AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Da Kai yake amsawa kawai a natse batareda ya Bude bakiba sai thank you data kama bakinsa Dan ko gaidasa Kai Saiya ce Maka thank you.
Dakin ya iso ya tsaya a natse tareda zare hannuwansa Dake cikin aljihun wandonsa tareda Dan sauke numfashi me sanyi da nutsuwa a boye Dan baisan Menene zai faru ayau din idan ta gansa ba duk da yasan saita sake kwana Daya kafin alluran ya saketa ta dawo daidai.
Sister Ashley ce ta Bude dakin zata fito zuciyarta cikeda tsananin farin ciki da Kwanciyar hankalin samun dawo da itan da Akai block din hakama Siddeeq ya sanar da ita Dr JEEY SEELAH mijin Ameenatou ne da igiyoyin aurensa uku suke kanta batareda ita kanta tasan ba shine Haroon twin dinsa ba daya rasu Dan haka ya sake bata tabbacin kulawa da Ameenatou da kuma tabbatarda ciwon Ameenatou Bai bari ko Bada hanya ko Daya da zata bayyanarwa da kowa wannan sirrin hakama a yanxu da jeey din yake nan ta ninka kulawan datake wa Ameenatoun sbd inshallah suna Saka ran sauki da lafiyanta zasu iya dawowa kowanne lokaci sbd daga yanzu Babu me qara yi mata kowace irin alluran.
Wannan maganar ta Saka zuciyar sister Ashley wankewa daga dukkanin damuwa akan Ameenatou tareda Jin farin ciki me tsananin gaske harma da fara tinanin daga Nan zuwa wata Daya da alluran keyi ta warware daga jikinka gaba Daya Ameenatou zata iya dawowa daidai idan har ba sake mata alluran akaiba gashi siddeeq ya bata tabbacin bazaa sake mata Hakan ba,
Ko siddeeq din Bai fada ba a yanzu da Dr JEEY yake asibitin a matsayin kaman sabon shugaba Dan labarin tafiyar Dr Dee yagama yaduwa tasan Babu abinda zai sake Ameenatou dinta inshallah.
Cak tayi saurin dakatawa tareda Dan komawa Baya a natse sbd batai tinanin da tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacin ba a kofan dakin Amma Tino shi waye din ya sakata sauke numfashi a boye cikin girmamawa tace
“Barka da zuwa Dr”
Qamshinsa ne ya cike mata iskan kofan dakin Yana kutsawa cikin dakin tareda faduwa ko Ina cikin sanyi da nutsuwa sanyin ke shiga har hancin Ameenatou din Dake kwance idanuwanta a rufe Amma ba baccin takeyi ba.
Da tattausan muryansa me nutsuwa ya amsa da “yawwa,thank you”
Shigowa dakin yayi Yana Maida hannuwansa aljihun wandonsa idanuwansa akan inda Ameenatou din take kwance shiru cikin wasu cotton Riga da wandon bacci marasa nauyi kalan blue me haske.
Ahankali ta Bude idanuwanta ta zuba masa su gabaki dayansu suna Wani irin narkewa da cikowa da Hawaye masu sanyi da suka gangaro mata gefen fuska a hankali sbd azaban datake Ji a zuciyarta na cinta da jininta na rashin kuzarin zuwa garesa.
Sister Ashley sanyi jikinta yayi idanuwanta itama na cikowa da Hawaye masu sanyin tausayin Ameenatou din Dan kuwa a cikin idanuwanta daga ita har shi JEEY din suna iya hango tsagwaron zallan so da tsananin kaunar datake masa a matsayin Haroon batareda tasan Haroon dinma gaba daya baya duniyarba ya tafi inda har abada idan ba a mafarki ba bazasu taba sake haduwa ba.
Sister Ashley Bata taba sanin mara hankali na iya son Abu da gasken gaske kauna mara sirki me karfin gaske irin Hakan ba,
Da cikin cikakkiyar kuzarinta take tabbas tasan Babu abinda zai hanata nufar Dr JEEY din ta kasa rabuwa dashi Dan Haka ciwo da radadin Hakan yake bayyane a fuskanta suna kallo sedai Babu yanda zatai mata Dan kuwa Alamu sun nuna Ameenatou din ba lallai ta samu kwatankwacin son da Haroon yayi mata daga Dr JEEY din ba,
Sunkuyar da Kai sister Ashley tayi batareda ta Kalli kallan da Dr JEEY din kewa Ameenatou ba batareda ya qyafta ko idanuwansa ba Dan kuwa ayau fuskan Dad Omar dinsa yake kallo a baby face dinta tareda fuskan Haroon duk a lokaci Daya hakama innocence dinta na hanasa Tantance da kamannin wa zai kalleta a cikinsu.
