AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
A yanda takardar take hotonta kawai ya dauka tareda turawa Sir Ahmed din ta Whatsapp sbd yasan ko ya kira ba dauka zaiyiba Dan haka ya tura Yana fatan gwajin sa’ar da yayi ya zamar masa alkhairi.
Ameenatou na shiga satin haihuwanta Hafiz yaje Nasarawa ya qarasa siyar da Rabin gidansu ya dawo da kudin suka Siya mashin din da zai fara sana’ar Dan Acaba Sbd dole Saida Hakan tinda haihuwa zaa musu,
Rago suka siyo aka daure na radin sunan abinda zaa Haifa,
Sauran kudin Kuma abinci suka Siya da Yan kayan buqatan Ameenatou wadda zuwa lokacin gadan gadan sauki yake zuwan mata sbd halin quncin dasuke ciki tini ya Dade da tafiya da walwalanta.
Kudin sun qare Dan haka Dan sauran abinda ya rage suke lallabawa Dan kuwa kudin da suka tanada na zuwa haihuwa tini suka shige a lalura Amma suna da tsammani tinda Acaba Hafiz din yakeyi Wanda shi Kuma a nasa bangaren Bai fara ganin haske ko Daya ba a Harkan acaban.
Ana gobe EDD din Ameenatou zai cika kaman a mafarki cikin dare Dadah taji Wani irin sautin kuka me karfin gaske daya Saka dukkaninsu fitowa rikice suna nufo dakinta Babbah na cewa haihuwa ce.
Hafiz Jin yayi gabansa yayi mummunan faduwa sbd Babu kudin komai a jikinsa hakama tausayin Ameenatoun yake ji kaman zai fasa kuka.
Babbah ne a gaba suka shiga dakin gabaki dayansu suna kunna hasken wutar dakin da Babu komai acikinsa bayan katifa da jakar kayanta ta sakawa.
Ganinta zaune tsakiyar katifa rungume da cikin jikinta kanta aqasa tana Wani irin kuka sosai Mai tsananin tsima zuciya Wanda Bata taba yinsaba a rayuwarta tinda aka haife takeyi dukkanin jikinta na Wani irin rawa.
Tsayawa Dadah tayi cak daga inda take sbd take ta fahimci meyake faruwa itama take Hawaye suka balle mata jikinta na tsananin sanyi tana kasa qarasawa.
Babbah da Hafiz ne sukai kanta da sauri sedai hannu Dadah ta miqa ta riqe hannuwansu tareda girgiza musu Kai tana cewa
“Ku barta tayi kukan ta dawo daidai ne Inshallah”
Da sauri Babbah ya juyo ya Kalli Ameenatoun idanuwansa na cikowa da wasu irin hawayen farin ciki da baqin cikin lokaci Daya sbd ta dawo daidai ta samu kanta da wannan mummunan kaddarar ta haihuwa irin wannan da ko ita bazata Tina waye yayi mata wannan zalincinba.
Hafiz kuwa kasa riqe nasa kukan yayi yafara Hawaye kukansa na cin karfinsa ya fasa ahankali Yana qarasawa gurinta ya ambaci sunanta cikin radadin zuciya murya na karyewa.
Ambatar sunanta da yayi ya Sakata cusa kanta cikin kafafunta tana sake fashewa da kukan dayafi na farkon tsima zuciya.
Rawa muryan babbah keyi Yana riqe kukansa yace
“Ameenatou sai hakuri,
Haka Allah yaso,
Kaddararmu ce wannan,mudai fata da burinmu Daman kece Kuma tinda munsamu kinzo hannunmu cikin Aminci da yardarsa ai mun gode masa wannan Rabo Kuma shima dai mum Barwa Allah komai mun karba allah zai Saka mana ga duk Wanda ya Miki Hakan, inshallah zamu samu kyakkyawan sakamako daga ubangiji,Abdul ya tafi sedai addua shima,Haroon ma sedai adduar……
Kasa riqe kukansa yayi ya fasa Wani kuka mara sauti me tsananin ciwo da radadi Yana sauke Kai sbd dukkaninsu baqar Rana ce wanna garesu ta haihuwan Nan,
Da ace aure ne akan Ameenatou da haihuwar Nan da sunfi kowa farin ciki da murna Amma shikenan yanzu basuda wani farin ciki bayan fatan saukanta lafiya ta tashi lafiya itada abinda zata haifar musu.
Hafiz ma kuka yakeyi sosai kaman qaramin yaro sbd dawowanta daidai sai yanzu ne zasu koka rashin Dan uwansu da sukai Abdul.
Dadah ma kukan takeyi an rasa me magana a cikinsu Daren tsit hakama gidan tsit sannan dakin ma tsit sheshekan kukansu ne ke tashi kowannensu zuciyarsa kaman zata mutu sbd radadi da Kuna tareda damuwanda basusan Yaya zasuyi ba Kokuma ta ina zasu fuskanci rayuwa yanzu.
Kukanta yafi na kowannensu tsananin radadi da azabar zuciya sbd batasan ma Me ake nufi da duka bayanan da akeyiba abinda ta sani kawai shine Haroon ya rasu hakama Yaya Abdul to Amma a Ina ta samo cikin jikinta?
Aure Akai mata da wani batareda tana cikin hankalin kanta ba………
Fashewan ruwan nakuda ne masu karfi ya Saka dukkaninsu dago jajayen idanuwansu suna kallan ruwan dayake gangarowa daga karkashinta.
Dadah na ganin Hakan tayo kanta sedai Kuma take azabbiyar ciwon mara ta tinkarota gadan gadan cikin tsananin ciwo da azaba ta dago jajayen idanuwanta ta Kalli dadah Dake tambayarta nakuda ta taso ne?.
Fitowa su babbah sukai daga dakin sbd sosai nakudar ta taso mata me azabar radadi.
Rikicewa Dadah ke Neman yi Amma sbd dare ne dole ta nutsu tafara taimaka mata tinda Babu Daman zuwa asibiti yanzu hakama Babu Daman Kiran Mai Taimkawan.
Cikin qanqanin lokaci Ameenatou tafara ficewa hayyacinta sbd azaba da wahala,
Hafiz kuwa sai duba wayarsa yakeyi Yan fatan gari ya waye da wuri ya fita Neman kudi kafin a haihun Babu komai na abinci Kokuma abin Sha a gidan bare kudin siyan magani.
Babbah kuwa gabaki Daya fita hayyacinsa yake Neman yi da ciwon kirji ya taso masa sosai sbd ranar yau din tana dawo masa da tinanin komai na ranar da Aminatunsa take nakudar haihuwan Ameenatoun Kuma a ranar ne ya rasata rashi na har abada.
Nakudarta tayi nauyi sosai Dan haka tafara gabalaita karfinta yafara karewa daqyar suka samu Safiya tayi Hafiz ya fita jiki na rawa zuciya ba kwari Neman abinda zai samo ya kawo ko asibiti ne sai atafi akaita.
Yana fita Dadah dataga tana Neman rasa ‘yarta fita tayi hayyacinta ga hadari me tsanani ya Hadu ana kokarin fara yayyafi ta fita ta Nemo Hafsatu me karban haihuwa Dake maqota dasu.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
98
*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
************
DAWOWA LABARI
Ameenatou tsananin azaba ya Sakata somewa tana kwance kaman Babu Rai a jikinta Babbah ya iso kofar gidan da taxi din Daya samo daidai lokacin Shi Kuma Hafiz Yana kokarin tsayawa wani passenger Daya samu zai hau mashin dinsa wayarsa Dake aljihunsa tayi ringing Ya Ciro Yana Dan kare wayar da hannunsa sbd ruwan sama Baya ganin me Kiran sosai.
Bai ga suna ko numbern data kira dinba sbd ruwa Dan haka daukan Kiran kawai yayi tareda dorawa a kunne kafin yayi magana Kai tsaye yaji muryan da ko bacci ya tashi zai ganeta ta ambaci sunanta cikin Wani irin nutsuwa da Kamala tareda tsagwaron ilimin Daya ratsashi duk da akwai sauran rashin hayaniyar ciwon da yayi.
Sakin mashin din Hafiz yayi sauran kadan su kife yayi saurin riqe kan mashin din Yana kashewa muryansa na rawa ya amsa da cewa