AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Bai taba sanin Yaya tudu ko yanayi da fasalin Jin jikin mace yake a jikinsa ba sai yau duk kwata kwata Babu wani abu dayaji Kokuma ya Tantance Yana ji din akan Hakan sbd shi hankalinsa kwata kwata na akan yanda ta cukuikuyesa ne Wanda Sam Sam Baya son Hakan hakama komai zai zo ne Kokuma yazo a bisa abinda baiyi tinanin ko kadan zai yiyu ba Dan kuwa Bai taba tinanin Haroon da tinaninsa suna Nan daram cikin Kai da zuciyarta ba Dan Hakan zai iya samun matsala da kasancewansu tare sbd tinanin shi din Haroon ne hakama Babu wata hanya ko mafita Daya me yiyuwa da zai sakata fahimta ko yadda da ba shi din bane duk duniya idan zata taru kuwa Dan haka take yaji kansa yayi mugun sarawa tareda daukan zafi Dan kuwa Babu ta yadda zaman mata Haroon din.
Sister Ashley datake kallan yanda idanuwansa suka sauya da tinanin dayake ransa batareda tasan Menene ba Amma ta tabbatarda na ‘daci ne ga kayan jikinsa data cukukuye tana sake yamutsasu da qanqamesa tana cigaba da girgiza Kai a kirjinsa batason Jin komai Bata Kuma son komai sai shi din Dan haka duk yanda sister Ashley taso tayi ta kasa cireta karshe Wani numfashi mara sauti ya sauke me dumi a hankali sai a lokacin ya motsa tareda dago hannuwansa duka biyun Yana kokarin kaiwa kanta ya cireta daga jikin nasa Amma Kuma hannuwansa kwata kwata Basa kaunar yin Hakan Dan raayinsa ne mace idan ba patient dinsa bama Baya tabawa hakama sbd baida raayi kwata kwata ko shaawan hulda da mata ko mu’amalantar duk wani abu daya hada da taba jikinsu ya saka bai zabi zama likitan mata ba.
Ameenatou kaman kowace mace ne a gurinsa ta wannan fannin sbd idan ba Dan tana macen da haroon yafi komai so ba kuma ‘ya daya tak jinin Dad Omar dinsa da babu abinda zai saka ko kusantar inda take yayi sbd Raayinsa da kaidarsa.
Akan Bayanta ya Dora hannuwansa ahankali zai janyeta sabuwar Nurse din da aka sauya da sister Ashley ta shigo dakin dauke da maganin Ameenatou din na dare da idanuwanta akansu cikin mamakin Abinda ya tayar da ciwon Ameenatou din,
Cikin yar rikicewa ta Kalli JAMAAL din Daya dago idanuwansa ya kalleta a Dan fizge Yana dauke kallansa tace
“Barka da dare Dr”
Bai amsa ba ya dauke hannuwansa daga jikin Ameenatou din sbd ganin ta nufi gefen gadon dakin ta ajiye maganin hannunta da alluran data shigo dasu ta nufosu tana kiran sunan AMEENATOU din itama.
Idanuwansa akan magani da alluran da nurse din ta ajiye ya kafesu Yana kalla
Wani irin ihun da Ameenatou ne ta zuba ya saka shi dawo da kallansa kanta da sauri sbd karfi da yaji dasuke cireta daga jikinsa.
Ihunta ya Saka Fahat Dake hanyar isowa dakin isowa da sauri tareda wata nurse Dake dakin kusa Dana Ameenatou din.
Suna shigowa dukkaninsu ganin Dr JEEY din a dakin ya Sakasu Dan dakatawa suna kokarin gaidasa Amma hankalinsa Baya kansu Yana kan Ameenatoun dataqi sakinsa tana rikicewa gaba Daya kaman Wanda take kwance tin safe Bata ko iya motsi ba.
Ganin yanda aketa Neman fizge fizge da ita tana kwacewa hakama gaba Daya ta rikice Tama Fi karfinsu sister Ashley din da Basu taba tinanin tanada wannan taurin kan da karfinba Dan kuwa Wani irin riqone tayi masa Daya Saka bottoms na gaban rigarsa fara fizgewa suna zubewa qasa sbd ana janta taqi sakinsa hakama gaba Daya ta haukace musu.
Ganin faffadan kirjin Dr JEEY din dayake fari tas Babu ko alaman irin gashin kirjin Nan ma ya fara bayyana har zuwa gurin cikinsa dayake murde da wasu irin lafiyayyun Abs dinsa da zallan geamin ya budasa ya Saka Nurse Fahat qarasowa da sauri tareda dayar Nurse din suka nufosu
Yana isowa baiyi wata wata ba ya miqa hannuwansa kanta zai kamota ya cirota bakinsa na ambatar sunanta cikin sautin Daya sarkesa batareda ya shirya ba sbd hannunsa dayaji an rike Kai tsaye batareda kalman komaiba.
Dagowa yayi da sauri ya Kalli hannunsa da aka riqe basai ya dagoba ganin baturen hannun dayake riqe da nasa ya sakashi sanin komai Dan haka Saiya hadiye Wani yawu tareda kokarin waskewa Yana ja da Baya kadan Yana kasa kallan Dr JEEY din Wanda yake masa kallan qyama da mamakin da nufinsa Kai hannuwansa zaiyi jikinta ya cirota.
Su sister Ashley ma kokarin sanyi jikinsu yakeyi da ganin Hakan suka fara kokarin rage fizgota sedai Kuma a cikin borin idanuwan Ameenatou din suka sauka kan Fahat take ta fasa ihu jikinta na daukan rawa take ta qarasa rikicewa gabaki dayanta tana fizge fizge tana qarasa yaqa rigan Dr JEEY din gaba Daya
Take dukkaninsu hankalinsu ya tashi harda shi fahat din Bai tsaya komaiba ya fara kokarin janyo gadonta su dorata Akai a daure Yana warware belt din Dake nade,
Hakan ya qarasa tado haukanta gaba Daya tafara ihu tana Wani irin fizgewa zuwa lokacin ma ta sakesa gaba Daya haukan takeyi sosai.
Cikin kankanin lokaci nurses suka Karu a dakin take aka kira Dr Dee Wanda take ya Bada umarnin kafin ya iso a daureta a gadon gashinan tafe.
Jin Hakan Nurses suka Saka Wani irin karfin Dayafi nata tana cikin Wani irin mummunan yanayi suka danneta a gadon Fahat tini ya fara kokarin daureta da belt duk JEEY din na tsaye na kallansu idanuwansa na wata irin sauyawan data Saka dogon hancinsa yin wani irin ja a take.
Rintse idanuwansa yayi ihunta da kukanta da karfinta yafara karewa sbd tsananin tsoro da tashin hankalin abinda tasan za’a yimata a duk lokacinda aka daureta a gadon Wanda ba itaba duk patient aka dauresa a gado suna gane abinda zaayi Wanda azabarta Bata misaltuwa a garesu.
Yanda kukanta ke ratsa kunnuwansa Ya taba zucuyarsa da wani irin dacin Daya sake sauya fuskansa gaba Daya.
Hannun Fahat ya riqe Kai tsaye batareda sun San Daya iso gurin ba Saida suka ga farin hannunsa ya ratsosu ya kama na Fahat din a Karo na biyu.
Dukkanin nurses din gaba dayansu dagowa sukai cikin tashin hankali da sauri suka kallesa sedai Babu Wanda gabansa Bai Fadi ba da mummunan yanayin da suka Gani a fuskansa take sister Ashley tayi saurin sakin Ameenatou din tana Dan matsawa Baya.
Fahat ma sakin belt yayi Yana kallan fuskan JEEY din cikin tsananin mamaki da shakku me girma.
Sauran ma tini suka saketa sedai kafin suyi wani motsin Dr JEEY hannuwansa biyu ya saka ya kamo Ameenatou din gabaki dayanta Yana Riqeta da kyau sbd idanuwanta Dake rintse tana ihu tana fisge fisge cikin ficewa hayyaci.
Zillewa take Neman yi yayi mata wani irin kyakkyawar riqo Yana hanata fizgewan.
Da sauri nurse Fahat ya sake karfin halin motsawa kaman zai matso Amma Bai matso din ba Yana kallan yanda take qarasa yagalgala rigan jikin Dr din da sauri sauri yace
“Dr zata iya Maka rauni haka takeyi ko za’a…..
Katsewa maganarsa tayi sbd Wani fisgan datai ta yakushi lafiyayyar fatan Dr JEEY din me taushi take gurin ya fasa jini ya fito..
Ganin Hakan dukkaninsu suka yo kanta da sauri sedai kafin su iso ta shige jikin JEEY din ta qanqamesa gabaki Daya tana cigaba da kuka me karfi.
Rintse idanuwansa da sukai ja yayi radadin yakushin da sanyin tafin hannuwanta data zagaye jikinsa da Babu kayan sbd rigarsa data koma labari dasu suna ratsasa lokaci Daya.
Hakan ne ya sake rikita nurses din cikin tashin hankalin wannan Barnar suka fara kokarin Kiran Dr Dee a waya.
Sai alokacin Dr JEEY din ya Bude bakinsa da muryansa datake a shaqe ya dakatar dasu tareda cewa kowa ya tafi sister Ashley kawai ta tsaya zaiji da komai cikin nutsuwa.