Shiru dakin yayi itama Ameenatou din har lokacin idanuwanta dasuke a lausashe akansa suke ga bacci na cinta Amma ta kasa rufe idanuwanta sbd kada ta rufe ya tafi ya barta.
Sister Ashley data lura da Hakan ta qaraso ahankali ta ranqwafo ta Dora hannunta akan lallausan fatan fuskanta ta shafa a hankali tana Ambatar sunanta da cewa
“My sweet girl zatayi bacci ko??
Ahankali cikin wahalallen karfin hali ta tilastawa jikinta motsawa ta girgiza Kai so Daya har lokacin idanuwanta na kansa wasu hawayen na gangaro mata.
Daga shi har sister Ashley sun San ba qaramin karfin hali da azaba ta daure Tasha ba gurin tilastawa jikinta motsawan sbd sanin azaba da karfin alluran Dan haka sister Ashley tayi saurin tsayar mata da Kai tana share mata hawayenta da tissue cikeda kulawa da tausayawa tace
“Kinason Dr kada ya tafi right??
Lumshe idanuwansa dake sake tsiyayo Hawaye tayi tana kallansa zuciyarta na narkewa.
Lumshe idanuwansa da suka sauya yayi Yana dauke kallansa daga fuskanta dayake ganin mutanen Nan biyu a ciki ya Tako a hankali ya iso har bakin gadon Yana rasa abinda zai fada,
Sister Ashley na ganin Hakan ta silale gefe tana Satan kallansa sai daukan ido yakeyi komai nasa class ne dashi hatta shirunshi Wani iri dashi.
Hannunta dayane yake motsawa ahankali alaman son take ta motsa bayan Hakan bame yiyuwan bane,
Saukan hannunsa ahankali kan nata din ya Saka sister Ashley sake ajiyan zuciya me sanyi a boye sbd tinda ya shigo din hawayen Ameenatou ya Sakata Jin kaman ta janyosa takai gaban Ameenatou din ta Dora hannunta akanta ko yarinyar zata Jin sanyi.
Ita kanta Ameenatou din idanuwanta ta rufe a hankali tareda budesu akan fuskansa daya kallanta cikin murya mara sauti sosai ya Bude Baki yace
“An Bata dinner??
Matsowa sister Ashley tayi tana kallan Ameenatou din tace
“Tasha tea Wanda idan tana cikin wannan alluran dole iya tea dinne yake shiga tinda bakin bazata iya budesa ba bare hadiyewa da kyau”
“Any damuwa?fever or something??
Girgiza Kai sister Ashley tayi tana cewa
“No,sedai ciwonta da daddare Yana tashi sosai fiyeda yanda ka Gani jiyan wasu lokutan Kuma dai Bata Hakan sai tsakan dare” ta qarasa maganar tana gudun fadan abinda Bata tabbatar ba.
Akwai sauran bayani a maganarta idan yaji qarashen sautin daidai Dan haka ya dago zai juyo ga mamakinsa da nata hannunsa Dake kan na Ameenatou din ta riqe na yatsinta biyu cikin kuzari.
Kasa juyowa yayi sbd idanuwansa da suka Dan rage budewa ya Kalli sister Ashley data dauke kallanta kan hannun nasu yace
“Akwai abinda kike tinanin Yana kawo Hakan?
Menene yake Saka ciwon nata tashi Kai tsaye?
Dagowa tayi ta kallesa kadan tana cewa
“Bata taba yadda kowa ya rabeta ko ya kusanto gurinta idan ba ni ba sai Sir siddeeq sai doctors wainda Suma duk suka taho sai ciwon ya tashi,
Bata taba yadda da kusancin kowa ba Hakan shine ke tayar da ciwonta sosai kum……
Idanuwansa Daya dago ya zuba mata gaba Daya ya Sakata kasa qarasa maganar.
“Akwai Wanda yake zuwa ne dayake Saka ciwon tashi cikin dare?
Akwai staff Da aka taba bawa Daman kwana a cikin patients ne
A can baya tana Hakan?
Tana firgita ne cikin baccin dayake tayar da ciwon?
Ina buqatan amsa Daya Kai tsaye game da Hakan.”
Rikicewa sister Ashley ke Neman yi da maganarsa Dan tasan illan fadan abinda Bata tabbatar ba musamman a asibiti Dan zai iya kawo babban matsala da zata iya kawo illa me girma ga likitoci da kaf ma’aikatan Dake cikin asibitin Dan haka ta dago zatai magana Amma kallan dayake cikin idanuwansa ya Sakata Neman rikicewa tace