AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Kallan Dr Dee Dr Zakeer yayi Kai tsaye ya sanar dashi sabon babban likitansu kenan daga Poland Wanda zaiyi aiki dasu na Yan watanni Yana hada Wani research ne akan PSYCH yana gamawa zai tafiyansa.
DR JAMAAL MAM SEELAH Wanda aka Fi sani da Dr JEEY SEELAH.
Kallan JEEY din Dr Dee yayi da Dan sauri gabansa na faduwa Yana Kuma boye tashin hankalinsa da tinanin dayake Neman shiga ya sake fuska sosai cikin sake bayyanarda girmamawansa ya sake gaisawa da JEEY din Wanda baida Wani bayani me tsayi da zaiyi bayan yi musu sallama suka fito gabaki dayansu tareda sanar dasu gobe zaiyi reporting yafara aiki.
Sosai su Dr Zakeer da sauran manyan harma da MD din asibitin da suka iso suka bayyanarda farin cikinsu da Jin dadin samun Daman aiki da babban kwararran likita kamansa duk da kusan ba qwarensa kadai ne abinda yasaka ake girmamasa ba da kiyaye masa sanin su waye SEELAHs ne,
Sunan SEELAHs nada Wani irin girma da matsayi na girmamawa da kiyayewa sbd tarin arzikinsu da power da suke da ita me karfi.
Dr Dee yafi kowa shiga rawan jiki da rikicewa lokaci Daya Amma Babu Wanda ya gane Hakan ko Lura sbd kwarewansa a iya mu’amalantar Jamaa dan haka zubawa Jamaal idanuwansa yayi Yana son Tantance bature ne ko bahaushe Dan Nigeria Kuma da gaske shine JAMAAL ‘dan Mam Seelah tak Daya rage Wanda idan ya fahimta daidai kusan shi da mahaifinsa ne ko sunansu Alh Lameenu Baya kaunar a ambata idan suna tare sbd kada ko a wasa sunansu ya Hadu da sanin alaqan Dake tsakaninsu dashi bare Ameenatou.
Siddeeq ne ya Bude masa kofar gefen zaman banza na gaba ya qaraso a natse ya shige Yana Ciro wayarsa ya Saka Kiran wata number Yana shigewa motan da kansa ya rufe Siddeeq ya zagaya ya shige ya tayar da motan Wanda su Dr Zakeer ke bi da idanuwansu Har lokacin iskan Bata koma musu daidai ba da sauran qamshinsa Daya bar musu.
Sister Ashley Dake jiran fitowan sir siddeeq akan maganar sauyin gurinta batama San sun fito ba sedai motar data hanga tana ficewa harabar asibitin tasu me tsawon katangar da baka ganin waje tabi motan da idanuwanta da suka sauya sbd tashin hankali da damuwan rashin madafa Dan kulawa da Ameenatou kaman Wani sabon aikine me albashi me tsoka da Bata kaunar rasawa ko kadan Dan haka duk ta shiga damuwa hakama har cikin ranta Allah ya Saka mata kaunar Ameenatou din Dan haka hankalinta be kwanta ba da yanda ciwonta yake tashi da dare dole akwai abinda yake faruwa a block din datake son sani Dan haka kwata kwata batada nutsuwan barin Ameenatou a daidai wannan lokacin.
Daga asibiti kuwa Kai tsaye Masaukin JEEY din suka nufa Wanda yake a Houston Astrt Victoria Island kafin ma a qarasa Isa estate din nasu na Houston Astrt suke guda hudu a guri daya masu shegen tsaro da securities hakama kowanne gida kusan yanada nasa securityn na musamman hakama ba hayaniya sam a gidajen dan dabam dbam ne nasu JEEY din sune na marasa yara daga me shi shikadai se me mata su kadai akwai Wanda na masu yara ko family da yawa ne dabam.
Tin wancan zuwan nasa ya Siya gidan Amma Baima shiga ba aka samu tashe tashen hankalin da yabar qasan Kuma ko yanzu Bai dawo da niyar zaman ba ya dawo ne sbd Tafiya da Ameenatou kota halin Yaya so tinda sun kasa samun sallaman tafiya da ita Dan haka dole Yana buqatan Aiki a cikin asibitin na Dan lokaci Dan samun Daman dawo da ita daidai Dan su samu sallaman tafiya da ita sbd duk yanda zaiyi kafin yazo a sallametan su tafi Abin ya gagara sbd kanta ya juye sosai hakama shi kansa yanada hanyoyin amfani dasu ya tafi da itan idan yaso Amma Kuma a yanzu da abin yayi tsanani haka dole Saiya nutsu ya karanci yanda ake treating nata tareda alluran datake Kai da magani yasan girman matsalan da nisanta yanda yana tafiya zasusan ta inda zasu fara tinda tako ina sallaman taqi samuwa.
Parking Siddeeq yayi a lafiyayyar haraban gidansu dake zagaye ko a cikin estate din ya juyo ya kalli JEEY din da har lokacin fuskansa baa sake take ba sbd abubuwan da ya sun zafafa kansa ciki hadda rashin sanin inda hafiz da baida lafiya ya iya daukan Babbah ya tafi dashi sbd shi kansa Hafiz din yasan dole Baya iya tafiya a daidai tinda kariya nawa ce a jikinsa Amma ace siddeeq din Bai sanar dashi komai yanda ya kamata ba sai yanzu dayayi zuwan da Babu Shiri.
Numfashi ya sauke ahankali kafin ya Bude Baki bayan ya Dan juyo ya kalli siddeeq din a natse da sauti mara karaji yace,
“Babu Wanda zai San Ina qasar kota Yaya,
Duk abinda zaisaka asan Ina qasan a toshe sa tukuna ba yanzu zan dawo ba.”
Gyada Kai siddeeq yayi Yana cewa
“Babu matsala duka na gama da wannan”
Gyada Kai yayi tareda Bude motan ya zira kafafunsa ya fice ya nufi kofa.
Password na Bude kofan ya saka ya Bude ya shige lafiyayyar palon da Akai tsarinta daidai da yanda siddeeq yasan Yana gudanar da rayuwarsa hakama koina an gyareda tsaf da safen kafin saukansa Dan Bai sanar dashi Yana hanyar tahowaba Saida ya shiga jirgi ya sanar masa Kuma ya kashe wayan dan haka Babu Bata lokaci gari na wayewa kafin ya iso da safen nan aka gyara koina tareda yin shopping na dukkanin abubuwan buqatansa Daya San dole dasu yake amfani.
Sanyin AC ne ya gama gauraye palon da qamshin turarensa Daya Hadu dana humidifiers da burners da suka gama aiki tinda safen duk da Bai fiya son irin wainnan qamshin ba.
Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya shige Yana kashe wayarsa Dan Yana sauka Bai wani huta ba suka wuce yaga Wanda zai Gani akan case din asibitin daga can ya wuce asibitin Dan haka yanzu hutawa yake buqata kansa ya sake kafin yasan ta inda zai Saka a fara Nemo masa su Babbah.
Yana shigewa Kai tsaye wayarsa ya ajiye ya nufi closet ya zare kayan jikinsa ya jefa a laundry ya janyo towel daga inda towels dinsa suke a jere ya daura a qugunsa ya shige toilet.
Siddeeq na shigowa Kai tsaye kitchen ya nufa ya zauna energy drinks din da aka kawo tin kafin isowan JEEY din a fridge tareda ruwa masu yawa kafin ya fito sbd Cook din Daya iso ya basa Daman shiga kitchen bayan ya gabatar masa da komai ya fito ya fice Dan Shima gidansa Dake kusa zai tafi ya huta kafin lokacin gama abincin yayi Kuma yasan JEEY dinma a yanzu hutawan zaiyi Baya buqatan kowa.
Wanka ya fito qamshin Liquid soap din his majesty Yana tashi daga jikinsa fatansa sai daukan ido takeyi kaman ta lafiyayyan mace.
Baya zama gaban mirror sedai ya tsaya Dan haka daga tsayen ya goge jikinsa da towel ya shafa lotion na his majesty din sai body splash me sanyin gaske.
Underwear kawai ya Saka sai armless transparent freesize ya Dora jallabiya Akai yayi Sallah Yana idarwa ya zare jallabiyan ya haye lafiyayyar gadonsa dataji wasu tsaddadun beddings ya kwanta bayan ya kashe hasken dakin.
Ya manta raban Daya samu Daman kwantawa yayi baccin Hutu kawai sai yau din duk da Baya cikin nutsuwan zuciya Amma dai ya kwanta din Dan samun sakewan Kai harma da zuciya.
Karfe uku cook ya gama girka komai daidai irin girke girken da Jamaal din ze iya ci daidai Dana can qasar sbd bayani da siddeeq Daya masa na kalan cimar JAMAAL din.
A dining ya jere komai tareda cutlerys da komai harma da cups duk Saida ya ajiye komai kafin ya tafi saikuma gobe.
Yana fita Bai wuce ba a gurin securities ya Jira Saida siddeeq ya taho bayan la’asar shirye cikin qananun kaya marasa tsayi sai qamshi yakeyi Shima me sanyi sbd yar nutsuwan Daya samu ta dawowan Mai gidan nasa ya miqa masa id card na shigowa kullum batareda an dakatar dashi ba ya wuce shikuma ya qarasa yayi parking.