AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Tana fitowa siddeeq ta hango tareda Ashley Suna fira da dariya da sakewa Arfat na jikinsa Yana Jin kaman zai hadiyesa yayi masa wata siyayyar rashin lissafi sbd mahaukatan kudin daya zubar na turarukan Arfat din.
Juyowa sukai Suna kallanta fuskarta a matiqar hade hakama a Dan rikice duk da ta boye hakan.
Siddeeq kan JAMAAL dayake tafe bayanta ya Maida Idanuwansa Yana kallan yanda yake Shima a kame Babu abinda ya damesa.
Suna isowa ko gaisawa Bata tsaya tayi da Siddeeq ba ta wuce Batama jisa Yana magana ba.
Murmushi Mai aji kawai Jamaal din ya sake Yana kallan Arfat cikeda wata irin Azababbiyar kauna take ya ware masa hannu Arfat din kuwa yazo da gudu ya fada jikinsa ya daukesa yayi sama dashi siddeeq kuwa ya ringa musu hoto.
Ashley ma Cikin kauna da kulawa suka sake gaisawa Suna yiwa Arfat wasa kaman zasu hadiyesa dukkaninsu su ukun.
Sanin tana Cikin rabuwar tinani hade da bacin Rai ya Saka ya Kalli Ashley bayan yabi inda Am din tabi da Mayen kallo me nutsuwa da tsafta yace tayi driving da kanta karta bari am din tayi.
Cikin sakewa tace Dr ka tabamun Baby kenan naga fushin ya dawo Kuma.
Murmushi kawai yayi Yana sake kallan kofar fita Yana cewa
“Babyn naki ce yanzu batason Jamaal Haroon inaga Arfat kadai takeso yanzu”
Dariya siddeeq yai Yana kallan boss din nasa.
Har mota siddeeq ya biyo Ashley da Arfat bayan an zuba uban siyayyar da Akai musu din a baya sai Kuma wata jakar daban da Siddeeq ya miqawa Ashley Yana nuna mata Am din da fuskanta take a matiqar daure da Ido alaman daga Jeey ne ya juya ya Basu guri Ashley ta Saka am fitowa suka sauya mazauni ita ta tada motar taja suka bar gurin.
Har suka isa Babu me magana sai Arfat dayake cakuda am din da zancen handsome Dr Jamaal Yanata fada mata Yana sonsa yace Kuma zai ringa zuwa Yana ganinsa sun zama buddies.
Saida sukai parking am ta juyo ta Kalli Ashley tanason magana Amma ta kasa Dan haka Ashley ta sake murmushi me hade da dariya tana cewa
“Karki damu Babu maganar komai Dana fada masa a yanzu din gameda Arfat.”
Ajiyan zuciya ta sauke tareda sake murmushn dole tana cewa thank you.
Ciki suka nufo su Sarrah suka fito suka dauko kayan suka shigar musu dasu har sama.
Hutawa sukai sukai wanka sukai sallan magrib da ake kira kafin Ashley ta sauko zuwa kitchen duba aikin da Sarrah tace tazo ta duba idan komai yayi sbd Didi Bata Nan.
Tana isa kitchen din Cikin girmamawa masu Aikin sukai mata barka da zuwa tana Dan dubawa Sarrah aikin datakeyi tace ta duba mata.
Am Bata sauko ba sai datai ishai ta sauko sauko sanye da Riga da wanko masu Dan Fadi kadan da kauri sedai yanda sukaiwa jikinta kyau kaman baby Kuma iri daya Dana Arfat sedai nata blue nasa white kafafunta slippers ne farare masu Dan Fadi ko hula Babu a kanta ta sauko tana waya da p.a dinta Dake mata Wani bayanin tafiyar aikin data kamata zuwa Macau next week.
Kai tsaye dining room take kokarin nufa sbd kowa na can ita kadaice Bata kan table Dan haka tana saukowa ta nufi can tana kashe wayarta.
ARFAT tini yayi gaba da gudu Yana ambatar grandpa da karfi ya wuce.
Daidai isowanta tsakiyar palon kafin ta nufi hanyar dakin cin abincin Shikuma Yana Sako Kai a palon sanye Cikin hoodie Sartorios Dark blue hannuwansa sanye Cikin duka aljihun wandonsa ya qaro Wani irin haske da nutsuwa tareda kyau a tafiyar,
Hutun gaske yayi bawai business kadai ba Saida kansa ya sake gabaki daya ya dawo a yau din da safe.
Qamshinsa kadai ta shaqa tasan Yana gurin ta juyo da sauri sbd Bata yadda da hakan ba ta dauka hancinta ne kadai sedai tana juyowa sukai Ido biyu dashi Yana tsaye a bayanta sbd ganinta ya sakashi dakatawa Yana kallanta sbd yanda kayan jikinta suka maidata kaman wata sweet16.
Tana ganinsa tayi saurin dauke Kai tana juyowa tareda yin gaba zata wuce da sauri sedai taku biyu yayi ya riqo hannunta Cikin nutsuwa tareda dawowa baya da ita ya hade bayanta da kirjinsa Yana Kai bakinsa kunnenta yace
“Meyasa kika juyo??
Kallan kofar dining room data shigowa tayi da sauri tana kokarin kwacewa kada babbah ya shigo ya Dan Yana ganinta zai iya kamuwa da paralyze.
Qin sakinta yayi Yana zagayeta da hannunsa daya dayan Kuma ya shafi wuyanta Cikin nutsuwa Yana cewa
“Uhmm?
Meyasa kika juyo?
Banza tai masa tana sake son kwacewa.
Bakinta ta Bude zatai magana yasan baqar magana zata fada masa Dan haka yakai bakinsa yayi kissing bayan wuyanta tareda sakinta Yana wucewa gaba kaman ba shine yayi hakan ba a natse Cikin kamewa da class ya Saka Kai dining room din Yana Dan sake fuska tareda sallama da muryansa me Dadi da class.
Mum dinsa dasuke tare ta dakata ganinsu a hakan itama shigowa tayi palon tana kallan Am fuskanta cikeda tsananin farin Ciki da kauna me tsanani tana cewa
“Heyy my love Yaya kike?
Kasa motsawa Ameeenatou tayi sbd mamakin daga inda Mum din ta fito sbd idan har tare suke da Jamaal din taga abinda ya mata kenan.
Kasa dagowa tayi ta Kalli Dr Aleena din Cikin girmamawa da radadin zucin abinda ya mata ta Bude Baki ta gaidata tareda mata sannu da zuwa Suna wucewa dining room din a tare.
Suna shiga ya dago mayun Idanuwansa ya zuba mata itada Mum dinsa Yana kallan mata biyu dayafi so fiyeda komai a rayuwarsa Dan zai iya bada rayuwarsa akansu.
Zaune yake gefen Dad dinta sbd Dad dinne da kansa ya buqaci ya zauna kusa dashi sbd yai kewansa sosai tafiyar Nan da yayi Kuma baiyi communicating da kowaba.
Ganin Dr Aleena Dad ya sake sakin fuskansa sosai farin Cikin ganinsu itada da Jamaal din na qaruwar masa.
Itama farin Cikin ne ya cika ta na ganin Hadda Arfat Yana table din.
AM kuwa gefen Ashley ta silala ta zauna tana kallan wayarta da Sako ya shigo ta Bude batareda tasan numbern ba tana budewa abinda tagani a Cikin text dinne ya sakata Dan dagowa tanason kallansa Amma taqi hakan sbd Dad dinta dayake kusa dashi sbd abinda yake Cikin sakon ya tabbatar mata da waye ya turosa.
Fatmah da tinda ya shigo taji duniyarta ta tsaya ta dago Idanuwanta Dake cikeda azaban sonsa ta zuba masa tana Jin kaman bazata iya daurewa rashinsa ba idan har Bata samesa.
#MAMUH#
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
123
*_UMMU FARUQ GRAPHICS_*
shin kun daɗe kuna neman inda za’ayi muku haɗaɗɗun designs na businesses ɗinku?
to albishirinku nesa tazo kusa domin kuwa mu a UMMUH FARUQ GRAPHICS mun ƙware a designs kala-kala kamarsu;
(AI CREATION WANDA KUKAFI SANIDA IMAGE LOGO,NORMAL LOGO,3D MOCKUP, FLYERS,BANER,STICKER,ADVERT VIDEOS,BUSINESS CARD,BOOK COVER, DA DAI SAURANSU.haka zalika kuma masu shirin biki ba’a barku a baya ba mun tanadar muku da haɗaɗɗun INVITATION CARDS,INVITATION VIDEO,SAVE THE DATE, also BIRTHDAY CARDS,BIRTHDAY VIDEOS,POSTER,CALENDAR,CERTIFICATE,e.t.c duk munayi akan farashi mai sauƙi da rahusa in shaa Allah
just DM me
@09035390383
for your beautiful designs.
*********
Kasa sake karanta text din tayi ta ajiye wayar kan kafafunta tana dagowa ta Kalli Ashley da itama ita ta kalla sbd ganin ta kalleta.
Dan basarwa tayi tana fara kokarin fara cin abincin Wani sakon ya sake shigowa wayarta taqi daukar wayar ta duba Sabin zai iya yiyuwa daga garesa ne Dan haka abincinta tafara Cikin nutsuwa tana Dan kokarin sakewa Cikin yaqe tana Dan amsa Mum idan ta jeho nata tambaya.