AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Yana shigewa siddeeq din ya rufo kofar tareda tattara aikin Daya zo dashi ya fice office din tareda rufewa bayan ya kashe masa laptop dinsa Dake kan table a kunne.
JEEY kuwa Yana shiga bedroom din Kai tsaye lafiyayyar gadonsa Dake cike da pillows masu shegen laushi da beddings masu laushin gaske da tsada sanyin AC da qamshi sun kamasu ya kwantar da ita har lokacin idanuwanta a Bude suke sedai sun Dan lumshe alaman azaba kadai ce ke mata yawo a jijiya.
Ahankali ya janyo duvet Dake Bakin gadon ya rufe Rabin jikinta da kusan duka Rabin nata kayan Suma ta yagasu.
Miqewa yayi tareda juyowa ya shige toilet Kai tsaye Wanda yake kusan na gidansa sbd gyara da wata lafiyayyar Shirin da siddeeq yayi masa.
Tsayuwa yayi a mirror batareda ya iya kallan fuskansaba sbd Wani irin radadin daci da qunci ne ya rufe zuciyarsa na ganin halin Daya Saka ‘yar mutane,
Bai taba tinanin zata samu kanta a wannan mummunan halinba da bazai taba yi mata alluran da yayi mata tin farko ba,
Bai taba sanin alluran da yayi mata da hannunsa zai lalata rayuwarta Hakan ba sai yau Daya sheda wace irin rayuwa take ciki ganin idonsa,
Qattin Maza ne ke Kai hannuwansu jikinta suna danneta da hannuwan nasu ana cutatar da rayuwarta da magani da alluran da kasheta ma zasuyi ba iya haukantar mata da Kwakwalwa kwata kwata ba….
Rintse idanuwansa yayi da suke masa Wani radadin yaji yaji sbd tafasan da zucuyarsa ke yi.
Rigar jikinsa ya zare a hankali tareda jefarwa cikin laundry Yana zare har wandon ya janyo sabon towel ya zare daga leda ya jefar da ledan Yana Jin kansa na daukan wani zafin gaske da abubuwan Dake dawo masa.
Ruwan dumi ya sakarwa kansa Yana rufe idanuwansa ahankali ruwan na bin fuskansa zuwa wuyansa da shatin raunin datai masa suna tabawa Wani radadin na sake shigarsa Amma radadin dayake ransa yafi na raunin ciwo.
Ya jima kafin ya fito daure da towel ya goge jikinsa ya Saka wasu kayan bana bacci ba tinda baa gidansa yake ba,
White Nike loose fit shirt ya saka da white wandon me tsayi.
A single couch Dake dakin ya zauna ahankali tareda dago idanuwansa da sukai wani irin laushi sun cire Jan da sukai ya zubawa fuskanta Dake kwance kan pillow Daya Saka mata gashinta duk ya warware ya fita band da aka daure mata dashi.
Dauke kallansa yayi daga kanta ahankali tareda miqewa ya dauko magani da alluran Daya dauko daga dakinta a cikin aljihun wandon Daya cire ya dawo ya ajiye kan table tareda dauko wayarsa ya kunnata tareda dawowa office dinsa ya zauna ya Nemo wata number ya Saka Kira Dan aikata abinda yakeson aikatawan.
Har tsakan dare sosai Yana zaune ya kasa Kwanciya bayana zafin zuciya Babu abinda yake fama dashi
Daqyar yaga anyi asuba ya fice Masallacin cikin asibitin.
Yana dawowa daga masallaci sister Ashley yayi text din tazo.
Babu Bata lokaci kuwa sai gata tana zuwa ya umarceta da taje ta kawo wasu uniform din Ameenatou din tazo ta Saka mata sbd na jikinta sun yage sosai.
Bayan tafiyanta kasa barin ta dawo yayi ya shiga bedroom din ya dauko Ameenatou da har lokacin Bata iya ko motsawa ya nufi dakinta da ita a wheelchair da kansa ya turata,
Yayi Hakan ne sbd Babu Wanda yake shigan masa dakin dayasan Yana bacci bayan Mum dinsa sai Siddeeq sai Haroon da ya tafi yabar duniya sai Kuma Ameenatou din da yau ta hau gadonsa.
##MAMUH#
#DR JAMAAL JEEY SEELAH
#MAM SEELAH
#LAMEENU SEELAH
#OMAR SEELAH
#AMEENATOU SEELAH
#ARFAT SEELAH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
69
Koda ya Isa dakin har lokacin block din tsit yake Babu motsin tashin patients sai motsin cleaners kawai,
Sister Ashley na ganin ya kawo Ameenatou din duk ta sake rikicewa da tashin hankalin yanda Akai take office dinsa da wannan lokacin na asuba itama yau din a asibitin ta kwana.
Itace ta gyarawa Ameenatou din gado ya dauketa kaman baby da kansa ya kwantar da ita tareda dago idanuwansa yayiwa sister Ashley kallan day Sakata Neman rikicewa sbd kwarjinsa da kyansa dayake cikawa mutane da yawa ido yace kar ta bar Ameenatou din daga yau zata dawo block din.
Wayarsa ce tayi ringing Dan haka Bai qara magana ba ya bar maganar a taqaice ya juya bayan ya sake maimaitawa sister Ashley din ko paracetamol idan ba shine yace ta Bata ba kar a Kuma Bata komai Daya danganci magani ko allura duka zaiji da komai ayau din.
Juyawa yayi ya fice Yana daga wayan
Sister Ashley tabi bayansa da kallo tana Jin duka jikinta mutuwa Amma Kuma batajin zata iya shiru zataiwa sir siddeeq magana taji matsayin Dr JEEY SEELAH a gurin Ameenatou sbd hankali da dokan aiki harma da sanin iyakar da Allah ya saka tsakanin mace da namijin da ba muharrami ba ta hanata daukan kwanan Ameenatou office din Dr JEEY duk wannan magana CE da babu wanda zai daga bakinta.
Daga Nan kwancen ta zare kayan Ameenatou din ta sake dorata wheelchair ta nufi toilet da ita Tayo mata wanka suka fito ta shiryata tareda Bata tea ta Dan gyara mata gashinta ta zauna tana magana cikin kulawa da kauna tareda lallabawa ta fice tabarta kwance idanuwanta na rufewa bacci me nauyi na daukanta.
Karfe goma na safe Dr Dee ya iso asibitin a gigice sbd mummunan sakon Daya samu Rana tsaka na daukesa da Akai Kai tsaye kwata kwata da asibitin Shima kaman yanda sukaiwa Dr Adams Dan gwara Adams da suka daukesa daga Nan guri me kyau aka turasa shi kuwa wata kaddararriyar asibitin mahaukatanta dataci uwar uban wannan da hauka aka turasa a Wani local government Dake under Lagos din hakama asibitin bama zai kirata da asibitin ba sedai gidan Tara mahaukatan kan hanya Dan kuwa mahaukata gwamnati ke kamawa na kan hanya tana tarasu acan ana Dan dubawa da yawansu tsaban haukansu data baci har kashe nurses sunsha yi da likitoci sai gashi kwatsam baisan ta inda hakan ta faru ba ya wayi gari da wannan mugun ji da mugun ganin.
Gigicen dayake ya Saka kwata kwata baisan ma wa zai fara Kira yaji inda wannan mugun abun ya samesaba Dan haka Kai tsaye yayo asibitin sbd Jin ko akwai lefi ko matsalan da aka samu da sunansa.
Yana isowa Dr JEEY ma shi yabar asibitin zuwa gida Dan hutawa ko kansa zai sake daga nauyi da ciwon dayake masa.
Rashin ganin Dr JEEY ya Saka Dr Dee sake shiga tashin hankali gashi idan yaqi zuwa kaman ya dakatar da aikinsa ne gaba Daya Dan haka yake a cikin tashin hankalin da Bai taba shiga ba a rikice ya Nemo numbern Alh Lameenu seelah Dan samun numbern Dr JEEY din batareda tinanin tin farko ai baima fada masa JEEY din Yana kasar ba.
Dad Lameenu na tareda Mam suna magana a office din Mam din Dake seelahs Kiran Dr Dee ya shigo wayar daddy Lameenu din.
Jin ringing din wayarsa ya Sanyashi juyowa ahankali ya Kalli gefensa datake a ajiye,
Ganin sunan Dr Dee ya sakashi Jin faduwan gaba Amma Bai nuna komaiba ya fuske tareda miqa hannunsa ya katse Kiran Yana cigaba da magana da Mam Wanda yake karanta sakwannin da suka samu na amincewan hadin gwiwan da suka samu daga wani Dan South Africa na aiki dashi na millions of dollars.