AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Dadah tinda Taga basuda ranar komawa zama ne shikenan Dan haka dole ta sake jikinta ta karbi rayuwar hannu bibbiyu Dan Babbah tini ya ware ya zama lafiyayyan dattijon da Hutu da Arziki yake ratsawan,

Hakama ganin ‘yayanta Ameenatou da Hafiz sun samu rayuwar datake musu fatan samu ta wadataccen ilimin da Jin dadi tareda arziki tini taji ha kalinta ya qara Kwanciya dan haka batada wani aiki saina hutu da hutu itama saikuma na rigima da qiriniyar ARFAT.

Arfat lafiyayyan yaro ne Daya taso da karfinsa Da Dan jikinsa bulbul Babu wani nakasa ko ciwon komai a tattare dashi bayan na mura dayake yi wasu lokutan musamman idan ya shiga Rana ya Dan yi ko awa Daya haka a ciki to jikinsa Bata dauka take zai fara ciwo da rashin lafiya,

Da farko sunji tsoron yanda Allah yayi SA bature sosai Dan kuwa kusan kullum sake zama bature yakeyi sbd yanayin haskensa Daya zarce na Momma dinsa sosai hakama gashin kansa sosai yake gashi me santsi shiyas baa Wani bari Akai Akai Uncle Hafiz dinsa yake masa aski,

Ta bangare Daya Kuma idanuwansa da suke Wani irin kala dasu kaman blue kaman green sune suke bawa Dad omar shakka da tsoro sbd idanuwansa koyaushe kama suke masa da idanuwan daya sani amma ya kasa tina na waye.

Su kuwa su Babbah ko kamanninsa basa son tsayawa tantancewa sbd a zahirance Babu amfani ko buqatan Hakan tinda dai sune suke Haifa abunsu,
A gabansu Ameenatou ta haifar musu shi Dan haka Babu zancen sauya musu Akai Arfat dinsu koyayane kamanninsa sonsa a jininsu yake.

A cikin shekaru ukun Nan komai na rayuwarsu Babu Wanda bai canza ba,
Cimarsu, rayuwarsu, yanayin jiki da halittarsu harma da halayya sbd ita rayuwan Hutu,Jin dadi Kwanciyar hankali da daula tareda ilimi da wayewa ta dabance Dan haka Babu Wanda sauya me girma Bai samu ba a rayuwarsa.

Hafiz ya bude sosai geamin da tsananin hutun Daya ratsashi da ilimi,yayi haskenda zaka dauka shi kansa halfcst ne dan haka kallo daya bazaka gane shi din bane.

***********
Qarasa saukowa tayi daga saman tana kokarin nufar dining room Dadah ce t fito daga hanyar lafiyayyar kitchen dinsu da Babu abinda Babu na buqata hannunta dauke da tray me dauke da transparent bowl na glass an yanko fruits an zuba condensed milk da Madaran gari sosai Akai ta Kalli Ameenatoun fuskanta a sake da kulawa sosai tace

“Zaki fita ne batareda kinyi breakfast ba??

Ajiye handbag din hannunta tayi tana cewa

“No, Dadah Ina sauri ne 10 zan shiga exams yanzu Kuma is after 9 Ina buqatan Isa da wuri,
Ina Babbah ya tashi kuwa?

Wucewa Dadah tayi ta Isa dining ta ajiye tray din hannunta tana cewa

“Zo zauna kiyi breakfast din dai kafin ko fita banasan fitarnan batareda kinci komaiba,gashinan duk cikinki ya shafe sbd rashin cin abinci yanda ya kamata”

Murmushin Jin dadi tayi tana rungume dadahn ta Baya tana cewa

“Dadanah yau ni kikeji Dani kenan?”

Itama dadan murmushi tayi tana janyota daga bayan nata ta zaunar da ita akan dining tana cewa

“Idan na Dena ji da ‘yata naji da waye??

“Hmmm Dadah ai Kinsani ni yanzu duk Kunje Kun Raba mun soyayyana da kukemin Kun bawa ARFAT har nashi Yana son fin nawa ma,
Ni Babbah ma fushi zan fara dashi”

Maids ne guda biyu suka shigo dining din kowanne Yana Turo kayan breakfast da aka shiryo.

Suna isowa ta farkon ce ta fara Dan kallan Ameenatou cikin girmamawa tace

“Good morning lady AM”

Dan juyowa tayi tareda amsawa a natse tana kallan abincin da suke jerawa kafin dayar itama ta gaidata suka gama jere komai suka juya.

Qamshin Hafiz ne ya cike gurin dadah ta dago tana cewa

“Bara naje dai naji da Angona kafin ku gama tinda ga Hafiz Nan,
Kaima ta tabbatarda kayi breakfast din kafin ka fita.”

Daukan tray dinta data ajiye farko tayi ta wuce zuwa sama inda Ameenatou ta sauko.

Dago fararen idanuwanta tayi ta Kalli Hafiz lokacinda ya qaraso gurin ya ja kujera ya zauna ya ajiye wayoyin Dake hannunsa guda biyu gefensa ya dago Shima ya kalleta Yana cewa

“Yaya dai,
Ina Champ dina?
Haryanxu Bai tashi bane banjisa ba time na school ma Ya wuce fa.”

Hanyar sama ta kalla kafin tace

“Yaya Hafiz ko gaisawa bamuyiba fa,
Yana can Yana rigima yau da ita ya tashi Sam shi bazashi school ba sai Dad ya Kaisa da kansa Kuma ka sani Dad Baya qasar bansan ya zan masa ba ga Dadah can ta tafi Kila su daidaito.”

Sam sama Yaya Hafiz din yayi breakfast dinsa da bama Wani abin kirki yaci ba ya miqe ya nufi saman Kai tsaye zuwa dakin ARFAT din Dan yasan Yana can.

Yana Isa ya miqa hannunsa ya Bude kofar dakin Ya shiga Yana cewa

“Where’s my boy??”

ARFAT din Dake tsaye sanye da bvlgari underweyna Yara me shegiyar tsada gabaki Daya jikinsa kaman babyn da Bai taba fita Rana ta tabasa ba haskensa koyaushe qaruwa yakeyi,

Kaya Dadah zata Saka masa ta basa fruits dinsa Amma Yana Jinsa ya kwace da gudu ya Isa gurinsa bakinsa a washe da farin ciki Yana cewa

“Uncle Buddy”

Daukesa Hafiz yayi yai sama dashi Yana cewa

“Waye ne ya taba mun my boy?”

Dadin maganar yaji ya juyo ya Kalli Dadah Yana dariya fararen qananun hakoransa na bayyana kafin ya juyo ya Kalli Hafiz din yace

“My Mommah and granny D”

Kallan Dadah Hafiz yayi Yana qarasawa ya karbi kayansa a hannun Dadah ya ajiyesa kan gado tsaye tafara saka masa Yana cewa

“Dadah kune kuka tabamun yaro keda yarinyarki gashinan yayi fushi yaqi zuwa school,”

Ko kulasa Dadah batai ba ta Kalli Sarrah Nanny din Arfat din wadda ita iya aikinta a gidan na kulawa da Arfat da duk abinda ya shafeta Koda slippers dinsa ne kuwa.

Tana tsaye yaqi yadda ta Saka masa kayansa gashi lallabasa akeyi baa masa Wani dole Mommah dinsa da Dadah ne kadai a gidan suke masa fada da masa dole Amma kowa Baya takurasa Baya laifi ko kadan a agurinsu.

“Sarah jeki kici gaba da aikinki”

“Ok ma” tafada tareda juyawa tafara gyara dakin da Babu ma Wani gyaran komai a cikinsa gashi da girma da kayan Yara irin na buqata da wasan Maza masu tsada da kyau a tsare kaman dakin shine na sarkin mansion din gaba Daya”
##MAMUH
#AM JDEN
#THE JDENS
#THE SEELAHS
#ARFAT OMAR JDEN

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
100

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected