AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

 

***********
Hawayen farin Ciki Mai tsanani ne ya ciko Idanuwanta tana kallan Arfat din fuskanta na bayyana hakan,

Takowa tayi tana nufosa Shima tsayawa yayi Yana kallanta da Blue Idanuwansa gefen momma dinsa.

Ameeenatou data sake fuska tana kallan Ashley gyada mata Kai tayi tana cewa

“NUHU ARFAT hs name”

Dawo da kallanta kan Arfat tayi Ciki kulawa da sakewan fuska sosai tana nuna masa Ashley tace

“Arfat,your special Aunt Ashley,
Say hello”

Sakin fuska yayi Yana kallan Ashley din ya maimaita sunan special Aunt Ashley da bakinsa kafin ta ware masa hannu ya tafi kuwa ta masa kyakkyawar runguma tana Maida hawayenta na farin Ciki sbd murnanta tai yawa,

Babynsu ne wannan na asibiti,.
Babynsu ne da suka Sha gwagwamarya akan samuwarsa da renonsa.

Wani kaunarsa itama taji ya mamayeta Dan haka ta dagosa tayi kissing hannunsa tana shafa fuskansa ta tambayesa Yaya yake
Ya amsa Yana kallanta Cikin sakin fuska.

Dagowa tayi ta kalli Ameeenatou Dake kallansu tana murmushi cikeda kauna da kulawa kafin ta Bude Baki tayiwa Ashley din barka da tashi.

Sarrah ce ta sake dawowa dakin dauke da lafiyayyan breakfast din Ashley din ta ajiye akan table tareda gaidasu cikeda girmamawa ta juya ta fice.

Tana ficewa zaunawa sukai anan sukai breakfast tare Arfat Yana jikin Ashley da kanta ta ringa feeding dinsa da kanta Suna magana da Ameeenatou din Cikin nutsuwa da kokarin sakewa da juna.

Saida suka gama suka sauko qasa Sarrah Kuma ta hau Dan tattara inda suka gama din.

Kai tsaye bangaren Dad suka fara zuwa suka gaidasa ta sake gaisawa da Mum Nur da Dad din harma da uncle Ahmed da Didi
Fatmah ma duka an gabatar musu da Ashley din daman a gurin breakfast Dad ya fadawa kowa matsayin Ashley a familyn daidai yake Dana kowa sbd inshallah ta zama tasu sune familynta ayanzu kaman yanda itama sune nata familyn a yanzu.

Babbah yayi mamakin hakan sedai Kuma Dad din ya sanar dashi sunyi magana da Ashley batasan waye uban Arfat ba Dan haka kawai kaman yanda suka rufe zancen basa tayarwa sunbarwa Allah.

Babbah yayi farin Cikin ganin Ashley sbd Yana kaunar duk me kaunar budurwansa musamman ita datai Wani irin zaman tsakani da Allah da ita.

A bangaren su babbah suka wuni Cikin kauna da kulawan dadah sai Rana bayan azahar Hafiz ya fito ya shigo palon su dadah sanye da guntayen kaya lafiyayyan fatar jikinsa na daukan Ido ya zauna cikinsu a tare sukai lunch dukkaninsu
Ashley na ganin kauna da kulawan dayake ta sakata hawaye tana hadiyewa sbd tsakani da Allah suke nuna mata kauna da kulawa.

Har dare suna bangaren su dadah sai da sukai dinner gaba daya gidan a tare dining room suka sake tattaunawa da Ashley Dan ta sake da kowa Dad Omar yace ta shirya washe gari akaita siyayyar abubuwan buqatanta.

Mum Nur ma haka ta sake Janta a jiki Cikin sakewa da magana hakama Didi
Su dadah kuwa already tafara Dan sakewan dasu a wuni daya.

Suna hayewa sama wanka kowannensu yayi tareda sallan ishai da Akai tini kafin Sarrah ta dauki ARFAT daga dakin Ashley takaisa dakinsa tai masa Shirin bacci ta dawo dashi dakin sbd Ashely tace abarsa ya kwana gurinta.

Ameeenatou tana gama Shirin bacci kwantarwa tayi duk da tanada aikin dataso dubawa a laptop Amma sai safe.

Washe gari AM Bataso zuwa office ba Amma akwai meeting da zasuyi dole tana buqatan halarta Dan haka Mum da Ashley dinne suka fita tareda driver a Cikin lafiyayyar motar data Saka Ashley sauke ajiyan zuciya.

Suna isa Mum Nur gurin hutarwa VIPs ta nufa ta zauna ta bawa Ashley card tace duk abinda idonta ya sauka Akai tana buqata ta dauka.

