AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Barin jikin dadah Fatmah tayi ta nufi hafiz ta rige hannuwansa duka biyu tana sake fashe masa da Kuka tana cewa ya fadawa babbah ba soyayya sukeba.

Daidai Nan babban ya sake fitowa ya kallesu yaga yanda ta cukuikuye Hafiz din Shikuma Yana kokarin kwantar mata da hankali take ya dauke Kai Yana sake cewa “dakyau” ya ficewansa.

Hafiz sakin Fatmah din yayi ya fice Yabi bayan babban Dan suyi magana.

Mum Nur ce itama tazo tana shiga farin Cikin zancen itama Dan tsaf hakan yayi mata Dan haka rarrashinsu da kwantar musu da hankali itama tafara yi tana Jin duka ta Dena Jin laifinsu saima kaunarsu.

Haka aka wuni a gidan ana zuba bori karshe dai Koda zancen ya isa kunnen su Dad Omar take ya amince ba musu uncle Ahmed ma kusan farin Cikin da Didi tayi shi yayi Yana sakawa babbah albarka da qarin Nisan kwana.

Dr Aleena ma hakan ya mata Dadi Dan haka a bakinta su Jamaal suka samu zancen.

Kallan siddeeq Jamaal yayi zaiyi magana siddeeq din ya katsesa Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da cewa

“Am 100 percent happy and okay with it”

Rungumesa Jamaal yayi Yana cewa

“Congratulations to us tohm,and luv you my personal person, Siddeeq and Jeey for life bro”

“Thank you hero”
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
148
Kwana biyu shiru su Jamaal sukai a nasu bangaren sbd nasu Shirin Wanda ya Saka Mum Aleena dawowa dole.

Dad Omar ma Suna dawowa ba Bata lokaci Aka buga katin dauren aure bayan an gama zaman Neman auren an amince da komai da kowa.

Lafiyayyan gida a maqale da mansion din aka fara ginawa Hafiz Wanda dole sukai shiru suka zubawa sarautar Allah Ido akan auren da ko zasu mutu sunsan Babu fashinsa.

Fatmah ma data Hana kanta zaman lafiya ganin Babu abinda zai Hana auren dole ta dangana.

Ashley hadda kwanciya rashin lafiya tayi kwana biyun Amma haka ta gama ciwon ta miqe Babu alamar fasa komai itama dole ta dangana gashi daga ranar Bata sake daga wayar siddeeq dinba sai dai yayi text ta kalla ta share jiki a sanyaye.

Su Mum Nur Wani gyaran gaske aka fara yiwa amaren harma da Ameenatou da Mum Nur keson ta tare itama Dan tasan Jamaal bazai taba barinta ba kaman yanda Taga shirunsa tasan komai zai iya yiyuwa.

Dole bikin daman an sakasa wata daya me zuwa ne sbd Shirin komai Cikin nutsuwa.

Gabaki daya familyn mata Paris suka tafi sukai shirye shiryensu acan kafin daga Nan suka wuce Dubai acan Akai gyaran amaren da Babu wacce Bata sauyaba hatta mum Nur da Didi gyaran sukai take suka koma kaman wasu Yan mata amaren sbd Suna sunada kyan jiki.

Ameenatou kuwa kasancewan akwai Ciki a jikinta sai ta fisu yin haske sosai sai Ashley wadda itama take fara sosai Fatmah kuwa daman chocolate beauty ce,skin dinta brown ne me shegen kyau da lafiya ga Hutu dayake Ciki tin haihuwa haryanzu.

Duk wata siyayyar da zasu sunyi,

Hafiz da kansa ya bada mahaukatan kudin da zaa hadowa Fatmah din lefen alfarma Wanda yaji sarkokin gwal bama guda daya ba da tsadaddun komai.

Satinsu uku suka dawo Nigeria Dan haka Suna dawowa aka fara bikini da zai hada duka wasu shegun qasa da manyan mutane Tako Ina.

Kwanansu hudu da dawo aka kawo lefen Ashley Dana Ameenatou Wanda ya girgixa mutane aka ringa yawo da bikini kawo lefen kawai da Akai Wanda shi kansa bikin kudin da aka kashe masa zai Gina gida da furnitures din cikinsa.

Babu abinda ya banbanta lafiyayyan lefen Jamaal Dana siddeeq Wanda Mum ce ta dauki manyan Nigerian designers na Hausa da sukasan al’adun Hausan da maman fadeela da Ayesha ta fita dasu waje sukaiwa dukiya zubarwan da kusa su kansu masu siyayyar duk budewan idonsu da kudin da suke cikinsu Basu taba hado kayan lefen irin wannan ba.

Sarkokin gold Dana diamonds kadai dasuke Ciki Saida aka ringa yawo da hotinansu.

Ta bangaren sauran surutar sakawa kuwa da sauran kayan baa magana.

Acan gidan Jamaal din kuwa Suna barin qasar aka daga gidan aka sake budesa sosai da Wani irin girma aka Gina part biyu iri daya masu girman gaske da walwala Cikin qanqanin lokaci Suma aka kammala gyaran sedai komai dayake gidan uncle Ahmed ne yayi SA sbd komai iri daya aka siyawa su ukun wanda kowannensu har Fatmah gidanta yake dauke da palours guda kusan uku uku da bedrooms da zasu Kai hudu hudu Dan haka luxuries ne kawai ta ko Ina sbd ba qananun kudi aka zubarba aka zuba musu luxuries din.

Dad Omar daya rasa abinda zai musu sbd angama komai motoci ya siyawa kowannensu har Jamaal da Siddeeq din
Angwayen mota iri daya ya Siya musu Rolls-Royce phantom fullsize luxury car sai Matan su uku ya Siya musu Bentley continental gt farare tas.

Babbah da baisan duk wannan hidimar ana yinta ne da yarsa ba sbd ganin ma Cikinta harya Dan fito ana ganinsa ya barshi akan sunayi ne duka Dan shawo kansa ya sauko shiyasa Akai su lefe da sauransu duk da Abu daya ya sani Babu wanda zai dauki yarsa ya bawa Wani idan ba shi yaso hakan ba.

Ba sosai ma Ameenatou ta sake a bikin ba sbd Cikinta dayake a dan bayyane Dan qarami dashi da Kuma boyon da sukewa angwayen Dan ko Ashley taqi bawa siddeeq daman ganinta hakama sisters dinta sunxo bikin sedai haka suka koma kaman Yan kallo sbd ita Kanta Ashley din tayi musu Nisan da sedai kallo da fatan qarin daukaka su da ita Danma tana Basu kudi sosai.

Sunga Siddeeq Shima Wanda suka buqaci ganin mijin yar uwarsu ko yayane kafin su wuce Dan haka Yana ganinsu Shima kudin gaske ya Basu tareda Saka driver ya maidasu har Abeokuta.

Dad Omar ma yayi musu alkhairi hakama babbah ya musu alkhairi Dan haka da farin Ciki suka koma batareda sun tsaya har a gama bikinba sbd basuga irin tasu jamaar ba agurin manyane masu abin duniyar gaske Tako Ina a zagaye da shaanin.

Ranar daurin auren da farin Ciki tareda hidima families din suka tashi musamman dayake haddata maauratan sun dangana sun Dan sake.

Karfe 12 na rana dubban Jamaa suka sheda daurin auren SIDDEEQ ALEEY SEELAH kaman yanda Jamaal ya basa last name dinsa Tin da dadewa Da Amaryansa AYSHATU ADRIAN JDEN(Ashley)
Sai Kuma HAFIZ NUHU JDEN da tasa Amaryar FATMAH OMAR JDEN.

Yanda Akai daurin auren Cikin Taron Manya da aminci aka Kuma watse a farin ciki.

Medias da maroqa tareda Yan jarida Tako Ina Dan haka koina haska angwayen daukosu akeyi Cikin shigar alfarma da kowa yasan kudi ne kawai yake magana ta ko Ina a jikin 2 families din.

JEEY SEELAH kuwa kusan yafi agwayen daukan Idanuwan mutane da cike musu Ido sbd yanda shigar daurin auren tayi masifar Yi masa kyau Yana sanye da sky blue tsadaddiyar soft shadda Mai babbar Riga da hula sai agogon diamond na BottegaV dayake hannunsa qamshinsa ne nutsuwa sai tashi yakeyi.

Siddeeq da Hafiz ma sky blue shaddodin ne a jikinsu sedai nasu design daban da nasa iri daya sunyi Wani irin kyau.

Daga can gida kuwa a ranar amaren zasu tare Dan haka ana gama daurin auren yamma na Yi aka fara Shirin Kai kowacce gidanta.

Ameenatou Kuka sosai tayiwa babbah kafin daqyar ya amince ta fita aje Kai Amaren day ita.

Da farko Sam Sam Bai aminta da fitartaba sedai yaga yanda ta nuna tuba da Kuka sosai ga Kuma Cikin dayake jikinta da bayason Wani ciwon ya sameta Mum Nur da dadah suka Saka Baki ya amince.

Tausayin kansu taji itada Ashley sbd da baa barta ta Rakata ba Jin sukai kaman sun rabu kenan Dan haka ana barinta taji Wani irin sanyi da farin Cikin data dauki lokaci batai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected