AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Suna ganin motar Seelahs suka San Jamaal ne.

Haroon ne yafara fitowa Dan haka suka tinkarosa siddeeq na masa barka da zuwa Saida Jamaal din ya Bude dayar kofar ya fito suka gane ba shine suka tinkara ba Haroon ne Dan haka suka juyo suka dawo bangarensa suna masa barka da zuwa.

Cikin girmamawa ya gaida baba Yana tambayar siddeeq exams dinsa Daya gama a jiya.

Fitowan Dr Aleena ne ya Saka baba da siddeeq kallanta suna tabbatarda itace mahaifiyar su Jamaal din sbd kamannin da suka hada Dan haka cikin mutuntawa da girmamawa sosai suka gaidata suna mata sannu da zuwa cikin turanci.

Amsawa tayi itama a mutunce kafin sukai cikin gida gabaki dayansu.

Umma ma tarban mutunci da girmamawa taiwa mum din da Haroon duk da Shima ya zama kaman na gida yanda Jamaal yakoma Kai tsaye Dan gidan baida shamaki da koina da komai.

Dakin fadila suka nufa tana zaune a jingine da gado an mata kariya da pillows masu taushi idanuwanta a rufe tana Jan wani kasalallen wahalallen numfashin dayake shiga lungs dinta daqyar.

Kallo Daya mum tayi mata ta juyo cikin sanyin jiki ta Kalli Jamaal Wanda yanayinta yake karanta Dan ko a Poland tana cikin manyan likitocin da ake alfahari dasu manya.

Qarasawa tayi har inda fadilan ke zaune ta Bude idanuwanta ahankali da Jin qamshinsa da shi kadai ne yake Ankarar da ita da zuwansa.

Akan mum ta sauke idanuwanta dasukai ciki sosai Bata iya budesu duka sosai sbd rashin karfi sosai.

Durqusawa mum tayi gabanta tana mata sannu cikin tsananin kulawa da nutsuwa kafin ta Kai hannuwanta biyu ta kamo hannun fadilan Daya tana gyara zamanta gefenta cikin sanyi ta tambayeta Yaya jikin.

Cikin nutsuwa da sanyin murya me tsananin taushi ta amsa tareda yi mata sannu da zuwa sbd karfin hali.

Tsit dakin yayi kowannensu na tsaye daga waje daga Jamaal din Se mum ne kadai a dakin tafara dubata tana Jin shakkar abinda tafara tinanin matsalan take.

Kallansa tayi lokacinda ta zare oxygen din hancin fadilan takai hancinta tana shaqa kadan tana Dan rufe idanuwanta Dan shaqarsa cikin relaxing komai nata.

Numfashin fadilan ne yafara sama sama Dan haka ta mayar mata dashi ahankali tareda sake kamo hannunta tana Jin pulse nata.

Cikin abinda Bai gaza mintina arbain na zuwa hamshin ta kusan gama karance matsalan fadilan ta gangan jikinta.

Kallan Jamaal tayi Wanda gaba Daya ya tashi daga likita a lokacin ya koma kaman me jiran sakamako.

Numfashi ta sauke tareda miqewa tsaye ta dawo gefensa ta tsaya a natse tace

“Ina buqatan ganin file nata yanzu a fito dashi daga asibiti a kawomin”

Kallan fadilan yayi tareda kamo hannunta Daya acikin nasa yayi mata sannu kafin ya Kalli mum cikin Dan sassauta murya Yana baro gurin fadilan yace

“Mum asibitin zaa tafi da ita yanzu ai sbd acan ne zatafi samun cikakkiyar time da kulawa da duk abinda ma zamuyi…”

Kallan fadilan itama mum tayi cikin sanyi da tausayi kafin ta dawo da kallanta kansa tace

“Abarta a gida zan dubata anan tareda duk abinda nakeson tantancewa sbd Ina tinanin koma Menene matsalan daga oxygen data shaqa ne yayiwa lungs nata mummunan illa a yanda na karanci numfashinta da kyau da yanda kirjinta yake amsa zuwa lungs din but Ina buqatan sabon oxygen akawo daga wani gurin daban bana asibitinku ba.”

Manyan idanuwansa da suka mum din kallansa tana Jin sanyin jiki ya zuba mata Yana Jin gefen kansa na sarawa sbd tinanin oxygen nata nada matsala shine abinda Bai taba shigowa kansa da bincikensu ba sbd daga asibitinsu ake Bata shi Dan haka ma ne Bai taba tinanin Koda bugun iska wai zaa samu matsala a oxygen din datake shaqa ba,.

Hakan ne ya hanasa Gano asalin matsalan Dena shigarda da numfashi keyi dakyau kenan duk qwarewansa a aikinsa ko me??

Jin yayi kansa na Neman daukan zafi Dan haka mum tayi saurin fahimtar dashi tana tinani ne kawai Amma suna buqatan wani oxygen din kafin su tabbatarda Hakan ne.

Fitowa dukai dukkaninsu shine a gaba mum din na Baya Basu sanar da kowa komai ba Sukai musu sallaman zasu dawo anjima suka fito.

A mota shiru yayi yaja sauraron bayanan Mum datake qara Bude masa komai sbd itace take gabansa sosai a kwarewa da sanin aikinta.

Haroon ma kasa yadda yayi da zaa iya samun matsala a cikin oxygen din Daya fito daga asibitinsu sbd wannan babban laifi ne ake magana Wanda zai Saka a dole license na asibitin gaba Daya a rufeta Kuma hakanma zai iya taba aikin likitocinsu da yawa harma dashi Jamaal din.

Shiru Jamaal yayi Bai iya cewa komai sbd Jin zuciyarsa na tarwatsewa idan har ya tabbata akwai abinda yake cikin oxygen din fadila yayiwa lungs nata mummunan illar da Babu gyara bazai taba yafewa kansa ba akan sakacinsa.

Suna Isa gida Kai tsaye hanyar bangarensa sukai parking ya fito da kansa ya budewa mum din mota ya kama hannunta ta fito
Haroon kuwa kayanta ta fiddo dasu daga bayan motar suka nufi kofar palonsa.

Kai tsaye har bedroom din dayake part dinsa Daya yakaita Haroon ma ya shigo da kayanta yana sake juyawa zancen fadila a ransa tareda tsoron halinda Jamaal zai shiga idan Hakan ta tabbata,
Yana tsananin son Dan uwansa fiyeda komai da kowa a duniyarsa Dan haka bayason damuwa ko bacin Rai Bare tashin hankalinsa Dan haka duk ya rasa sukuni.

Key din motarsa ya dauka ya fice Kai tsaye asibitinsu ya nufa ya buqaci oxygen daban da sunan wani patient din zaa sakawa hakama ya buqaci wani daban da sunan fadilansa kafin ya dauko file nata ya fito asibitin.

Wani asibitin abokinsa ya buqaci wani oxygen din take ya biya ya karba ya dawo gida.

Koda ya dawo mum tayi sallah taci abinci ta huta ba laifi Dan haka ta sake wanka suka fitowa zuwa gurin fadila batareda Haroon ba sbd shine yayita kulawa da mum din tareda Mum Atee da Bata nunawa Dr Aleena din komai na hakama mummy Sarat matar Dad Lameenu ta shigo sbd Dr Aleena mutuniyata ce sosai
Tarba me kyau tayi mata tareda asmy da hawwah yayanta.

Kai tsaye daga gida office dinsa suka koma asibiti acan suka hau tsananin bincike da tantancewa tareda aune aune.

Kansa ba qaramin zafi ya dauka ba
Ita kanta mum din tana cikin fargaba da tashin hankalin abinda zasu iya tabbatarwa.

Haroon ya kira yaje ya taho dasu umma da fadila wadda kwata kwata bayason ana damar da ita da yawo.

A cikin Daren kwana sukai shi da mum dinsa da wasu amintattun likitocinsa suna bincike da aune aune harma da hotunan Daya kamata suyi mata duk sunyi.

Sai asuba suka samu kansu tareda tabbatarwa da Jamaal chances na surviving dinta Bai wuce 2% ba sbd koma Menene aka rikida oxygen din data Dade tana shaqa yayiwa lungs nata da cikin mummunan illanda sai addua kawai Amma dai idan har ta take lokacin aurensu zasu tafi da ita waje su miqawa wasu manyan likitocin su Gani ko zaa samu 2% din tayi Aiki.

Sakamakon Bai gama kammaluwa duka ba Dan haka mum ta Hana a sanar da Jamaal din abinda suka fara Gani Dan bandashi Akai sauran aikinba ta sallamesa ne.

Da kansa ya mayar dasu umman gida Haroon Kuma ya tafi da mum gida.
#MAMUH#
#DR JAMAAL JEEY SEELAH
#AMEENATOU SEELAH
#DR ALEENA SEELAH
#MAM SEELAH
#LAMEENU SEELAH
#OMAR SEELAH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected