AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Karki sanar da kowa zuwa anjima idan jikin baiyi sauki ba zan sanar da Daddy”

Numfashi Mai sanyi safiyya ta sauke ahankali cikin tausayin Aminar idan nakuda ce tace

“Toh shikenan Allah ya Baki lafiya yakuma saukar Dake lafiya”

“Amin” Aminar ta amsa daqyar tana Dan daurewa bayan ta amsa ruwan a dogon glass cup Tasha kadan ta ajiye.

Bayan fitar safiyya sosai tafara Jin yanayin na karuwa har Akai magrib ta tashi daga Palo Takoma bedroom tayi alwala tayi sallah,
Tana idarwa ta fito taje bedroom din Omar bayanan ya fita sallah.

Koda ya dawo a tare suka zauna palonsa sukaci abinci Wanda kadan ya Bata a baki tace ta koshi ta tattara kayan da kanta ta fita dasu.

Daga can Bata dawowa dakinta a ta shige tayi sallar ishai tayi Shirin bacci ta kwanta a dakinta sbd batason zuwa dakinsa ya gane halinda take ciki.

Yana masallaci sallan ishai Babba ya iso ba qaramin mamakin ganinsa yayi ba sbd Babu Wanda yasan yana tafe har aminan Bata saniba.

Cikin kulawa da farin ciki sosai ya tarbesa suka shigo Kai tsaye masaukinsa suka nufa sbd Amina tariga tayi bacci dukansu sun sani Dan haka babban yace abari da safe kawai tagansa har murna saitafi ma.

Ba musu Omar yayi Naam Dan Hakan Dan haka take aka kawo masa abinci kala kala aka sake gyare masa boys quarter din aka kawo cartons na ruwa da drinks aka Saka a fridge sukai Saida safe ya fice yabarsa akan Saida safen.

Har bedroom dinta yace yaga bacci ya dauketa me sanyi da nutsuwa Dan haka Bai tayarda ita ba ya kyaleta ya wuce bedroom dinsa kawai sbd yasan tana buqatan hutawa sosai Akai Akai sbd cikin jikinta.
#MAMUH#
#MAM#LAM#OMAR#SEELAHS
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#HAROON SEELAH
#LOVE
#CRAZINESS
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU SEELAH

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar

13
‎‎KISSA TRAINING CLASS

MASU SO SU KOYI KISSA
MASU SO SU IYA KISSA
MASU SO SU SAN KAN KISSA
MASU SO SU ZAMA HATSABIBAI AKAN KISSA
GANE IDAN AN SHIRYA MIKI KISSA
KISSAN IYA KWACE DANGIN MIJI
KISSAN IYA KWACE MIJI
BA BOKA BA MALAM BAKUMA MAGANI KAWAI KISSA KADAI

ZOKI SHIGA AJIN KISSA DA NAIRA DUBU KACAL!!!
5DAYS TRAINING CLASS WANDA BABU YANDA ZA’AYI KIYI TRAINING DIN NAN BAKI IYA KISSA DA KISISINA BA.
KISSA SHİNE BABBAN MAKAMIN MATAR AURE❤️
ZOKI SHIGA KAFIN KISHIYARKI TARIGAKI SHIGA

KISSA CLASS PAYMENT IS 1k

GUESS WHAT 5 LUCKY ACTIVE MEMBERS ZASU CI NAIRA DUBU ASHIRIN EACH 20k EACH

ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN SET NA TURAREN WUTA BY RUKY

ANOTHER 5 LUCKY MEMBERS ZASUCI KYAUTAN KAYAN MATA FROM HONEYDROPS KAYAN MATA
JOIN YANZU YOU MIGHT BE THE LUCKY WINNER

CHAT ME UP DON SHIGA WANNAN KISSA TRAINING CLASS
07012181461

****************
Kwantawa yayi Yana waya da Nur wadda ke sanar dashi zuwan Mam ayau din gidanta ya kawo mata ziyara tareda Jamaal harma ya Bata kyautan 5000 dollar.

Numfashi ya Dan sauke ahankali Yana Jin dadin kulawansu ga Iyalin juna shiyasa ma yake Jin damuwar tinanin Dake shigarsa na son tattarawa ya koma inda ya fito sbd tsaron lafiyarsa data iyalinsa da ‘yayan da zaa fara Tara masa amma Kuma Yana cikin damuwa da baqin cikin rabuwa da ‘yan uwansa da sukai alkawarin rayuwa tare su mutu tare.

Bayan gama wayarta guraren 1 na dare ya tashi yayo alwala kaman yanda ya Saba yazo ya tayarda sallah.

Ya Dade a farke Yana adduoinsa da Babu Daren da bayayinsu tinda ya samu kansa a rayuwar Kwanciyar hankali da nutsuwa Bai taba tsallake Daren da Baya sallolin dare da adduoi ga iyayensa na asali da suka haifesa Dasu kasim ba da iyayensa na riqo harma da ‘yayan da baisan zai haifa ba Yana musu adduar zuwa duniya lafiya suyi rayuwarta lafiya Kuma su komawa ubangijinsu lafiya.

Karfe uku na dare ya miqe daga lafiyayyar gadonsa bayan ya kwanta sbd dubo Amina Dan Basu taba kwana na tareda ba idan har Yana gari sai yau din,
Kuma motsi yaji kaman harma da magana Dan haka fito Yana sake kallan agogo Kai tsaye ya nufi hanyar bedroom dinta.

Koda ya tura kofar bedroom din tana zaune tsakiyar gadonta ta hada zufa sosai idanuwanta sunyi jajir tana cikin azaba Mai tsananin gaske.

Cikin sauri ya qaraso gurinta Yana ambatar sunanta cikin kulawa Mai tsananin gaske da tashin hankali.

Hawa gadon yayi Yana kama hannunta datake qanqame gado dashi,
Cikin tausayinta me tsananin gaske yace

“Labor ne?,tin yaushe kika fara ciwon?
Meyasa Baki sanar saniba?

Saukowa yayi gadon ya koma bedroom dinsa ya dauko wayarsa yafara Neman wayar Ahmed yanason sanar dashi suna buqatan zuwa asibitin a tsakiyar dare Kokuma kawo likita gida Amina zata haihu.

Kasa samun wayar Ahmed din yayi yakoma Kiran ta Aron shikuma tashi Bai dauka ba.

Saukowa yayi kasa ya nufi bangaren masu aiki da kansa yayi knocking ya kirawo safiyya ta fito sbd tafara manyanta dole tasan kan haihuwa kafin ya samu Ahmed.

Komawa yayi dakinsa Yana ci gaba da Kiran wayar Ahmed Baya samu Dan haka ya yanke shawarar fitowa da kansa yaja mota yakaita asibiti sedai fitowarsa harabar gidan yafara cin karo da abinda ya girgizasa.

Jini yagani a gurare daban daban a harabar gidan Wanda yake fresh da alama yanzu yanzu jinin ya zuba duk inda ya fito.

Tashi hankalinsa yayi take ya juya da sauri zai koma cikin gidan sedai ko taku Daya beyiba wutar gidan ta dauke gaba Daya abinda Bai taba faruwa dasuba a rayuwar gidan Dan haka gabansa yayi mummunan faruwa da wani irin mugun sauri ya nufi ciki Yana jefa kafafunsu cikin duhu wayarsa tini ya saketa ya dawo ga matarsa.

Acan cikin gida kuwa tini nakuda ta tasowa Amina gadan gadan a yanda take safiyya ma Bata tinanin zaa iya daukanta zuwa asibiti Dan komai yazo gab.

Babbah da Shima haka kawai ya kasa bacci duk tsananin gajiyar Daya debo Yana Jin motsi ya leqo idanuwansa suka sauka akan Omar Daya fito harabar gidan seikuma gashi an dauke wuta.

Harya koma ya kwanta saikuma ya Tina da akwai me ciki a gidan kodai nakuda ta tasowa Amina ne?

Tashi tayi batareda tinanin komaiba ya fito daidai ganin wulgawar mutane kusa Guda biyar zuwa cikin gidan ta kofar Baya take gabansa ya Fadi Dan yasan dai gidan baa dauke wuta hakama su waye suka shiga gidan.

Shima duhun ya ciyo yayo cikin gidan Kai tsaye kofar da mutanen suna shiga Shima ita ya shiga Dan Baya tsoron barayi Sam tinda Shima ya samu damar satar zeyi idan bazaa kamasa ba.

Shigowar babbah ta kofar Baya da shigowar Omar ta kofar gaba duk basuyi nasarar rigan mutanen Isa ga dakin Amina ba inda take kwance cikin tsananin azaba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected