AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Yaya Hafiz dina Dan Allah kayi hakuri wlh tallahi inshallah bazan sake jiqa Maka takarminba bama zan sake sakawa ba nayima Maka alkawari na shiryu”

Dago idanuwansa da sauran fushi ke cikinsu yayi ya kalleta Yana Hana kansa hakura Dan yasan fada tayi indai itace ko fita bazaiyiba saita sake Bata masa Rai sunyi fada.

Hawayen idanuwanta take kokarin saukarwa tana sake basa hakuri take yaji zuciyarsa ta fara saukowa daga fushin sbd duk masifan rashin jinta Neman maganarta basa iya fushi da ita Dan kaman yanda su dadah suka gama sangarta haka Suma Yannan nata sun gama sangartata da kauna me tsananin gaske da dukkanin gidan ake mata Sam Babu me qaunar ganin hawayenta shiyasa idan taso Abu Hawaye take musu saisu kasa riqe fushinsu su watsar.

Harararta yayi Yana daga takarman Dake hannun nasa ya kalla kafin ya dawo da kallansa kanta Yana daidaita murya daga fushin da yayi yace

“Shikenan na hakura Amma kika sake tabamun kaya saina fasa Miki Baki kinsanni sarai.”

Gyada Kai tayi da sauri tana cewa

“Eh bazan sake ba,komai bazan Saka tabawa naka ba saina tambayeka,Amma Dan Allah Yaya Hafiz da gaske baturen Nan zai sake zuwa site din aikinku?

Tsoki Hafiz din yayi Yana fincike hannunsa daga nata Yana wucewa cikin haushin ma Bata lokacinda da yayi Dan ya dauka tuban gaske tayi Ashe sbd me gidansu da shi Yama kasa iya riqe sunansa take magana Wanda Rabon da su gansa anjima sosai Dan tini aikin site din ya tsaya cak Anma Dena project din kwata kwata dukansu an sallamesu Se yanzu ne zaa sake tayarda aikin an mayar dasu aikin masu rabo kuwa har Lagos zaa tafi dasu.

Gefen dakinsu ya nufa ya shanya takarmansa kafin ya shige dakinsu Yana kokarin qarasa shirinsa ya fita abinda yake gabansa.

Ita kuwa juyar da idanuwanta tayi tana juyawa ta koma dakin dadah tana cewa

“Babbah nidai kace Yaya Hafiz koba yau ba idan baka Nan karya Dakar Maka ni,
Nida nakeson auren bature tayaya zai aureni idan akaimun Tambo.”

Batareda babban ya kalletaba Yana fitowa daga dakin yace

“Bama ze fara dukanki ba bare tambon ai yasani sarai,
Yadai samu sa’ar dokarmun ke a Baya yanzu kuwa Babu yanda zaayi Ina kallan tsaleliyar budurwa a gabana Ina jiran ganin aurenta ya dakarmun ita, ko kudi aka basa bazai dakeki ba indai Ina Nan.”

Dadi zancen yayi mata ta juyo tana kallan Dadah data karasa Saka mata zip tana cewa

“Dadah ko Babbah Baya Nan Dan Allah ki ringa tinawa Yaya Hafiz zancen Nan Koda nayi masa lefi”

Miqewa dadah tayi tana nufar gaban tsohuwar madubinta ta dauko turaren Ameenatun dasu Hafiz ke Siya mata Baya taba yankewa tareda duk wani abu da sabuwar budurwa ke buqata kwata kwata basa wasa da lalurarta ko buqatunta sbd tini suka manta da ba uwarsu Daya ubansu Daya da itaba Dan kaunar da suke mata kusan duk Neman da sukeyi Dan inganta rayuwarta ne duk da ta renasu sosai har gwara Yaya Abdul tana girmamasa sosai akan Hafiz data Rena sbd biye mata dayake yi kusan Babu ranar da basa fada tin kafin suyi wanna girman,
Da suka girma kuwa tini suka koma yanzu shiri anjima fada yace Saiya karyata ko balla mata kafafu.

Fesa mata turaren me sanyin kamshi daidai dadah tayi tana dauko mata hijab gogagge kalan kayanta ta miqa mata tana cewa

“Ki Dena shiga sabgarsa tinda Kinga dai bakyason tabo ko Daya a jikinki,
Idan Baki Dena ba ko a hanyar rakaki makaranta Saiya miki dukan ba sanin kowa bare me cetan ki.”

Bata fuska tayi tana qarasa Saka hijabin tace

“Ai Babbah yace ko a waje karya taba masa ni”

Takarmanta dadah ta fitar mata kofar daki tana cewa

“Zo ki tafi kinyi latti sosai”

Jin haka ya Sakata fasa Saka takarman tana dawowa Baya ta dauko wayar Dadah din ta danna Taga karfe Hudu saura mintina kadan ita da ake fara tarewan latti karfe biyu da rabi.

Dadah na ganin ta ajiye wayar tana narke fuska tafara daga murya tana Kiran Hafiz.

“Hafiz fito ka Kaita makarantar ka roqi malam Dan Allah ayi mata hakuri bazata sake latti ba uzuri ne yasakata lattin.”

Hafiz Dake daki Yana Saka kayansa Yana jinsu yayi musu shiru Dan babu hakurin da zaije bawa malam Dan kullum haka takeyi duk ya lalace ya qare a hanyar makarantarta bawa malamai hakuri da uzurin karya Baya hanyar bokonta Baya hanyar islamiya kaman mara aikin yi.

Sake qwala kiransa Dadah tayi yanaji yayi kaman Baya gidan Dan yakai malaman suna ganinsa suke sauya fuska.

Babbah Daya fito bandaki sarai ya hango Hafiz din a daki yace

“Yana jinki Kaita ne bazaiyiba idanma kin takurasa haka zaibi hanya Yana mangaremun yar budurwa Dan haka muje na Kaita da kaina ai mun Saba ba akanta farau latti ba hakama ai uzuri ne,wuce maza muje.

Saka takarmanta tayi ta fito dadah na miqo mata jakarta tana cewa “A dawo lafiya yar budurwan Babbah”

Hafiz Dake kallansu ta window da harara yabi Bayan Ameenatoun Yana cewa

“Duk anbi an sangarta yarinya Bata ganin girman mutane Dan an renasa ace kullum Saiya Rakata makaranta saikace qaramar yarinya,
Duk an ishemu da wata yar budurwan Babbah da Dadah mtseww”

Dadah Dake jinsa cewa tayi

“Idan ka gama yi mana fada ubanmu saika fito ka wuce inda zaka tafi ka dawo da wuri ka biya mata ku dawo tare.”

Yana Jin Hakan ya fito baice komaiba ya fice Yana gyara zaman rigar shaddarsa a jikinsa dan qamshin turarensa me arha na tashi Dan gurin fira zasu gurin budurwansa.

Yana fita Dadah ta bisa da kallan mamaki tana girgiza Kai Dan tasa wannan Doron dayake dagawa Yana qamewa fira zasu.

Yana fita Abdul ya shigo gidan sanye da kayansa na aikin securityn Bankin first bank kadai dayake ta gurarensu.

Gaida Dadah yayi Yana cewa

“Budurwan gidan ta fita ne naji gidan tsit.”

“Taje makaranta Babbah ya tafi Rakata jiya da shekaran jiya bataje ba tana fama da yatsarta datai tintibe Se yau ya Sena mata ciwo ta shirya ta tafi”

Yana Jin Hakan yashigewansa Yana cewa

“Wannan budurwan daya bita da Kun cire mata shi Dan Babu Wanda zaiso ta ahaka Kun gama lalata kayarku”

Banza tayi masa ya shige ya tube ya fito sanyeda da wando dogo ba Riga da kwandon kayan wankansa ya wuce Bandaki bayan ya debi ruwa a bokita Dan Shima wankan zeyi ya fice fira zashi Shima yau din Dan ya kwana biyu Bai ziyarci budurwansa ba.

A hanyar makaranta Saida Babbah ya Siya mata agwaluma cikin bakar leda ta Karba ta Saka jaka suka Isa tana Dan narkewa babban shikuma Yana ganin Hakan ya Bada himmar yiwa malam bayanin rauni taji jinya sukai sosai.

Malam iliya ya Saba da wannan karfin halin na Babbah Dan haka baiyi musu ba yace Allah ya tsare gaba ta wuce aji kawai.

Wucewa tayi Babbah na mata adduar adawo lfy da adduar Allah ya Bata ilimi fiyeda kowa makarantar.

“Amin” tace masa tana wucewa gaba kadan kadan tasake cewa

“Babbah kasa Yaya Hafiz yazo daukan fa”

“Tin kafin a tashi zan korosa”

Dariyar mugunta tayi tana wucewa aji da sauri.

Tana shigowa ajin kawarta ta musamman ta tarbota cikin murna daga Nan sukai gurin zamansu.

Dayake sune manyan makarantar da zasuyi sauka a kwanakin kusa a tacesu shiyasa su kadai ne ajinsu daban Amma sauran makarantar kusan aji Daya suke sedai kowa da karatunsa da ake masa Yana bayarwa ranakun laraba da litinin.

Tin kafin lokacin tashi ya qarasa yi Babbah ya ringa Kiran Hafiz a wayarsa me malatsai Yana cewa yaje ya taho da Ameenatou din.

Hafiz idan akwai abinda yafi zafi da takaici Yana cikinsa Dan kuwa a gaban budurwansa yake babbah keta masa wannan Kiran Dan haka dole yayi sallama da ita ya nufi hanyar makarantar Yana tafe Yana masifa da bacin Rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected