AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Wani irin mannuwan gaske me karfi kirjinta yayi da nasa Wanda ya Sakasa loosing balance ba zato yayi Baya ya saka hannunsa daya da sauri ya dage gaban mirror din gurin kayan da suke Kai suka zube qasa sbd mugun dafan mirror din dayayi idanuwansa na sake rinewa daga washewan da basu gama yi ba,

Hannunsa Daya ne ya dafe kansa Dan kasa riqe kansa da yayi daga tsayuwa Dayan kuwa zagaye yake da ita sbd Bata kariya daga faduwan da suka kusa yi.

Hakan ne ya sake bawa kirjinta mannuwan fiyeda farko da nasa hakama har lokacin Bata motsaba tana zagaye dashi batada niyar sakinsa sai numfashinta me dumi dayake saukan masa a gefen wuyan Daya Sakasa rintse idanuwansa ya budesu batareda ya iya kallanta ba Dan sanyi yaji take Yana shigarsa kamanma zaiyi rawan sanyi yakeji.

Wata ajiyan zuciya me sanyi ta sauke ta kukan datasha,

Dumin ajiyan zuciyan tata Kai tsaye cikin wuyansa da kunnensa ya sauka take yaji balance dinsa na sake gazawa da sauri ya miqe tsaye da kyau Yana son cireta daga jikinsa gaba Daya Dan ya saka ko rigarsa ne.

Qin sakinsa tayi saima dagowa datai da kanta ahankali cikin sanyi da rashin kuzari sosai ta zuba masa idanuwanta da sukai laushi tana sauke numfashi ahankali ahankali Wanda yake shigar masa Kai tsaye cikin nasa hancin tareda qamshinsa da har lokacin yake jikinta Wanda ya gauraye da nata qamshin me sanyi.

Qin kallan fuskanta yayi sbd Jin Yana Neman rasa numfashinsa Dan haka da sauri ya sake cireta wannan Karan kuka ta fasa masa mara karfi me sanyi da rashin karfi tana juyawa cikin kuka ta nufi kofan dakin ta fice ta nufi kofan ficewa office din tana Kiran sunan sister Ashley da karfi.

Ganin kofan ficewa ta nufa ya Sakasa rintse idanuwansa da sukai ja ya budesu Yana Jin tsikar jikinsa suna tashi Bai tsaya Saka Rigan ba yabi bayanta Koda ya isa tanata dukan kofan da karfi tana Kiran sunan sister Ashley.

Hannuwanta biyu ya kamo Yana janyota sedai gaba Daya taqi sauraronsa tama rikice ihu tafara tana cewa sister Ashley kawai takeso.

Girgizata yayi da sauri Yana cewa tayi shiru da muryansa da yayi nauyi sedai batama Jinsa.

Jikin nasa datake so ya janyota ya rungume ahankali Yana Jin tsikan jikinsa suna sake miqewa,

Turesa tayi tana sake rikicewa batasonsa sister Ashley takeso,
Sister Ashley kawai zata gurinta,

Daukanta yayi gabaki dayanta kaman ba budurwa ba ya juya dakin da ita sbd ihunta karya tada mutane.

Suna shiga dakin ya zaunar da ita bakin gado zaiyi durqusa yayi mata magana ta miqe tana buga masa haukan Daya sakasa rintse idanuwansa dan ya rasa Yama zaiyi mata ya dakatar da ihu da Kiran sunan sister Ashley din.

Hannuwanta ya sake riqowa zai ambaci sunanta ta fizge tana sake rikice masa.

Dafe kansa yayi dayaji Yana Neman daukan zafi ya rintse ido ya Bude idanuwansa suka sauka akan vest dinta data fara zamewa daga kirjinta Dan hannun Daya tini ya zame Dayan ne kadai ya rage,

Da sauri ya dauke idanuwansa akan jikinta Yana kallan fuskanta da duk ta rikita kanta ta rikitasa.

Hannunta ya kamo ta sake bugewa ta nufi kofa ta fice zuwa office dinsa ihunta na qaruwa…

Ko taku uku batai ba daga tsakiyar office din ya dauketa cak da hannuwansa biyu ya Dorata kan table din office din Kai tsaye ta Bude Baki zata ci gaba da ihun ya dago jajayen idanuwansa ya Kalli cikin tsakiyan nata idanuwan kafin ya gangaro da jajayen idanuwan ya Kalli bakinta Dake ihun Kiran sunan Ashley…

Rintse idanuwansa yayi ya sake budesu acikin idanuwanta da wata irin sauti a shaqe mara karfi ya Bude Baki ya ambaci complete sunanta

“AMEENATOU”

“Ameenatou,pls”

Sunanta daya ambata yaso tasiri akanta Amma Kuma sosai tayi fushi Ashley kawai takeso Dan haka takai tafin hannuwanta biyu ta Dora a tsakiyan kirjinsa Dake Bude zata turasa Amma Hakan ya gagara sbd hannunsa Daya Dora ya riqe nata duka biyun dan dakatar da ita daga qarasa hade fatansa da fatan tafin hannunta.

Saukowa tayi da karfi tana sake nufar kofar sedai hakurinsa ya qare da ihun da rashin sanin yanda zai rarrasheta Bai tsaya komaiba ya dawo da ita kan table din Yana zaunar da ita ba zato ya ranqwafo ya hade fuskansa da nata hancinsu na gogan na juna,

Numfashinsa ne yake shiga hancinta tareda fitinanniyar qamshinsa tareda jikinsa da yayi mata rumfa dashi gaba Daya ya Saka kasa ci gaba da ihun jikinta na mutuwa hakama dumin numfashinsa da tafin hannuwansa Dake tallafe da fuskanta suka Sakata dago idanuwanta Dake jiqe da Hawaye ta zuba masa shikuma a lokacin rufe idanuwansa yayi Dan Bai taba sanin qamshinsa nada daukan hankali ba sai a yanzu dayakejinsa Yana fita daga jikinta Yana shigarsa Kai tsaye.

Hannunsa Daya yakai batareda ya janye ba ya Dora akan sirrin hannun rigarta Daya zame yafara janza ahankali yana mayar mata dashi daidai har Saida ya Maidasa kafin ya Bude idanuwansa ya Kalli idanuwanta da shi suke kalla.

Shiru dukkaninsu sukai ahakan numfashin junansu na shigarsu kafin ta Bude Baki ahankali zata kira sunan sister Ashley lips dinta suka shafi nasa sbd motsawan da sukai…..

A jeme ya dago jajayen idanuwansa ya Dora akan lips dinta da suke sake furta sunan Ashley suna shafan nasa….

Table din dasuke Kai ya damqe da hannunsa Daya Yana dauke Dayan daga riganta Daya gyara idanuwansa har lokacin kan fuskarta.

Wani irin zafin jiki yana taso masa Dan haka ya janye daga gareta da sauri Yana daukanta gaba dayanta ya nufi dakin da ita.

Gadonsa ya nufa ya kwantar da ita batareda ya sake kallanta ba ya juya ya shige toilet.

Yana shiga ruwa ya zubawa fuskansa tsawon mintina kafin ya fito ya goge fuskansa da jikinsa da wani towel din qarami kafin ya dauko wata rigar ya Saka Dan wancan tana yashe ne qasa Babu kalan takawan da basuyi mata ba sbd rikicin Ameenatou din.

Ficewa yayi daga bedroom din har lokacin Bai sake kallan inda take ba ya koma office ya zauna tareda dafe kansa da yayi nauyi.

Tinda ya kwantar da ita Yana shigewa toilet Bacci ya dauketa Daman baccin Takeji rigimar ce ta hanata baccin Dan haka tinda ya kashe mata jiki da numfashinsa rigimarta ta tafi Yana kwantar da ita baccin ya dauketa.

Ta jima da bacci Yana office din zaune idanuwansa a rintse Yana jiran kansa ya sake can sama sama kunnuwansa suka ringa jiyo masa maganarta.

Bude idanuwansa yayi tareda miqewa a natse ya nufi dakin ya shigo Yana kallanta.

Bacci takeyi a dunqule guri Daya ta qanqame jikinta tana magana ahankali ahankali.

Tsayuwa yayi tareda zuba mata ido yanda bakinta ke furta sunan dayake Jinsa har zuciyarsa wato “HAROON”.

Numfashi da ajiyan zuciya me sanyi mara sauti ya sauke ahankali kafin ya Tako a natse ya iso bakin gadon ya zauna tareda Jan duvet ahankali ya rufeta Yana gyara mata kanta Daya sauka daga pillow.

Saukan hannunsa akanta Daya gyara ya Sakata firgita sosai ta tashi a firgice zatai yunqurin tashi sbd Fahat Daya Riga ya Sabar mata da ana tabata cikin dare take firgita da ihu Dan haka Yana ganin irin firgitan datai ya kamota Yana Bata Daman ganin fuskansa
Da sauri ta ambaci sunan Haroon tana fadawa jikinsa ta qanqame tana sauke ajiyan zuciya ahankali tareda komawa baccinta a jikinsa.

Dole yanaji Yana Gani yabarta jikinsa taci gaba da baccin sbd zareta jikinsa zai iya tado rigimarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected