AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ta jima sosai a jiki bayan su brush da wanka da sauransu kafin ta fito daure da towel brown.

Tana fitowa binta da kallo Ashely tayi cikeda kauna da burgewa tana Tina lokacinda take mata wanka kaman Babynta kaman yanda take fada shiyasa ko a yanzu ta Saba my baby ko my princess take kiranta.

Itama tashi tayi ta nufo toilet din ta shige Dan wankan.

Ameeenatou kuwa gaban dresser ta tsaya bayan ta goge jikinta tukun ta dauko Mai Tai shafa sama sama me qamshi da rashin maiqo sosai.

Turarukanta ta shafa ba sosai ba ta Saka Riga da wando masu Fadi da kauri na B&P tukuna ta dauko wayarta t duba al-qiblah ta Dora rigar sallah a kanta Mai hade da qaramar veil tayi Rolling ta tayarda sallolin dayake kansu tafara.

Koda Ashley ta fito ta gama harta zare kayan sallan ta daga bedroom din tana zaune lafiyayyan luxury palon dakin nasu tana waya hannunta daya riqesa cup din Cappuccino tana Sha hankalinta kwance hutunta ya bayyana.

Da Dad dinta take wayar wanda suka jima sunayi kafin aka basa Ashley itama suka gaisa tukuna sukai sallama.

Babbah ta kira wanda Shima yake matse dayaji daga gareta.

Shima wayar suka ringa Yi sun dade kafin sukai sallama.

Hafiz ne Shima Wanda yake tareda Arfat nan suka shiririce Suna waya sun Dade kafin sukai sallama.

Sallan dhuhur da lokacinta yayi sukai kafin suka kashe hasken koina suka kwanta baccin hutawa.

Sai yamma sosai suka Farka.
Wani wankan suka sake Yi da sallan laasar data wuce sosai.

Suna gamawa Babu jimawa Akai magrib Saida sukayi tukuna sukai ordern abinci wanda kusan duka snacks ne sai pasta sauce with tomato sbd Ita kanta Am Bata son abincinsu sbd Chinese ne yawancinsu
bare Ashley da daman haryanzu Bata Wani cin ire iren abincin Nan ko acan Nigeria dinma
Sbd haryanzu cimarta daban take ko a mansion dinsu.

Snacks da Milkshake Ashley taci sosai ita Kuma am din pasta tace da warm milk ta koshi daganan akazo aka tattara gurin sukuma sai alokacin suka zauna Suna Dan kallo sama sama am tana Aiki a laptop wanda emails ne datake jira suka shigo na meeting din gobe da zasuyi.

Dayake yawanci irin luxury hotels dake hade da casino resorts daddare shine tamkar ranarsu sbd a Lokacin ne kowa ke fitowa Yasha iska yayi rayuwar Jin Dadi da hutawansa Amma da Rana Kam kowa Yana dakinsa basa fitowa Cikin Rana idan ba Wani aikin zaka tafi ba kokuma daman Wani aikin ya kawoka Dan haka a Lokacin ne koina yake sake shaawa Yana zama lively duk da bangaren dakunan tsit yake ko waya me qara baayi,hutawa Kawai da rashin hayaniya hakama cameras koina.

Ashley balcony din dakinsu dayake a tsare da Wasu irin kyakkyawan couches da pillows da table kaman Wani lafiyayyan palon hutawan palace ta nufa ta zauna tana kallan fadin Macau da galaxy din tana chatting dinta hankali kwance tana cin red apples masu girma.

Am tana gama duba emails dinta rufe laptop din tayi ta ajiye ta nufi bedroom ta zare kayan jikinta ta saka kayan bacci masu kauri Riga da wando ta Saka tareda socks me taushi ta haye gado qamshinta me Sanyi na fita ta shige bargo take bacci ya dauketa.

Ashley sai dare sosai bayan tagama hutawanta tukuna tazo tayi brush itama tayi Shirin bacci ta kwanta gefen Am din tana shigewa bargon tareda rufe Idanuwanta.

Washe gari sai guraren 10 AM ta tashi wanka Kai tsaye tayi ta fito ta shirya Cikin fararen Emporio Armanis ladies suits da suka zauna jikinta cif tayi Rollin kanta da dark Ash Versace silk veil sai handbag dinta ta tomford da wasu shegun jimmy choo heel.

Zazzafan Ginger tea Tasha da pancakes guda biyu ta jefa mint a bakinta ta tsotse tukuna ta fito James ne yazo har dakinsu ya jirata ta fito suka wuce inda mota ke jiransu a qasa.

Jakar laptop dinta James ya karban mata ya hada da tasa ya rige Shima Cikin suit din Prada masu tsadan gaske.

Suna saukowa Kai tsaye mota suka fada aka ja suka bar galaxy din zuwa inda zasuyi Taron meeting din.

Ashley Suna fita Bata tashiba ita sai kusan dhuhur tana tashi brush da wanka tayi ta fito daure da towel ta shirya Cikin skinny jeans da sweater designer ta Dora jacket a sama ta fito a restaurant dinsu tayi lunch dinta hankalinta kwance tana wayoyinta har sai laasar ta koma sama tana zuwa sallah tayi ta saura kaya daga sweater zuwa normal shirt sbd ita ba sosai take Jin sanyin ba.

Am Bata dawo ba sai gab da magrib Dan haka a gajiye ta iso wanka da sallah kawai tayi taci abinci ta kwanta bacci a matiqar gajiye.

Ashley ma sai dare sosai ta kwanta sbd tafara Jin dadin kasar hankalinta kwance take Jin nutsuwa da hutun na shigarta.

Washe gari ma haka ta fita Bata dawo ba sai dare ma Dan haka still batada lokacin fira ko hutawa bayan bacci sbd gajiyan gaske take debowa.

Haka tafara yawon meetings da abinda ya kawosu Babu Hutu kullum sai dare take dawowa harta Kai wata yar rama tayi sbd rashin Hutu
Saida ta koma tana bawa Ashley tausayi Dan haka idan ta dawo ta kwanta Cikin kulawa da kauna me tsanani tareda tausayawa Ashely ke mata massaging kafafunta da bayanta sbd ta samu bacci me Dadi Kuma hakan Yana taimaka mata sosai gurin ta Dan sake sakewa.

Kwanaki 8 ta share tana wannan wahalan kafin suka samu Saar abinda ya kawosu proposal dinsu ya samu karbuwa ya shiga Cikin kamfanin da suke son zuba hannuwan jarinsu.

Farin Ciki ne Mai tsananin gaske ya cika dukkaninsu harda su Dad ba qaramin farin Cikin hakan ya shigaba sbd takai matsayin dayakeson takai din Dan itace duka ta jagoranci komai a taqaice itace ta hada proposal din da komai da bayanin Dan haka suke cikin farin Ciki.

Babbah ma sadaka ya ringa Yi da kudi masu yawa Yana godewa Allah yar budurwansa ta Kai inda suke fatan takai din.

Mum Nur ma kiranta tayi ta tayata murna Cikin tsananin kauna da kulawa hakama Didi ta kirata.

Uncle Ahmed ma albarka ya ringa Saka mata Yana tsokanarta tana dariya Cikin farin Cikin kasancewansa Uncle dinta.

Dr Aleena ma ta kirata sedai Cikin Jin nauyi da rashin sakewa suka gaisa ta mata barka ta masa da godiya sukai sallama.

Hafiz ma Saida ya gama tsokanarta da kunnata kafin ya mata barka Yana Saka mata albarka taji Idanuwanta sun ciko da hawaye a duk lokacinda hafiz ya Saka mata albarka Yaya Abdul ne yake fado mata sbd shine me wannan halin na komai tayi sai ya Saka mata albarka kaman Wani babba a Lokacin.

Duk da sun samu aikin ba yanzu zasu koma ba sai anyi Taron Saka hannu da miqa hannuwan jarin tareda sauran manyan billionaires da suke qasar suma sunyi joining Dan haka Hutu zatayi na musamman kafin lokacin sbd zaayi kusan kwana 7 kafin lokacin.

A daidai wannan lokacin ne Abubuwan da suka faru a Nigeria na rasuwar su lameenu suka faru batareda sun sani ba Dan haka hankali kwance ta fara Hutu Bata fita koina koyaushe tana daki daga cin lafiyayyan abinci sai hutawa da sallah sai bacci.

Ashley kuwa tini ta fadan fara fita ita Kam sbd tafara gane kan gurin fita takeyi ta shaqata musamman da James ma ya fara yawon shakatawa take ta biye masa suke fitansu suje yawo su kashe kudi kaman basusan zafinsu ba su dawo.

A Cikin kwanaki kalilan ta samu hutun ya ratsata gajiyarta duk ta sake har Wani fresh ta sake sbd Bata taba fita ba tinda suka gama aikin koyaushe tana daki Rana Bata hau jikinta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected