AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Su biyar din basu taba rabuwaba tinda suke a rayuwarsu sai wannan ranar da biyunsu suka bar duniya gaba Daya sai Kuma yanzu da zaa tafi da Omar abarsu Badan sunso ba sai Dan ana son nuna musu fin karfi.
Mr Jaden da tin farko Allah ya Saka masa kasim arai sosai fiyeda kowa a Ashalawa sbd ladabinsa da nutsuwarsa data fita daban haka kawai yaji bazai iya barin Omar ba a Nan bayan rasuwar kasim Dan yariga yayi musu alkawari hakama zuciyarsa Bata yardar masa barin Omar a tsakanin mamman da lameenu ba Dan haka baiyi tsaiko a tafiyar tasu ba duk yanda Omar ke cikin tsananin tashin hankalin rabuwa dasu mamman Amma Shima yanason cika burinsu shi da kasim na rayuwar Kwanciyar hankali da nutsuwa tareda wadatar ilimi Dan haka yabi Mr Jaden din tinda su mamman din zasu biyo Daga Baya.
Mamman da lameenu tamkar tsokar jininsu ce ake yanka ana rabasu da ita sukeji a lokacinda suke kallo Omar zai tafi da tarin arzikin da suke ganin sunada cikakkiyar haqqi akanta tinda sune sukai aikin kawar da me ita din Dan haka kukansu da baqin cikinsu na tafiyar akan Hakan ne sedai zuciyoyinsu ne kadai ke kika Banda idanuwansu da suka bushe Babu komai Dake cikinsu bayan radadin Jan bacin Rai suna kallo har Mr Jaden Dake riqe da hannun Omar ya jasa suka nufi filin da helicopter din dazai daukesu yazo ya daukesu suka bar dajin Ashalawa.
##MAMUH#
#TOOTOOHOT
#JAMAAL JEEY SEELAH
#AMEENATOU SEELAH
#ZAFIN KAI
#LOVE
#DEEP
#ROM
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
#Arewabooks@Mamuhgee
5
Lagos suka Isa da Omar Wanda tini zazzabi da ciwo me karfin gaske ya rufesa Wanda idan suka so a lokacin Mr Jaden zai iya karasa illatasa ya gudu da dibbin dukiyar Amma Sam har cikin ransa bayajin zai iya Hakan Dan take kaunar Omar din ta cikesa musamman da a bayyane mutuwar Rabin jikinsa ta tabasa wadda ba zai taba mantawa har abada ba,Dan ko Babu kauna irin shaquwa da rashin rabuwarsu tin haihuwa dole kowannensu ya rabu ciki kuwa harda su mamman duk da babu Wanda yasan sune sukai kisan.
Mr Jaden na da gidan kansa Daya mallaka a cikin garin Lagos me girman gaske Dan haka ba asibiti ya nufa dashi Kai tsaye ba gidansa dayayi kama da Akira mansion suka nufo bayan yasa ankira likitan da zaizo ya duba Omar cikin gaggawa.
Isarsu Babu Bata lokaci aka shige da Omar har Daya daga cikin dakunansa Dake sama har cikin toilet take manyan yaransa biyu Ahmed da Aron suka gyare Omar din tsaf suka tsaftace sa daga datti da jinin jikinsa da duk ya bushe.
Kusan Omar din Baya hayyacinsa Dan haka suna gama gyarasa kusan gajeran wando sabo kadai suka Saka masa sai aka kwantar dashi a lafiyayyar gadon Dake dakin tareda ragewa AC karfi suka fice daidai isowar likita da nurse namiji Daya sai Mr Jaden.
Bude musu dakin Ahmed yayi Yana matsawa gefe suka shiga.
Kallansa Dr yayi ya raunikan jikinsa sai Kuma zazzabin gaske me qarfi dayake Saka jikinsa wani irin jijjiga.
Babu Bata lokaci ya fara dubasa cikin sauri sbd ganin Yana buqatan taimakon gaggawa.
Da farko akwai inda yake buqatan dinkuna sosai a jikinsa sbd deep yanka Daya samu sosai Dan haka su aka fara duk da an masa allura Amma Yana cikin azaba sosai sedai ko motsi Baya iyawa har aka dauki tsawon lokaci sosai aka gama.
Ruwa da wasu alluran akai masa tareda rubuta maganin da zai buqata Sha suka fito akan zaa daukarwa Omar din nurse me kulawa dashi.
Bayan tafiyar su Dr sai alokacin Mr Jaden ya samu kansa Shima yaje yayi wanka yaci lafiyayyar abincin da aka jere masa su a dining ya koshi ya kunna wayoyinsa ya ringa wayoyi tsawon lokaci kafin ya shige yayi Kwanciyarsa yafara baccin Hutu.
Omar Bai farfado ba sai bayan kwana Daya da wuni Wanda har hankalin Mr Jaden yafara tashi sai gashi ya farka Kuma lafiya kalau Babu zazzabi ko wani ciwon sai raunikansa da Suma zasu warke a hankali.
Kulawa dashi sosai nurse dasu Ahmed sukai harya samu damar yin wanka da kansa yayo alwala yazo Ahmed dayake musulmi Dan uwansa ya nuna masa gabas yayi ramakon sallolin dasuke kansa duk da ba wani ilimi ko sani akan Addini suke dashi sosai ba Amma dai sunsan sallah Kuma basa tsallaketa.
Ko kafin ya gama sallolinsa tini aka shigo da abinci aka jere masa su lafiyayyu masu Kara lafiya da drinks masu sanyi kadan.
Aron ne ya shigo Shima da wasu sabbin kayan sakawar bayan wainda aka kawo masa kafin ya fito wanka.
Yana idar da sallan abincin ya kalla tareda juya idanuwansa Yana sake kallan dakin dayake ciki din Wanda Basu taba sanin akwai tsari irinsa ba duk yanda suke hararo rayuwar kudi da Jin dadi Basu dauka haka abin yake ba a zahiri.
Tamkar mace haka yaji idanuwansa sun ciko da wani irin Hawaye masu tsananin zafi da radadin rashin su kasim a duniya daidai lokacinda ya kamata su ji dadi,
Bai taba sanin samuwar arzikinsu zai tafi da jini da rayuwar Yan uwansu Rabin jikinsu ba da tini ya Dena rokarwa kansa arzikin.
Su kasim sun bar duniya basa tareda shi hakama su mamman dasuke raye a yanzu basa tareda juna,tayaya zai fara rayuwa Babu su,Suma su mamman din tayaya zasuyi rayuwa Babu shi din.
Share hawayensa yayi yana daga hannuwansa yayiwa iyayensu dasu kasim adduar dacewa da Rahama Suma su mamman yayi musu adduar Allah ya Basu abinda sukai burin samu acan Ashalawa din kafin su baro.
Miqewa yayi daidai shigowar Ahmed Wanda kaman shine Mr Jaden ya bawa Ragamar kulawa da Omar yanda ya kamata tinda sune suke Addini Daya da juna.
Kallansa Ahmed keyi Yana Dan sake fuska cikin kulawa ya sanar dashi ya taso yaci abinci sbd lokacin Shan maganinsa yayi.
Ba musu Omar din ya taso sbd su Ahmed din sun girmesa sosai Dan alama Dan zasuyi shekaru talatin su zuwa sama shikuwa a lokacin ne suke shekarunsu na ashirin zuwa da Daya.
Abincin kudi Kai tsaye zai kira abinda yake kalla a gabansa da sunan abincin,
Brown basmati rice ce da aka dafa da abubuwan da bama zai iya gane me dame bane a ciki Se brown chicken breast a jere cikin wata glass bowl daban.
Ahmed ne ya basa kwari gwiwan fara cin abincin Wanda Yana fara Kai spoon na farko bakinsa idanuwansa suka ciko da Hawaye zuciyarsa na karyewa da tino Yan uwansa su mamman ko sun samu sunci abincin Daren kuwa kokuwa ma kila suna can cikin azabar duhu da zafin ramin gurin Gina.
Ahmed Dake kallansa Yana tinanin Allah me bawa Wanda yaso,
Gasunan dai sunata Fadi tashin nema Amma ga yaro qanqani kaman Omar Allah ya basa Arzikinda zasu lalace a karkashinsa gurin bauta masa kaman bayi.
Harya ci abincin ya gama Hawaye ne ke tsiyaya daga idanuwansa da sukai jajir Babu farin ciki ko kadan a ransa Dan kuwa rayuwar da zai fuskanta Babu seelahs ko Daya a cikinta bazai taba farin ciki ba duk Jin dadin dazai samu acikinta.
Bayan gamawarsa Ahmed da kansa ya kwashe kayan ya fice dasu tareda dawowa sukai sallahn ishai a tare dakin tukuna ya fito ya sauko ya barosa ya sake samun hutawa kaman yanda Mr Jaden yace abarsa ya huta sosai ya dawo daidai tukuna.