Siyayya sosai sukai wadda tayi yawan daya bawa Ashley tsoro sbd data Dan kwatanta ta dauka Mum shirme ta dauki siyayyar Dan haka da kanta ta tashi ta dibar mata asalin designers din gaske suka zubar da kudi suka dauki kaya wanda sedai motar gurin ce ta Kai musu kayan gida su daga Nan gurin siyan kayan native suka nufa anan ma wasu mahaukatan laces masu kudin gaske ta dibar mata da atampopi ready made din kwarai suka sake zubarda kudin kafin suka nufo gida.

Suna dawowa a gajiye Babu abinda sukai abinci suka zauna suka ci Koda Ashely ta isa dakinta tini Sarrah ta gama jere komai ta tsarasu hatta shoes da bags da Tarin uban undies din tini ta gyara komai ta jeresa.

Wanka tayi ta fito ta nufi dakin Arfat lokacin Sarrah na tareda shi tana tayasa wasa da books dinsa na drawing.

Yana ginin Ashley ya dawo gurinta suka dawo palon saman suka zauna kallan cartoon tana biyewa wasansa.

Sai yamma Ameeenatou ta dawo gida a gajiye tareda Hafiz da Fatmah wadda itama gabaki daya ta lafe sbd jiran inda tashin hankalin maganar data fada zata fara bullowa sbd tasan Jamaal bazai yadda da aurenba ayanzu a dayan tinaninta Kuma shirun dayayi ya fasa auren ne Shima yabarsa.

A jere motocinsu suka shigo Mansion din kowa yayi parking ya fito sukayo Ciki.

Samanta ta wuce Kai tsaye sbd gidan tsit su Dad tasan basa Nan Mum Nur Kuma tana samanta Didi Kuma tana kitchen ta sani.

Tana shigowa palonsu na saman Arfat Dake tsalle jikin Ashley da gudu ya sauko yayi gurinta Yana ambatar sunanta.

Cikin farin Ciki ta rumgumesa tana kissing gefen fuskansa tayi gurin Ashley tana mata magana.

Bata Wani zaunaba ta wuce daki Saida tayi wankan tai sallan laasar ta shirya ta fito Cikin skinny jeans da shirt me Fadi tazo ta zauna Sarrah ta kawo mata abinci anan ta zauna tanaci Suna magana fira da Ashley harta gama.

Cikin kwanaki kalilan Ashley ta Sabu da familyn duka ta sake a cikinsu ta koma yar gida sosai ake kaunarta ba banbanci ta zama yar gida hakama itama bata Wani son zaman banzan saukowa takeyi ta tafi kitchen tareda Didi suke aikinsu masu Aiki na kamawa sbd didi karshe ce a bangaren girke girken zamani Dan certificate dinta na girkin sunkai kusan hudu Dan haka Ashley ta saki jiki tana koya sai ya zama sun dinke sosai da Didi Dan har fita sukeyi su kadai da mota idan gidan ya watse kowa na gurin Aiki.

Ameeenatou tayi busy sosai a kwanakin sbd ayyukan gabansu itada hafiz Dan Shima kusan Saida yayi tafiyar kwana uku ya dawo.

ARFAT ma shaquwa ce Mai tsananin gaske ta shiga tsakaninsa da Ashley sbd irin Azababben kaunar datake masa yanzu a gurinta ma yake kwana itace ke masa kusan komai Dan haka ita yakewa shagwaba yanzu.

Bata rufa sati hudu a gidan ba Dad ya Siya mata lafiyayyar motarta Allah ya taimaketa ta iya tuqin sbd lokacin Abdulra’uf Yana Raye yayi mota kafin suka siyar daga baya.

Rayuwar Ashley ta sauya daga sister Ashley zuwa Ashley Ra’uf Cikin qanqanin lokaci.

Ta dawo fresh dinta tayi kyan Gani haskenta ya bayyana sosai ta samu kwanciyar hankalinta da nutsuwa.

JAMAAL kuwa da Siddeeq kusan babu ranar da basa waya Amma Babu wanda yasan da hakan sbd su kansu gidan mamakin jinsa tsit sukai tsawon lokaci Amma dai Babu wanda yayi maganarsa.

Ameeenatou ta samu kanta Dan haka ta shirya hutawa zatai na sati biyu kafin ta fara fita aikin.

Kwananta biyu Bata fita koina ba tana hutawa a gida sai ranar na ukun suka shirya itada Ashley da Arfat suka fita yawo.

Riga da skirt ne a jikinta na Wani simple lace se shegiyar tsada daya kwanta ba nauyi ko kadan maroon kala sai black a jikinsa kadan kadan.

Qaramin veil ne a jikinta wanda ko handbag Bata fito da ita key din motarta ne kadai sai wayarta sai Kuma card dinta dayake Cikin jakar Ashley wadda itama kanta Ashley a account dinta zaa samu lafiyayyun kudi yanzu sbd Dad dayake sakar mata yanda ake sakarwa kowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected