AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Zaune yake shiru har kusan dare sosai kafin ya kwanta bacci ya daukesa Bai farka ba sai asuba.
Bayan sallan asuba da baisan time ba yasan dai lokaci yayi
Yana idarwa sake kwantawa yayi sbd maganinsa akwai masu Saka bacci sosai Dan Mr Jaden ya sanarwa Dr Omar din kaf rayuwarsa Baya samun baccin Daya kamata musamman a wannan lokacin shiyasa aka rubuta hadda maganin bacci.
Washe gari ma haka ya sake wuni daga cin abinci sai sallah Se bacci,
Daga Ahmed Se Aron ne kadai suke Dan shigowa Dan su Dan debe masa kewa Amma Sam Babu walwala ko farin ciki a tattareda shi.
Mr Jaden baya zama kwata kwata sbd komawa da zaiyi qasarsa Poland Kuma duk yanda yaso tafiya da Omar abin bazai yiyuba a yanzu Dan haka dole zai barsa yaje ya dawo kafin can anyiwa Omar din komai da komai na id cards da sauransu.
Kafin tafiyar Mr Jaden cikin kwana biyu yayi kokarin ganin Omar yafara sakewa sosai Dan yanason inganta rayuwarsa fiyeda yanda ake tinani,
Yanason mayarda rayuwar Omar abar alfahari ga Yan uwansa Da Kuma duk Wanda zaiyi muamala dashi,
Yanason Omar ya samu ingantacciyar rayuwar da har abada bazai taba tinani ko shaawan komawa Ashalawa Koda kuwa ziyara ne bare Dan wani abin daban Dan haka Babu Bata lokaci ya nema lawyernsa na Nan Nigeria me zaman kansa qwararre Akai rubuce rubuce akan zallan tsananin dukiyar Omar wadda kusan yawanta takusa ta dukiyar Mr Jaden din Dan haka a rubuce Mr Jaden da Omar abokanan kasuwanci ne da dukiyarsu ta Hadu tareda adadin ta kowa.
Omar ya amince da Mr Jaden dari Nisa dari sbd kasim ya yarda dashi sosai da sosai kafin ya rasu Dan haka Shima ya miqa dukkanin yardarsa ga Mr Jaden batareda Jin komaiba aka basa takardu duka ya Saka thumbprint nasa aka sealing.
Kafin tafiyar Mr Jaden duk wata sutura tin daga kan underwears da singlet da qananun kaya da manya har turaruka da mayukan da Omar zaiyi amfani dasu da takarman da zai Saka da duk wani abin buqata na rayuwa Saida aka siyosu tsadaddu masu kyau da tsari aka zuba a dakinsa Wanda yake sama babba da toilet dinsa.
Abu na farko daya bari shine zasu fara da basa ilimin Daya kamata Dan haka babban Dan amanansa Ahmed da Aron sune yabarwa komai a hannunsa Dan haka bayan tafiyarsa Id cards aka fara yi masa da passport da banki da komai sai da Akai masa kafin aka tanada malamai biyu masu kyau aka daukar masa Dan karatun da aka fara Babu kama hannun yaro.
Tin tinanin Yan uwansa na dauke masa hankali Yana rabuwa gida biyu har su Ahmed suka Bude masa wuta sosai akan karatun Wanda yakejin kaman bazai iya ba sbd Bai fara ba tin Yana kankani harya zo yafara Maida hankali sosai da sosai Baji ba Gani Dan kuwa Aron Sam Baya masa da sauki akan karatun Dan Mr Jaden ya Basu tabbacin akan karatun karsu masa da sauki ko kadan sosai yake buqatan Omar ya San kansa ya tsayu da kansa.
A bangaren Addininsa ma sosai Ahmed ke taimaka masa Dan haka ya sake zaucewa akan karatun ba wasa ko kadan.
Ahankali ahankali ya fara Bude kansa sosai komai na shiya yanda ya kamata Dan kuwa tamkar hannun sojojin koyan aikin soja aka miqasa a hannunsu Aron Babu wasa ko kadan akan lamarin nasa.
Babu ranar da Baya kewansu mamman da lameenu dasu yake kwana yake tashi a ransa sedai Babu yanda zaiyi tinda baimasan ta yanda zai ji daga garesu ba bare ganinsu dole sai ranarda Mr Jaden ya dawo shine kadai yasan Wanda zai kira a ashalawa a hadasa dasu a waya suji junansu hakama shi kadai ne Wanda yasan yanda zaiyi yakaisa ashalawa din idanma ganinsu yakeson yi gashi Mr Jaden kullum sukai waya basa tabbacin bazai dawo daukansa ba sai yafara fahimtar karatu ya iya turanci Dan haka ya sake Maida hankali sosai akan karatun.
Bayan kusan watanni masu Dan yawa rayuwarsa ta sauya cikin kankanin lokacinda baiyi tsammani ba shi kansa,
Ya sauya sosai ya samu Kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwa duk da akwai kadaici a tattareda shi sbd daga shi sai su Aron da masu aikin gidan ne suke rayuwa,
Baya muamala da mutane sbd koyaushe Yana gida sai Kuma idan sun fita yawon Shan iska ko siyayya ko kallan ball da sauransu Wanda sosai ake kokarin yin duk abinda zai sakashi Jin walwala ko makamanciyarta.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#DEEP
#JAMAAL JEEY SEELAH
#BLACKMONEY
#LOVE
#CRAZY
#LAHOT
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar
6
*_ASHNA BEAUTY SKINCARE_*
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*********
Babban abinda yafara sauyawa sosai a rayuwar Omar shine harshen yare,
Daga Aron har Ahmed dayake musulmi basa Jin Hausa Daman tin farko da dubaru suke magana dashi Dan haka da karfi da yaji yaren turanci ya fara kama bakinsa Dan kuwa ko Ahmed dayakewa kallan nasa ba bahaushe bane yaren igala ne da aka haifesa a Lagos ya tashi a Lagos Dan haka tini Omar ya sake ya fada yaren turanci Shima Yana cabawa.
Sabo da shakuwa dole ya shiga tsakaninsu duk da Yana girmamasu a matsayin wainda suka girmesa su Kuma suna kulawa dashi kaman jininsu Dan kuwa Babu abinda bazasu iyawa Mr Jaden ba ko Yana kasar ko bayanan Dan shine gata da rufin asirinsu da iyalansu.
Mutum ne shi Daya inganta rayuwarsu sosai yanada alheri baida rowa Sam shiyasa suka zama Yan amanansa Dan ya dade a Nigeria shekaru sosai anan yake huldodinsa da yawansu.
******Lokaci yaja Omar tini ya kwana biyu da shiga makarantar da ake kira yaqi da jahilci wadda kusan acan kansa ya qarasa budewa yanzu ba laifi Yana iya abubuwa wa kansa da da sama wainda su Ahmed suka koyar dashi da Kuma iliminsa Daya fara basa,
Shine yake zuwa da kansa yaje ya dawo da mota batareda ankaisa ba hakama Kuma Yana zuwa banki ya cire kudi da kansa batareda wani ya raka sa ba hakama siyayyar abubuwan buqatansa,
A rayuwarsa yanzu abu biyune ya rasa masu damun zuciyarsa kowanne dare shine rashinsu mamman da lameenu a tareda shi sai Kuma rashin Mr Jaden da kusan zuwansa biyu Yana komawa batareda shi ba Amma yanzu Kam da komai nasa na tafiya ya kammala haka yayi bankwana dasu Aron ya tafi yanajin kaman ya rabu da Dan uwansa na jini
Amma Ahmed dashi suka tafi sbd shi har lokacin baiyi aure ba Bai da iyali sabanin Aron yanada family Dan haka shi aka barsa da kulawa da gidan suka koma Poland kwata kwata.
Da farko yaso ganawa dasu mamman kafin tafiyarsu Amma ba lokaci Dan haka dole Mr Jaden yayi masa alkawarin zaa kawo su Suma Nan Lagos su samu Dan ilimin shigowa mutane kafin akawosu Poland inda yake su hade suyi karatu kamansa.