AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Dan haka tayaya zai bari Ashley da itace kadai ce ma a bangarensa yakejin tana yiwa AM so da kaunar da Babu sirki,
Duk mewa am wannan son bazai taba barin ya bar hannunsa.

Suma akwai wanda yake jiransu shi suka dauka suka wuce gidan Kai tsaye ya kaisu har kofar gidan,

Suna parking JAMAAL ya rintse Idanuwansa ahankali zuciyarsa sanyi me nutsuwa hakama siddeeq ajiyan zuciya ya sauke a bayyane Suna fatan Allah yasa Ashley dinsu ce da suke Nema ba wata ba.

Sallaman Abiola Siddeeq yayi akan ya jirasu bakin layin zasu taho idan sun gama.

Siddeeq dinne ya fara Bude motar ya fito hakama Jamaal Bai jira Abiola Dake kokarin Bude masa ya Buden ba ya fito.

Sister Ashley Dake zaune inda su Dad Omar suka barta ta zubawa cheques din dasuka bar mata gabanta Idanuwanta sunyi jajir kukane tayi Mai tsananin Ciwo da radadin gaske sbd Bata taba dauka tsananin kaunar datakewa Ameeenatou ba zata zama ta abinda zaa biyata da kudi ace tabar qasarta sbd hakan,

A yanda take Jin Ameeenatou kaman ita jininta ce,
Kaunar Ameeenatou da Jamaal a jininta suke sbd bazata taba iya yin abinda zai cutatar dasu ba Amma Kuma a yanzu an dorata akan zabin cutatar da daya tabar daya…

Idan har ta zabi tafiya Dan bawa Ameeenatou da Babynta kariya to tabbas ta cutatar da Jamaal wanda tasan a duk inda yake nemanta yakeyi,
Hakama idan ta zabi zaman zata Saka Ameeenatou da baby hadari.

Wani Sabon kukan Mai ratsa zuciya mara sauti ta sake sbd rayuwarta gabaki daya ta hargitse ta juye ta koma abar tausayi,
Bata kowa Bata komai,
Iyayensu sun rasu daga mamarsu har baban,yayyunta kuwa kowa ba baya abeokuta din kowa da inda yake rayuwarsa Babu ruwan Wani da Wani Dan kusan shekaru biyu kenan ma ko dayansu Bata sake Gani ba a wayar ma basa kiranta sbd addininsu da ba daya ba Dan haryanzu taqi riddah ta koma christian din dasuke mata barazanan idan Bata komaba ma kasheta zasuyi Dan gwara su San Bata Raye.

Batasan Ina zata Saka rayuwarta ba gashi yanzu qasar akeson ta bari ta bacewa kowa taje rayuwa a inda batada kowa batasan komaiba.

Tafin hannuwanta ta rufe fuskanta dasu lokacinda Wani sabon Kuka Mai radadi ya taho mata tana Jin inama itama ta mutu tabi Abdulra’uf da duka sun huta da wannan rashin madafar.

Buga kofar gidan Akai ta dago jajayen Idanuwanta da har suka fara kumbura sbd itama fara ce sosai sbd asalinsu Igbos ne.

Kasa motsawa tayi ta rintse Idanuwanta hawayenta na sake qaruwa.

Siddeeq daya kasa hakuri sake buga kofar yayi tareda shigowa sbd kofar a Bude take ya Bude bakinsa muryansa a natse yace

“Hello”

Dago jajayen Idanuwanta tayi Cikin farban data shigeta me karfi ta Kalli kofar tsakar gidan daga Dan sitting room din datake zaune zuciyarta Cikin tashin hankali ta furta “SIDDEEQ”

JAMAAL ne daya Sako Kai a bayansa qamshinsa ya bayyana a tsakar gidan Dan qarami wanda ya sakata miqewa tsaye qafafunta na rawa sbd muryan Siddeeq da kunnuwanta suka dauko mata da Kuma qamshin da tafi kowa sanin Kona waye sbd shine a jikin Ameeenatou dinta a Koda yaushe tabaro gurinsa.

Takowa tayi a hankali qafafunta na rawa kaman yanda zuciyarta ke rawa ta nufo kofar palon ta miqe hannu ta dauke labulen take numfashinta ya kusa daukewa tayi baya ahankali tareda dauke wuta sbd shock da Wani irin farin da sanyi sbd ganinsu Dan batasan ta yanda zata bar qasar ba batareda taga Jamaal ba zuciyarta takasa nutsuwa da yin hakan ko kadan sbd Jamaal ne nata a kaf ahalin Ameeenatou ita Jamaal tasani shi takeso shi take bi.

Siddeeq ma ajiyan zuciya me karfin gaske ya sauke Idanuwansa na tsayuwa akan Ashley din datake tsayen bakin kofar hawayenta na tsananta gudu Kan fuskarta.

JAMAAL ma Idanuwansa take suka sauya ya zubawa Ashely din Idanuwansa sauyin rayuwarta da quncin datake Ciki a bayyane yake ta koma kaman wata tsohuwar mace sbd baqin Ciki da wahalan rayuwa.

Ahankali siddeeq ya Bude Baki Shima ya ambaci sunanta Cikin baqin Cikin ganin rayuwarta data matu Yana tinkaro palon.

JAMAAL ma Saida ya hadiye abinda yake ji kafin ya Tako ya nufo palon Shima suna shigowa ta kasa riqe kukanta ta fasa shi ahankali tana godewa Allah a Cikin zuciyarta daya kawo mata JAMAAL din a daidai wannan lokacin da batasan tayaya zata iya barin qasar ba saninsaba ta gaya masa Koda yabar Ameeenatou tana dauke d Cikin dasu Dr Ibrahim suka do zubarwa.

JAMAAL da Siddeeq dukkansu sunsan kukan ganinsu ne takeyi da samun sassaucin abinda yake zuciyarta na shekarun sedai Idanuwansu da suka sauka akan cheques din dayake ajiye a taburin robar Dake tsakiyar palon ya sakasu kurawa sunan dayake rubuce baro baro akan cheques din duka biyu Ido siddeeq ya dago ya Kalli JAMAAL Shikuwa Jamaal din Idanuwansa take suka sake sauyawa ya dago ya Kalli Ashley wadda itama cheques din ta kalla hawayenta suka sake gangarowa tana sauke ajiyan zuciya.

Silalewa tayi ta zauna tareda Ciro wayarta Dake inda ta tashi batareda ta iya Bude bakinta ba kawai ta kunna recording komai na maganarda su Dad Omar sukai da ita tin daga lokacinda ya sanar da ita shine mahaifin Ameeenatou ta Saka recording din sbd ajiyewa Jamaal din koman dadewa yaji da kunnansa.

Ahankali maganganun komai ke sauka kunnuwansu shi da Siddeeq tin daga farkon zancen har bayyanar Cikin Ameeenatou da yanda akaso ciresa da Kuma accident dinta da rasa nata babyn datai tin Bata haifesaba Cikin ya bare har zuwa offer din Dad Omar din kafin uncle Ahmed ya Dora da kaman threatening nata sukeyi akan hakan.

Dagowa tayi da jajayen Idanuwanta ta Kalli Jamaal sai alokacin ta iya Bude Baki Cikin rawar murya tace

“Bazan taba iya boye Maka Ameeenatou tabar asibitin tana dauke da cikinka a jikinta ba,.tayi Kuka tayi Ciwo tayi hauka duka akan rashinka daga karshe tin tana asibitin tafara warkewa sbd so da Dama takan zauna da hotonka a hannunta idan na bata a waya ta zuba Maka Ido
Akwai ranar data fadamun date na ranar data fara haduwa d Haroon a ranar nafara sanin tafara dawowa daidai sedai Wani lokacin ta Dan sake juyewa.

A karo na farko da Jamaal ya dago Idanuwansa da sukai Wani mummunan ja ya zubawa Ashely tinda ya sunkuyar da Kai akan abinda Dad Omar yayi masa zuciyarsa na breaking Cikin tsananin Ciwo da zafi me radadin gaske sbd Bai dauka zai taba samun hakan daga uban dayasan radadi da ciwon rabuwa da ‘danka jininka gudan jininka,Jin date din Ashley din ta fada ya sakasa dagowa sbd date dinsa ne na karshe daya bar Nasarawa daga ranar yabar Nigeria gaba daya.

Shi kansa Siddeeq take yasan ba Haroon ne wannan lokacin a nasarawa Jamaal ne Dan haka ya sake tambayar Ashley date din Cikin sauri da shock…

Sake fadan date din tayi jikinta a matiqar sanyaye tana sauke numfashin Kar karshen zancenta gameda komai na Cikin Ameeenatou datakeson sanarwa Jamaal kafin ta juya ta shiga dakinta Babu Bata lokaci ta fito da Wasu takardun data dauke a tareda ita na Cikin Ameeenatou din ta juyewa Jamaal gabansa sbd Yana Cikin alkwarin datai sai ta bawa Jamaal scanning da takardun awon Cikinsa da hannunta.

Bazai iya motsawaba bare iya budewa da kansa sbd Yana Cikin mummunan halin da shi kadai yasan me yakeji a Cikin zuciyarsa Dan haka siddeeq ne ya Bude komai Shima hannuwansa na rawa ya dorawa Jamaal din a hannuwansa Yana kalla.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected