AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Sakin Ameenatou din yayi ya dakatar da nurse Fahat din daga ficewa ya nufosa sedai duk takunsa daga Isa garesa qamshin qaruwan masa a hanci yakeyi.
Nurse Fahat da Shima yake a matiqar tsarge sbd qamshin dayake tashi a jikin nasa na Ameenatou din Daya rasa wane turaren ne wannan sabo sister Ashley tayi mata amfani dashi ayau Daya kasa barin jikinsa Kuma har uniform ya sauya da sauri shine dalilin dadewansa Bai iso na Amma har lokacin tafukan hannuwansa da jikinsa qamshin yake tayarwa sosai.
A daidai lokacin da Dr JEEY din ya iso gaban Fahat din zuciyarsa ta gama cika da wata irin wutar zafin da Baya buqatan qarin bayani sbd qamshin dayake tashi sosai a jikin Fahat din su sister Ashley ma dukkaninsu tsayawa sukai suna kallan abinda zai faru din Dan kallo Daya zakaiwa Dr JEEY kaga yayi Wani ja duk farinsa ya koma ja kaman Wanda aka ajiye cikin Rana.
“Meya kawoka bangaren patients da dare?
Meye abinda ya Sakaka zuwa Nan dakin???
Wannan tambayar ya Saka kowa dawo da kallansa kan Fahat da sauri musamman sister Ashley data Kalli kayansa tasan ba sune a jikinsa ba koda suka Hadu dashi zasu taho dakin Yana cewa bara ya dauko allura da maganinta ya biyosu.
Sisters din biyu ma kusan a take suka lura da Hakan Dan Koda suka gansa a yanzu yanzun Nan fararen kayansu ne a jikinsa Amma a yanzu ya sauyo zuwa green Wanda suke sakawa idan zasuwa patients wanka da sauransu.
Rikicewa Fahat din yayi Yana kallan Jamaal din yace
“Dr JEEY,ni Kuma?
Ban taba zuwa……..
Qarar Marin Daya saukan masa ne ya Saka su sister Ashley firgicewa suna ja da Baya cikin tashin hankali.
Fahat dinma daukewa jinsa yayi harma da lafiyar ganinsa Dan wasu taurari yaga suna masa yawo ya dago da sauri ya Kalli Dr JEEY din Wanda ya sake jeho masa tambayar meya kawosa Nan din.
Ihun da Ameenatou keyi tana yaga kayan jikinta da jikin nata ma ya Saka sister Ashley rungumeta da sauri jikinta itama Yana rawa Dan shock din da suke kokarin samun kansu a ciki da abinda yake Neman tabbata.
Wayar Dake aljihunsa ya fidda Kai tsaye Kira daya yayiwa siddeeq Dake jiran Kiran ya kashe Yana qin kallan fahat din dake gaban nasa hannuwansa wata irin rawa sukeyi a boye sbd jinin jikinsa Dake kunar dayake Jin idan baiyi karfin halin riqe kansa ba zai iya aikata kisa a gurin.
Nurses da sauran duk Wanda yake dakin ficewa yayi sedai ko gama ficewa basuyiba siddeeq ya iso asibitin tareda team din da zasu Basu tabbacin komai tukuna ya nunawa Fahat din jinin MAM SEELAH ne ke yawo a jikinsa shugaban Ashalawa na yanzu gaba dayanta.
Ameenatou data kasa tsayuwa ta dawo daidai Siddeeq ya juyo batareda ya kalleta ba sbd yanayin jikinta da kayanta dasuka fara yagewa yace sister Ashley ta fita da ita tukuna.
Manyan asibitin da sauran doctors Dake cikin asibitin cikin Daren tini suka iso Babu Bata lokaci aka dauki tprint din jikin kofar dakin Da rigarta da akace sister Ashley ta kawo tini ta cirota ta bawa siddeeq ya kawo dayake ana cewa ta fita da ita tsoron Kaita Wani dakin tayi sbd yanayin datake cikin sai Kai tsaye ta nufi office din Dr JEEY din da ita Siddeeq ya Bude mata suka shige ya rufe.
##MAMUH
#SEELAHS
#DR JAMAAL MAM SEELAH
#AMEENATOU OMAR JADEN SEELAH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
72
Fahat kuwa tini tashin hankalinsa da balain dayake Gani na tonuwan asirinsa ya saka shi Neman haukacewan shima dan haka Babu wani sauki ko tausayi a idanuwan JEEY d suka gama rufewa Yana ganin yafara haukan ya Saka aka kawo masa Alluran da Dr Dee yake sakawa yana Ameenatou idan ciwonta ya tashi take yayi masa ita Shima.
Wannan aikin tin kafin zuwan likitocinsu da sauran manyan asibitin yayisa Dan haka Koda suka iso Fahat tini yake kwance Yana Wani juyi Yana ihu da buga Kai a qasa Yana yagar jikinsa.
Hankali tashe aka daukesa Akai dakin duba patients dinsu dashi sbd Babu Bata lokaci Dr JEEY ya sanar dasu da alama Daman yanada tabin hankali sbd an kamasa da laifin shiga dakin son haiqewa patient haukansa ya tashi.
Yana fadan Hakan ya juya ya wucewansa sbd Yana buqatan Fahat din a cikin asibitin Dan sanin waye yake son kashe Ameenatoun ta hanyar Banka mata alluran da kisheta zasuyi Kai tsaye bawai iya juyar da Kai ba Dan yanda akeyinsu abin ya wuce tinanin me tinani Dan haka bazai so miqasa yanzu ga sojojin da zasu kakkarya masa duka wata gaban Dake jikinsa Saiya gama dandana masa azaban da duka Ameenatou tasha dan duka lissafin yawan alluran dake cikin file da Akai mata Saiya masa adadinsu Dan yasan daga yau dayayi masa ta farko koma patient a asibitin Shima labarin nurse ya Kau tukuna.
Acan dakin kuwa doctors da Basu San allura ce akaiwa Fahat din ba hauka yakeyi tuburan sbd jininsa nada karfi shiyasa ma Bai sume ba yake buge bugen Daya Saka kayan dakin fara fashewa take hankalinsu ya sake tashi Dan tini yayiwa Dr Zakeer rauni dole Nurses dinsu Maza hudu suka Saka karfi aka dauresa a gado da belt cikin sauri aka dauko allura Aka lafta masa akan Wadda take jikinsa wannan Karan take ya sume sbd a cikin qasa da awa Daya an masa allura biyu duk karfin jini bazai dauka ba.
Siddeeq da ma’aikatan da aka kawo tini suka fice da thprint din,
Siddeeq Bai sanar da JAMAAL din Ameenatou na office dinsa ba ya wuce,
Shi kuwa kwata kwata Bai nemanta ba sbd sanin tana gurin sister Ashley Dan ganinta zai iya Saka jinin babansa Dake yawo a jikinsa yaci galaba akansa ya illata Fahat din gaba Daya musamman da tsoro ya saka Fahat din fadan wai kaddara ce ta Sakasa zuwa…. adaidai lokacin ne ya banka masa Alluran wadda da sama da goma ne a gabansa zai iya banka masa su duka.
Kai tsaye office din ya nufa lokacin karfe kusan uku da mintina koina tsit Babu motsin komai Dana kowa kaman Babu abinda ya faru duk da suna can dakin da ake komai suna fama da fahat din.
Sister Ashley ta samu Ameenatou din ta sassuto batareda alluran komaiba ta Dena ihun da haukan tayi shiru a kwance Babu kuzari ko kadan a aikinta ga sanyin AC din office din Daya gama kama koina sai Kuma Taga kaman sanyin zai mata yawa sbd Babu Riga a jikinta sai black halfvest me laushi da sirkin Roba data ke Dan kame da kirjinta tinda ta zare rigar jikinta ta bayar.
Rasa abin rufa mata tayi gashi Babu ta yanda ma zata Kalli ko kofan shiga dakinsa Dake cikin gurin bare ta shiga harma Kuma ta dauko Wani abin Dan haka dole ta miqe tareda zare Ameenatou din daga jikinta ahankali ta kwantar da ita ta Dan tafiya samo abin rufeta.
Tana ficewa Ameenatou din ta sake dunqulewa guri Daya sbd baccin Daya dauketa din,
Dakin Ameenatou din ta nufa sedai kusan Babu kowa koina tsit kaman baayi komaiba.
Wata Rigan ta dauko mata ta juyo tareda rufe dakin ta zare key dinsa da baa cirewa kowanne daki key dinsa na daga waje jikin kofan maqale ta waje ake rufesu baa barin key ciki su rufe kansu a rasa tayaya zaa budesu.
Ba komai ya Sakata rufe dakin ba Dan kada Wanda ya shiga ya Gano Ameenatou din Bata dakin Dan haka ta wuce da key din zuwa office dinsa takai mata Riga.
Basu Hadu a zuwa ba Dan hanyar databi daban da Wanda ya bi sai a komawan tana dosar office ta hangesa Yana gap da Isa Shima office din Shima Dan haka ta dakata cak daga inda take batareda ta qara taku ko Dayaba tana tinanin ta isa takai din kokuwa ta juya tinda ya riga ya isa ta tabbatarda bazai taba barinta kwana babu riga jikinta ba ga wannan sanyin hakama kwata kwata Ameenatou din Bata Wani son sanyi Dan haka ko ya barta ba kayan bazata taba barinsa bacci ba.