AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
“Karka damu she’s okay”
“I love her Mum”
“I know son”
Wucewa tayi ta gaba Omar ta wuce hanyar dining room Dan Yi musu iso ya bita da Wani irin tsaftataccen kallo.
Dining suka nufa dukkaninsu Banda Jamaal daya fice ya nufi bedroom din Mum dinsa.
Koda ya shiga tana jikin Ashley tana tsiyayo hawaye Ashley na share mata tana cewa
“Baby kukan ya isa haka kinsan daman ba isashiyar lafiya ne Dake ba zaki iya jawowa kanki Wani zazzabin akan Wanda kike fama dashi”
Qamshinsa ne ya Saka Ashley dagowa ta kallesa fuskanta Babu walwala sbd itama taji kunya da damuwan abinda yayi musu din ba zata.
Miqewa tayi zata fice batareda tace masa komaiba Ameenatou da Bata dago ba sbd tasan shi dinne ta riqeta tana Dan Bude Baki tace
“Ash gida zan tafi ki fadawa Hafiz yakaini”
Numfashi Ashley din ta sauke tareda dagowa ta Kalli Jamaal din wanda Am din yake kalla kafin ya Kalli Ashley yace
“Kije zan kaita gidan da kaina”
Ficewa Ashley tayi tabarsu su biyun.
Miqewa Ameenatou tayi tana goge fuskanta da tissue ta nufi kofa zata fice daga dakin.
Hannunta ya riqo tareda dawowa da ita zaiyi magana ta dago jajayen Idanuwanta ta masa Wani kallan tsananin zafinsa datake ji Cikin ranta.
Rungumeta zaiyi ta turesa tareda Bude bakinta zatai magana sai Kuma ta fasa kawai ta wucewarta ya sake riqota ta fizge hannunta tareda ficewa daga dakin.
Kai tsaye dining room din da kowa yake ta nufa tana zuwa ta zauna Babu wanda ta kalla sbd Zuciyarta Dake Cikin zafi da baqin Cikin kunyar datake daure da ita gashi kusan kowa Yi yakeyi Yana kallanta.
Fatmah da Mummy dinta ta rarrasheta ta samu ta Dena kukan itama kasa riqe abinda takeji tayi kaman yanda Ameenatou ta kasa riqe nata Dan haka kusan tare suka miqe daga dining din.
A tare suka Kalli hafiz dayaji saukan Idanuwansu akansa lokaci daya
Ya dago ya fara kallan Fatmah data ambaci sunansa Cikin sanyin murya kafin Ameenatou.
Kowa a tare ya kallesu harda Jamaal daya Kalli am Yana dauke Idanuwansa sbd yasan bazata taba yadda ya kaita ba Dan haka baice komaiba.
Hafiz tissue ya dauka ya goge bakinsa daga abincin dayake Ciki ya miqe tsaye Yana cewa dukkaninsu su biyosa.
Suna barin dining room din juyowa yayi ya fara kallan Fatmah zaiyi magana hawayen Idanuwanta suka sauko mata ta katsesa da cewa
“I wanna go home please” ta qarasa zancen da sanyin murya da Wasu siraran hawayen.
Kallanta yayi Cikin nutsuwa kafin ya dawo da kallansa kan Ameenatou da alaman ita fa??
Itama Bude bakin tayi Cikin sanyi tace
“I wanna leave this place too please”
Numfashi ya sake Yana cewa kowacce ta share hawayenta.
Ciki suka koma Suna bayansa sukai sallama da kowa suka juya suka fice.
Jamaal kallan nutsuwa yabi bayan Am din dashi Yana Jin sonta da babyn Cikinta na sake cikesa.
Dr Aleena ma Jin tayi kaman ta janyota ta hanata tafiya sbd Jamaal dinta Amma Kuma ganin yanda Omar ya sakewansa Yana murmushin data San Kila na mugunta ne ya sakata jifarsa da harara.
A yanzu Kam tabbas zai Saka Ido yabarwa babbah komai sbd yasan iya maganar ma an karba auren rigimace a gurinsa bare ganin Ciki kawai a jikinta ko jinsa.
A mota Ashley da Ameenatou ne a baya Fatmah a gaban motar tana tsiyayar hawayenda har Lokacin ba wanda yasan n menene hakama ba Wanda ya tambayeta tinda kowa ta gabansa ta ishesa
Hafiz ne kadai ya zaro tissue daga miqa mata Yana Dan juyowa ya kalleta itama kallansa tayi tana marairaicewa kaman zata fasa Kuka me qarfi ta karba tana share hawayenta.
Suna isa gida kowa ya fice daga motar Babu me magana kowa dakinsa ya nufa Cikin jimami.
Arfat na can gurinsu Mum Nur Dan haka daga Ameenatou din har Ashley tubewa sukai sukai wanka da Shirin bacci suka kwanta.
A dakin Ashley tayi kwanciyarta tanaji wayarta na ringing taqi dauka.
Ashly kuwa daman ta kashe tata sbd tin a hanya take ganin Kiran siddeeq taqi dauka.
Acan kuwa sai dare sosai su Dad suka dawo gida aka baro Arfat acan sbd Dr Aleena data roki Dad din wanda daman sunada siyayyar Arfat din dasukeyi sosai a gidan da Shirin idan ya taho Dan haka Babu buqatan komai nasa.
A hanya Mum Nur ta tada maganar Cikin Ameenatou din tana sake nunawa Dad din Dan Allah kada yayi wata maganar bayan a Saka lokacin bawa Jamaal din matarsa ta haihu acan tinda dai ta tabbata Jamaal din shine mahaifin Arfat sbd idan ya sake tada wata maganar kunya sosai take Saka Ameenatou wannan halin Kuma ba Dadi hakan kada m Wani ciwon ya shigo yinda dai yanzu ba ita kadaice ba.
Murmushi yayi kawai Yana Jin kaunar ‘yarsa da duka jikokin da zata Haifa masa sedai yasan ba shine matsalar ba a yanzu babbah ne Kuma shi duk da shine ya haifeta bazai taba hada girman babbah a kanta ba da kansa sbd son da babbah yake mata ko yayansa daya Haifa baya musu wannan son hakama Babu Wani Rai ko Abu dayakeda Mahimmanci a rayuwar babbah kaman Ameenatou sbd itace hasken zuciyarsa da Idanuwansa Dan haka Babu wani Iko da kowa a duniya zai nuna mas akanta shine me cikakkiyar ikonta Dan haka sai yanda babbah yace a yanzu Dan shine akaiwa babban laifi musamman ta yanda zai samu bayanin ARFAT Jamaal ne ubansa na asali..
Suna isa gida gidan tsit da alama kowa Yana daki Yana jimami Dan haka Suma Kai tsaye kowa makwancinsa ya nufa.
Babbah baisan meyake faruwa sbd Babu wanda ya fada masa Dan haka hankali kwance ya tashi sedai Jin gidan tsit Babu motsin kowa ya Saka dadah Tinanin ko lafiya Duk da haka sai tayi tinanin gajiyan daren da sukai ne jiyan ya Saka kowa hutawa ba buqatan fitowa da wuri.
Sai kusan 12 na rana tukuna suka fara fitowa daya bayan daya kuma a Lokacin ne zasuyi breakfast Wanda yake hade da lunch sai Kuma dare.
Fatmah datake sanye da pencil jeans da knit freesize Riga fara tana fitowa daidai Lokacin Jamaal ya shigo palon tareda Siddeeq Arfat Yana jikinsa.
Tsayawa tayi tana kallansa cikeda Jin kamarma ta tsanesa sbd abinda yaji din dan Bata dauka zai mutu akan macen da aka fada masa ta haihu baa San uban Dan ba.
Ko kallan inda take baiyiba sbd baima lura da ita kwata kwata ba Siddeeq ne kadai ya Dan kalleta Shima baice mata komaiba ya wuce.
Ameenatou ce da Ashley suka sauko daidai lokacin Suma
Ta Kalli Ameenatou din da Idanuwanta da sukai ja ta kasa riqe bakinta Cikin son samun amsar tambayarta tace
“Dagaske Cikin ne Dake?Kuma na wanda ya fada din?
Ke shikenan haka zaki ringa Ciki sedai a ganki dashi batareda sanin yaushe kike yo war abinki ba….
Dago jajayen Idanuwanta Ameenatou tayi ta Kalli Fatmah din wadda itama zancen ya fito mata Cikin ciwon yanda take jerosa.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
145
Ashley ce data sauko taji maganar ta Kalli Fatmah din zatai magana Ameenatou ta tareta ta hanyar cewa
“Menene naki a Cikin duk yanda nake daukan Cikin,inace nine nake dauka Kuma nake haihuwar”
Cikin takaici Fatmah tace
“Babu komai nawa a Ciki Amma keda kikeda komai a Ciki na dauka zaki fara tsayawa kisan mahaifin cikinki na farkon kafin ki sake kwaso Wani….”
“Duka wannan ba matsalarki bace Kuma bakya Cikin wainda suke dole da Susan mahaifin ‘dana sbd bakida alaqa da hakan bake ba kadai ko wanda suka Fiki banajin sunada alaqa da sanin hakan,nice dole Kuma nice na San waye uban Dana”
“Wane Dan ne kikasan ubansa?” Sukaji an fada daga bayansu Cikin mamaki da sauti me tattareda bawa maganar Mahimmanci.