayuwarka Dan haka bame yafewa haka suke shigewa lafiyayyan gadon dakin Anne suyi bacci Cikin Rufa daya.

Hafiz ne da dadah ke Dan rarrashinsu Suna tarairayansu Amma Didi ko gaisuwan Fatmah din Bata amsawa itada Mum Nur Ameenatou ma Mum Nur tayi fushi da ita akan maganar data fadawa Fatmah sbd tsakanin Dad Omar da Ahmed yanzu Yan uwantaka ce data Fi ta jini karfi Dan kuwa kowa a tare ya gansu a tare ya sansu Kuma alaqa ce data Riga ta zama family bazata taba gogewa ba sbd kaf gidan har Ahmed din kowama yayansa da matarsa da Jaden suke amfani a sunansu kaman yanda yanzu duka harsu Hafiz duka an qara jdens a karshen sunayensu so maganar iyaye da rashin daa ba dabia ko hali bane.

Anyi Taron kwana uku din a Abuja an gama a ranar Jamaal ya dawo Lagos tareda Siddeeq Banda su Mum dinsa da ba yanzu zasu dawo ba sai sun kwana biyu sbd wasu manyan kwararrin likitocin da Omar zai hada da Dr Aleena.

Duk Yanda Omar da Aleena din suke ganin yayansu sun girma Basu San sunada sauran lokacinsu ba sosai Saida suka kasance da juna a kwanakin sbd wata lafiyayyan sanyayyan soyayya ce me karfi da kwanciyar hankali suke gudanarwa hankali kwance.

Omar Jaden Bai baro Abujan ba Saida maganar aurensa ta fita duniya tasan matarsa ta biyu wadda ta fita tareda maganar auren ‘yayansu,

Ya gabatar da Dr Aleena second wife dinsa da Kuma son dayake mata itama kaman yanda yakeson matansa duka Dan haka take aka ringa daukansu hotina ana yadawa Kuma kowanne Suna tareda juna kusan ma duk inda zasu hannunsu Yana riqe da juna hotinan ke fita sbd ita dai baturiya ce hakan ba komai bane gareta hakan Shima tinda kusan haihuwansa ne kadai baayi baturen ba Amma Shima turai dinne kawai.

Bayan dawowan Jamaal duk yanda yaso yaga halal dinsa hakan Bai samu ba Dan Babu fuska a gurin babbah Dan haka dole ya fara lallaba babban sbd sai yanzu yake fahimtar zare hannun da Dad Omar yayi yabarsa dashi yasan karfin zuciyar gaske ne dashi saiya masa tasa karfin zuciyar akan son dayakewa ‘yarsa zai gane shi kwata kwata ma baisan meye kunyar sirikin da ake magana ba indai akan a Hanasa halal dinsa ce musamman yanzu datake fama da laulayin babynsa a karo na biyu.

Ganin take taken Hafiz akan son fitar da Yan matan zuwa Wani gurin su samu su Sha iska kansu ya sake ya Saka babbah taka masa Burkin karya kuskura ya shiga Cikin masu karban hukuncin sbd shi kansa me laifin ne sosai a gurinsa sbd duka halinda Ameenatou take Ciki ya sani shine suka Taru suka ci amanarsa aka barsa a iska qaton ga Babbahn mahaukata ko?
Ya kiyayesa sbd Yana laifi daya wlh dashi zai hada ya Basu baqin mamaki.

Hakan ya Saka Hafiz Dan kama kansa sbd yasan babban idan ya Riga ya dauki zafi akan Abu bare yanzu laifi ne akan duka wainda yake ganin sun Saka ‘yarsa taci amanarsa Dan Bai yadda yin kanta bane zugata yake ganin anyi Kuma ba kowane yayi wannan aikin ba bayan Ashley da Siddeeq da Jamaal din kansa harma dashi Hafiz din.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
147
Siddeeq ne ya turowa Ashley txt a kusan karo na Kila Dari Amma Bata basa reply sbd Shima fushin ya shafesa Dan haka shima baida nutsuwan Dan kusancinsa da Ashley din ya Saka ma yakejin duk ya shiga damuwar rashin daga wayar tasa da fushinta Dan haka ya dage gashi Kuma Jamaal na son magana da AM duka dole sai Ashley din ta basa hadin Kai Dan haka Bai denaba a wuni hakai zaita kira Bata dauka Yana bi da txt tinda shi yasan tana karantawa so da sauki ko Bata bada reply dinba indai ta Gani.

Yau ma txt yayi mata wanda ya saka jikinta sanyi sbd itama tana Cikin damuwar daurewa ne kawai takeyi tana sharewan sbd daga shi har Jamaal su San sun tabasu.

Zubawa sakonsa Idanuwanta tayi kafin ta sauke ajiyan zuciya tana dagowa ta Kalli Ameenatou Dake zaune ta zubawa tv Idanuwanta itama kewane sosai a Cikin ranta Amma Kuma fushinta yaqi sauka ko kadan.

Kiransa siddeeq ne ya shigo wayarta bayan sakon nasa Dan haka sake sauke ajiyan zuciya Ashley din tayi tana daukan wayar sbd babbah bayanan Yana gurin sallan laasar masallaci su Kuma suna palon a zaune Suna Dan kokarin ragewa kansu damuwa, dadah Kuma tana kitchen tareda Mai aikinsu Suna girki.

Ganin sunan siddeeq a wayar Ashley kafin ta daga ya Saka Fatmah Dake kusa da ita sauke ajiyan zuciya sbd ganin kwana biyun Dad dinta Ashley din yake kira yaji Yaya suke sbd Ameenatou ta kashe wayarta gabaki daya ta ajiye ita Kuma Fatmah din Baya kiranta kwata kwata ya Dena Dan haka Ashley dince dole wadda zai kira yaji Yaya suke Dan haka hankalin Fatmah baya kwance sbd Tino rantsuwar babbah duk Wanda ya kamaka kana waya dashi shi zai aura Maka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected