AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Hannu ya miqa mata Yana murmushi ya nuna mata gefensa alaman ta zauna Yana cewa
“Congratulations Lady AM…..
Hannunsa ta kama tana katsesa da cewa
“Dad ban yadda ba bayan baka Nan”
Zaunawa tayi gefensa tana dan narkewa da cigaba da cewa
“Babbah ma Bai je bafa”
Murmushi yayi Yana cewa
“Ayiwa Dad da babbah afuwa to,Amma next time zamu zama a gaba gaba ga duk abinda yazo na budurwan Babbah.”
Dadin kalman taji ta kallesa tana yar dariya tana cewa
“Dad ka it’s fadan sunan kaima kenan.”
Murmushi yayi Yana kallan wayansa da ake kira,
Bai daga Kiran ba suka shiga zancen business sai ga Uncle Ahmed ya shiga tareda Yaya hafiz daga geamin suke Nan suka zauna ta gaida Uncle Ahmed din tana masa shagwaban Shima Baije graduation nata ba.
Shima hakurin ya bayar tareda kyautar 10000 dollars as nasa gift din.
Godiya tai masa tana dariya ta Kalli hafiz tana cewa
“Me ma ka bani Kai as gift??
Dariya yayi Yana cewa
“Ohh ni kikewa gatse??
“Eh mana, Dad barazana ma ya ringa mun wai aure zaimun Muna komawa Nigeria shine gift Dina imagine”
Dariya dad din yayi Yana cewa
“Eh Kuma ai gift din aure Kam ai Mai girma ne,bare Kila yanada wanda zai bawa ke din kawai a Nigeria,
Ba haka akeyi acan dinba??
“Haka akeyi Dad kawai auren sadaka”
Cewan hafiz Yana kallanta da dariya a fuskanta.
Uncle Ahmed cewa yayi
“Ai daughter na ta wuce auren hadi ma bare na sadaka,
Yaya ma ake auren sadakan ne wai??
Ni Banma sani ba wlh”
Dariya sukai dukkaninsu Dad Omar na Tina aurensa da Aminatunsa mahaifiyar AM din.
Saida suka gama nishadinsu kafin suka nufi table da aka gama gyarawa tsaf da varieties na lafiyayyun abinci da teas kala daban daban Suma.
Zaunawa sukai Breakfast din sunayi a natse kowa na cin nasa abinda yakeda raayi Cikin nutsuwa da wayewa.
Bayan gamawansu sun jima Suna tattaunawa kafin kowa ya tashi.
AM shiryawa ta sake Yi ta fito Cikin wasu qananun kayan marasa nauyi ta fito suka fita tareda Dad dinta zuwa Wani gurin su kadai.
Basu dawo ba sai dare Dan haka wanka kawai tayi tayi Shirin kwanciya t kwanta.
Kwanansu biyu Suna hutawa kafin ranar signing din tazo sauran shareholders din ma Dake wasu qasashen sun taho ayau da gobe zaayi an kammala kowa ya koma kasarsa.
10 suka isa Building din Roches Publishers/Ltd
Lafiyayyun motaci ne biyu suka iso dasu gurin take securities suka qaraso Dan Bude musu mota,
Jden din da kansa aka fara budewa kafin Lady AM din tukuna dayar motar uncle Ahmed ne da hafiz da Shima ake masa kallan ‘dan jden dinne.
Hotunansu aka aringa dauka Yana jarida har suka shige tana gefen Dad dinta sanyeda Off-white dress na Amhash sai glass na Versace dayake fuskanta da wasu shegun wedges na tomford tayi Wani irin kyau ta fito Lady AM dinta sak hakama handbag din hannunta kudinta kadai zai iya siyawa Wani mota hannunta daya Yana riqe Dana Dad dinta hafiz da Ahmed Suna dayan gefen nasa.
A yau Omar jden seelah officially ya sanarwa duniya yarsa ‘daya tak dayake da ita shine ya Haifa abarsa da bakinsa ya fada ya Kuma bayyanar da ita tareda nunawa duniya Dan haka take aka fara daukan hotunanta ana watsawa a labarai da sauran media.
Hakan da yayi ya sake daga matsayi da Sunanta AM jden din Kuma take hankalin wasu da Dama ya tashi sbd dukiyarsa da sukeci Kuma suke jira sunsan tazo karshe.
A Nigeria ma zancen ya girgixa mutane da Dama sun shiga fargaba,
Alh Mam seelah kuwa a lokacinda yake kallan conference din a Cikin labarai da aka Saka Wani lafiyayyan murmushi ya sake Yana ajiye remote din hannunta gefen Mum atee Dake ta faman salati da shock na ganin Ameeenatou din a matsayin Lady AM jdens.
Mam kuwa wannan sanarwan Kai tsaye shine yasan sakon menene Omar din ya isar na bayyanawa duniya ‘yarsa daya zabi raba kansa da ita tsawon shekaru Dan bata kariya daga garesu Amma ayau shine da kansa ya kamo hannunta ya bayyanawa duniya ita,
Wannan Sako ne ya isar musu da Shirin fuskantar duk wanda yake jiransa Kuma sakon Kam ya isar Dan kuwa gashinan yanzu Suna ganinta Amma basuma San me zasuyi dinba sedai Kuma Omar abinda Bai saniba shine ‘yar tasa CE Kuma bayyanawa duniya ita shi a gurinsa shine Abu mafi farin ciki a garesa yanzu sbd yanda duniya yanzu tasan ita Lady AM jden din asalin ‘yar jden dince Kuma magajiyarsa kwaya daya tal to duniya ma zata San sirikar Mam seelah ce qwalli daya tal,
Matar zafaffen ‘dansa Jamaal seelah wanda Shima ayanzu duniya take takawa dashi a amtsayin seelah din dayafi kowannensu kudin kansa yanzu da Kuma kuruciya hakama babu wanda yasan asalin qasar dayake zaune dindindin a yanzu sbd baama ganinsa sedai labarinsa.
Zai nunawa Omar komene fuskantar junan da zasuyi to AM sirikarsa ce sai Kuma ta dawo hannunsa hakama aurenta dayake hannunsu mutuwa CE kadai me rabasa Amma mutum dai ko waye yace zai raba auren to kwanakinsa ne suke qarewa.
Wani murmushin me sanyi ya sake sakewa sbd a shekarun Nan Ya Gina kansa ne a boye tareda kwantarwa da ‘dansa kansa Yana bibiyarsa harya samu tausayin uba da ‘da a tsakaninsa da Jamaal ya dawo Yana magana da ‘dansa a duk lokacinda Jamaal din ya bada daman a samesa a waya din sbd samunsa Abu ne me wuya,
Jamaal Yana tareda shi Bai yafesa ba hakama ayau Allah ya bayyanar masa da sirikarsa mukullin arziki da cikan burinsa na Tim kafin asan zaa haifesu Dan haka kauna ta musamman yakejin yanaiwa Ameeenatou da kansa.
Omar ya hutar dashi ta bangarori da Dama Dan haka Babu abinda zai masa sai godiya da wannan conference din daya hada Dan isar da sakonsa.
Wayarsa ya dauka ahankali ya Saka Kiran Jamaal batareda ya tankawa Mum atee Dake gefensa tana fama da shock Dan kuwa itama batajin zata taba barin auren ‘yar jden ya fita hannunsu duk da Jamaal Bai taba bata daman shiga rayuwarsaba,
Kwata kwata ko ganin idanuwa batai masa Gani nawa ba Dan bayan muamalantar mahaifinsa ma bare ita Amma dai Kuma dukiya me sunan dukiyarsa Kam tana cinta iya ci sbd ya sakarwa Dad dinsa kudin fitar hankali sbd janyesa daga qazantacciyar dukiyarsu kafin rayuwarsa ta daidaita Dan har yanzu rayuwarsa a empty take sbd Babu abinda ya barwa zuciyarsa sani kadai.
Shi maganar aure duk iya yanda mum dinsa taso yayi auren babu ma mace a gabansa Dan haka ita kanta a yanzu ta bar maganar auren nasa sbd Yama wuce matsayin da zata zabar masa mace Dan basa gabansa kwata kwata ko a kalla.
Dad dinsa kuwa baima taba tinanin kawo maganar Wani auren a kansa ba sbd shi kansa a shirye yake zaman juran dawowan Ameeenatou hannunsu Dan haka baiga lokacin batawa ba gurin auro wata macen ga Jamaal Dan kaman yanda ya sani Jamaal bazai taba auren wata macen ba idan ba Ameeenatou din ya Gani ba Dan haka Babu maganar ma mace bare Wani auren Shima a kansa.
*****Daddy lameenu dayake zaune Shima a palonsa Yana waya da Wani likita Dake Angola akan ciwon matarsa datake zaune a wheelchair shekara biyu kenan tana fama da paralyze sanadin bacewan Aliyah shekaru uku yanzu Babu labarin komai duk iya bincike da batar da dukiyar da sukeyi ankasa samun komai dangane da inda take Dan haka daga shi har mum Sarah din Babu me isashiyar lafiya sbd ciwon zuciya dayake cinsu a tsaye har yakai ita ta yanke jiki ta koma hakan
Shi kuwa abin ya zamar masa masifa da tashin hankali sbd tsananin tsoron gurin binciken Neman Aliyah Mam ya Gano Wani Abu gameda abinda suke boye masa sbd Neman Aliyah kacokam dinsa a hannun Mam yake sbd shine yake komai da tsari ya karbi ragamar komai Dan haka lameenu jira kawai yakeyi a Nemo masa Aliyah Dan haka ya samu Damar barwa BB komai na ci gaba da illata rayuwar Ameeenatou Dake asibitin mahaukata a wannan shekarun..