AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Zuba mata idanuwa Fatmah tayi tin data doso palon koyaushe kyanta kaman qaruwa yakeyi,a yanzu zata iya cewa bayan rape da ‘dan gaban fatiha da AM din ta Haifa to Babu Wani Abu data rasa a rayuwanta sai kuma mijin aure Dan kuwa ko zata hakura da komai akan AM bazata iya dannewa ba tana kallo ta Dad Omar ya hadata da Wani Billionaire ta aura ba abarta Dan zata iya fadawa duniya AM jden nada ‘dan rape data Haifa mara uba.

Ita ma kyakkyawa ce Kuma fara hakama Babu abinda ta rasa sbd Dad Omar baya wasa da sake mata kudin duk abinda takeso a rayuwanta Amma damuwanta finta da AM din tayi a komai.

Fatmah dince a Palo zaune tareda Mum Nur da Hafiz dan haka kowa da tsananin kauna da kulawa yake kallanta tareda farin Cikin kasancewanta a cikinsu Amma Fatmah Kuma radadi ne me qunar zuciya take kallanta dashi har AM din ta iso
Ita tafara kalla Cikin sakewa ba damuwan komai tace

“Fatmah barka da gida,dazu bamu gaisaba Koda na dawo kaman bakya Nan ma ko?

Numfashi ta sake a boye tareda Dan sake fuska kadan tana cewa

“Eh,Ina Nan Amma Ina daki Ina bacci ne,
Barka da dawowa,ya Madrid?

“Fine Alhmdllh” ta fada tana isa gurin Mum Nur tana zaunawa gefenta tareda Dan shagwabewa tana cewa

“Mum amaryan Dad”

Dariya Mum din tayi tana cewa

“Rabb ya shirya AM”

Kafin su qara wata magana su dadah sun dawo Dan haka Bata tsaya komaiba ta miqe ta fice zuwa bangarensu tana iso babbah daya matsu yaga yarsa Shima tini ya kamo hanyar nasu bangaren a kofan palonsa suka hade tana ganinsa Idanuwanta suka ciko da kwalla tana rungumesa shi da dadah lokaci daya atare hawayen na saukowa tace

“Nayi kewanku babbah,
Dadah bazan iya sake dadewa Wani gurin ba tareda ku ba,wlh nayi kewanku.”

Kaman baby haka ta ringa musu hawaye Saida aka suka zauna Suna aikin rarrashinta babbah kaman zai fasa kukan Shima haka ya ringa rarrashinta yanajin radadin kewanta da yai Shima sbd a rayuwarsu idan ba da tsautsayin daya rabasu ba Shima sbd Baya hayyacinsa kwance Cikin Ciwo itama bata hayyacinta Basu taba rayuwa ba juna ba sai wannan karan.

Hafiz ne daya shigo yaga yanda su babban suke rarrashinta kaman yarinya qarama irin yanda suka Saba mata tin tana yarinya ya Saka shi hade fuska Yana cewa

“Meye hakan to??
Ke wai bazakiwa kanki fada bane kisan kin girma qatuwa Dake kin zauna kina hawaye ana rarrashinki.”

Harara babbah ya dago ya watsa masa kafin yace

“Meye naka a Ciki malam,inace mune masu rarrashin ba Kai ba ko?
Karna sake Jin kalman qatuwa a bakinka Ina tayi Wani girman data wuce rarrashi daga iyayenta tinda ba duniya ta haifeba,
Ko ta tsufa Kai indai Ina Raye saina rarrashi abata.”

Dadah dai Batama ce komaiba tissue ta Zara tana gogewa AM din fuska tana cewa

“Kinga Arfat Nan Yana kallanki Yana dariya da mamakin mommansa na Kuka ana share mata hawaye Dena ya isa hakan tinda gashi ai kin dawo din.”

Sai a lokacin ta dago ta harari Yaya Hafiz din kafin ta Kalli Arfat dayake mamaki da dariya yace

“Kaka Babbah Mommah na Kuka kana share mata hawaye kaida Granny dadah haka takeyi tin tana baby Irina itama??
Gashinan Uncle ya fada.”

Dariya Hafiz ya sake shida Arfat din lokaci daya Yana cewa

“Haka mommanka take koyaushe rigima, shagwaba,Kuka,tayita sakawa su dadah na sakani aikinta fa.”

“Really uncle??

“Yes Son,haka mommanka take,hmmm Nasha wuyanta,
See her face now ko kunya gatanan haryanzu budurwan Babbah”

Dariya Arfat yayi Yana sauraron kuruciyan mommansa wadda ta tashi tana kokarin bin Hafiz din dadah ta riqeta tana cewa

“Kyalesa haka yakeso ki tashi ki nunawa Arfat din abinda yake fada masa Dan haka karki bisu kyalesa”

Babbah Janta yayi har dining inda kafin fitarsu aka jere mata abincin da dadah ta girka musamman sbd ita kawai.

Zaunawa tayi tana ajiye tissue din datake share fuskanta dashi tana kallan Jerin abincin Dake dining din.

Wainna ta Gani taji Wani Dadi na mamaye ta,ta mayar da idonta kan Samosas da Kuma Nigerian JollofRice datake zuba qamshin Nikakken daman dayake cikinta da spices na gargajiya.

Kasa tsayawa kallan sauran abincin tayi tafara Bude plate da daukan cutlery dadah na fara zuba mata.

Rice din tafara ci baifi spoon hudu ba ta ajiye taci wainan dayayi haske sosai ya gasu yayi Saqa kaman Suna Nigeria ne.

Hafiz ma zama yayi bayan ya zaunar da Arfat a kujeran kusa dashi hadda babbah ma zaman yayi sbd suci gaba daya Dan sunyi missing hakan
Saida dadah ta gama zubawa kowa Shikuma Arfat ta zuba masa samosa daya da waina daya ta zuba masa Zuma a gefen wainan tareda zuba masa madaran mamansa da aka dafa mata ta sake masa mixing da Zuman a glass cup ta ajiye masa tana nuna masa yanda zaici wainan sbd baima taba ganinta ba,jollof din Kuma bata zuba masa ba da sauran abincin sbd kwata kwata baisan yaji ba Yanaci zai iya haukace musu sbd abincin sun Dan Yi yaji sbd a gargajiyance yau tayi abincin jamaar gidan ma kusan ba kowa yaci ba sbd Basu Wani iya cin yaji ba Amma uncle Ahmed da Dad Omar sunci wainan sosai sbd Babu wanda a cikinsu zai Tina yaushe yacita last,su Fatmah dasu Mum Nur Kam Basu ci ba har gwara Arry ya gwada ci Amma yajin yai masa yawa ya Saka Zuma yaci sosai da Zuman kaman yanda Aunt Didi itama taci sosai.
##MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
107

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************
Da daddare gurin Dad dinta da Mum Nur tayi dinner tareda su sbd haka take rabawa Dad dinta da su babbah kanta kowa tana tsananin sonsa tana kokarin basa time dinta da kulawanta yanda ya kamata sbd dukkaninsu ta rasa wanda ya fi sonta tsakanin Dad dinta da babbah.

Ko da suka gama dinner tin a Nan dining Arfat yayi bacci Dan haka Sarrah ta kira ta daukesa daga jikin Dad ta nufi sama dashi Dan masa wanka da Shirin bacci.

Itama bata Wani ci sosai ba sbd abincin Rana ya kama cikinsu sosai Dan haka itace ta fara tashi ta tafi har gefen Dad dinta inda yake zaune tai masa goodnight ta juya tayiwa Mum Nur hakama Uncle Ahmed kafin ta wuce tabar gurin sbd Didi batanan Fatmah ma Kuma haryanzu babu Wani shakuwa a tsakaninsu, da Arry ne ta Saba sosai har take wasa da shi sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected