AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Shiru kowa yayi tsit na tsawon mintina kafin md ya Kalli Babbah cikin qarfin halin da kulawa yace

“Duka bayanai gasunan munji Kuma mun fahimta sosai Amma duk da Hakan sbd tabbatarwa da gudun matsala tareda cike doka zamu baka hakuri yanzu ka tafi zuwa Nan Da kwana biyu saika dawo inshallah zamu baka damar ganinta harma fiyeda Hakan idan ka buqata”

Shiru Babbah yayi cikin nazari da tinani kafin ya dago yace

“Ba iya ganinta nazo yi ba,sallama muke so mu tafi da ita gida insha Allah zamu nema saukin daga Allah acan”

Daga md har su Dr Zakeer ajiyan zuciya me karfin gaske suka sauke a boye ta dr ibrahim CE ta fito fili sbd anzo inda yanzu Kam sukeson Azo Dan kuwa Babu Wanda ba tsoro da tashin hankali ne a ransa ba Dan alamun dai suna nunawa da gaske ita yar Jaden din ce tinawa da labaran rasuwar matarsa Da aka ringa yi a lokacin da Akai gobaran.

Wannan masifar da balain ko waye yayiwa yarinyar Nan ciki Allah ya Isa a tsakaninsu,
Dole ma suyi gaggawan binciken komai kafin jibi Babbah yazo su miqa masa yarsa su tafi tin kafin cikin Nan Daya fara fitowa ya bayyana su shiga masifar d batada kofar fita a hannun Omar Seelah.

Cikin girmamawa suka bawa Babbah tabbacin inshallah zuwa Nan da jibi yazo zasu duba su sallametan su basa ita din.

Farin ciki ne me tsananin gaske ya rufesu babban yai godiya sosai suka fito.

Suna ficewa md ya miqe Ya dauko ruwan hannuwansa na Dan rawa yakai bakinsa yasha Yana Jin zafi Tako ina,

Yau da ace sunje zubar da cikin Nan Wani abin ya biyo Baya Yaya kenan zasuyi da seelahs?
Cabdijam,
Jin yayi kwata kwata Babu abinda yakeso yanzu kaman Ameenatou tabar asibitinsu kota halin Yaya ne.

Kusan Suma su Dr Zakeer tinanin ne a ransu Dan haka take aka kira Dr Charles aka sanar dashi komai ya sauya,
Shi kansa Yana Jin Hakan ya ringa godewa Allah da matarsa Bata taba lafiyan Ameenatou din ba dan haka shi tin a cikin Daren ma ya fara tinanin Neman sauyin asibiti kawai Yama barta gaba Daya incase idan gaba tsautsayi yasa zancen ya dawo Baya.

Dr Zakeer ma fara neman yanda zaa sauya masa asibitin yayi Dan hankalinsa Kuma ya tashi akan lamarin,
Bawa Babbah ita shine rufin asirinsu ayanzu to Amma Kuma dawowan Dr JEEY shikuma wani tashin hankalin ne daban duk da kaman yanda md ya fada bai nuna musu yar uwarsa bace koya dawo suma bazasu nuna sun saniba magana Daya iyayenta sunzo an sallameta.

Cikin farin ciki su Babbah suke sukam Dan haka a masaukinsu da suka sauka na Wani hotel suka koma a shirye tsaf da Shirin tafiya kowanne lokaci.

******Sister Ashley Dake kallan Street din gabansu tana sanarwa me taxi din idan sun samu mutane a kusa pls suyi tambaya Dan batasan gidan datazo din ba itama.

Wayarta ce tafara ringing ta Kalli Jakarta Dake kan jikinta ta Bude tareda Saka hannu ciki tana Neman wayar.

Katsewa wayar tayi Wani kirin ya sake shigowa ta fito da wayar tana kallan screen din

Bazata iya Tina lokaci mafi farin ciki a rayuwarta ba kaman yanzu da wani sanyi da farin ciki me tsananin gaske Daya cike zuciyarta ba ganin sunan Dr JAMAAL akan wayarta.

Hannunta har Wani rawa sukeyi ta dauka da sauri tana hamdala farin cikinta da mutuwar jikinta duka a bayyane.

Tana dagawa kafin tayi magana muryansa tafara Ji cikin tsananin sanyi da nutsuwa yace

“Aslm alailkm.”

Amsawa tayi cikin girmamawa jikinta na sanyi da yanayinsa sedai Bata karayaba ta gaidasa.

Amsawa yayi da murya me kama da yanayi na rashin lafiya kafin da kasala yace

“I’m sorry,bazan iya magana ba ita kadai nakeson Ji,Inason Jinta,pls can you………

Katsesa Ashley tayi da cewa

“Dr JEEY kayi hakuri Amma kana buqatan Jina tukuna,
Ameenatou na dauke d……..”””dip Kiran ya katse.

Wani mummunan accident ne ya faru sakamakon motar data dakesu batareda sun San da zuwanta ba ta gefensu Wanda ya Sakasu mugun bugawa da transformer Dake gurin wuta tafara Watsi tana kokarin tashi.

Motar su BB da suka cirewa number tini tayi Baya duk da ta bugu sosai ta fashe ta gaba sbd yanda suka daki motar su Ashely din.

Reverse sukai suka bar gurin da mugun gudu goshin BB na zubar da jini sosai na buguwa Shima bullet hancinsa jinin yake zubarwa kansa na juyawa Amma haka suka tsere sedai basuyi tafiya me nisa ba suka parker motar Wani gurin da Babu mutane suka fito tareda cire komai nasu suka bankawa motar wuta sbd bazasuyi wata tafiya me tsayi ba zaa kamosu hakama sun bugu sosai Suma komai zai iya faruwa.

Mutane cikin gaggawa suka Dan taru sbd anguwan ba mutane sosai can JAMAAL ya siyawa umman gida,

Cikin gaggawa mutanen da aka samu sun shigo street din suka rufu aka motar dan taimaka musu.

Cikin yardar Allah daga Ashley har drivern Babu Wanda ya rasa ransa amma Ashley ta bugu sosai hakama bleeding takeyi sosai daga cikinta Wanda ya Saka wata nurse Dake gurin itama cewa tana tinanin cikine a jikinta Kuma Kila fita zaiyi.

Da gaggawa aka kwashesu zuwa asibiti sbd cetan ranta da abinda yake cikinta idan da akwai Rabon ya rayu.

JEEY kuwa tashi yayi daga kwancen dayake tareda zare roban drip Dake hannunsa ya tashi da kyau Yana sake Saka Kiran wayarta.

Cikin ikon Allah wayar Bata mutu ba Amma Kuma baa daga ba haka ta ringa ringing Amma baa dauka.

Siddeeq ne da isowarsa kenan Poland din tareda Mam ya shigo dakin asibitin Yana kallan JAMAAL daya Dan fada yayi haske sosai idanuwansa sun qara haske ya dago idanuwan ya kallesu.

Ganin Dad dinsa a tareda siddeeq din Wanda suka sauka kasar tare ya sakashi Dan dauke Kai Yana cigaba da Saka Kiran Ashley.

Tsakiyar dakin Mam ya iso ya tsaya akansa Shima kallansa yakeyi Yana auna irin hawan da jininsa yayi fiyeda a kirga sbd Jin JAMAAL din ciwon ciki me qarfi da zazzabi tareda tsananin damuwan ciwon Mum dinsa daya kwantar da shi ba tsammani.

Bai taba tinanin sake zuwa qasar ba Amma bazai iya riqe kansa ba ko kadan ga zuwa ganin ‘dansa Dan bazai iya komawa Nigeria dinbama da tinanin JAMAAL din ba lafiya.

Shiru ne ya ratsa gurin batareda kowa yace komaiba,

Mam yaqi magana ne tareda zubawa JAMAAL din idanuwa Dan kuwa yasan komai lalacewansa tinda ya Riga ya zama ubansa ya haifesa to ya gama da duk wani zafin kansa,

Shikuwa JAMAAL din da zafin kan nasa da radadin uba Daya kasance irin nasa yake yakicewa kafin ya juyo a hankali cikin kamewa da fuskewa ya Kalli Mam din Kai tsaye ya gaidasa Yana komawa da bayansa ya kwantar tareda Maida idanuwansa akan Siddeeq da baida ikon magana duk yansa ya so batareda Mam da Jeey din sunyi magana ba duk kuwa da yanda ya matsu ya iso yaga jikin JEEY din Dan ba qaramin tashin hankali suka shiga ba da ciwon nasa daya bawa har doctors dinsa tsoro.

Cikin Kulawa da tsananin kaunar da kulawan dayakewa jeey din a bayyane yace

“Yaya jikin Dr?”

Gyada Kai yayi a natse tareda kallan wayar hannunsa da idanuwansa Yana cewa

“Kira Ashley yanzu inason magana dasu”

Magana ya qarasa gurinsa yayi masa a natse kafin ya juya ya fice Yan daga wayarsa Dan Kiran Ashley yabarsu su biyu a dakin.

Wayar ya ringa Kira Amma shi ko shiga Batayi kwata kwata Amma Bai kawo tinanin komaiba yaci gaba da sake gwada kiranta Dan Shima yanason magana dasu din kwana biyu Bai samu Daman waya da kowaba kansa ya cake da zafin ayyuka acan Greece sunyi yawa ga Jamaal Baya Nan ga ciwon JAMAAL na rana tsaka da kokarin isowansa Poland hakan yasa wayoyinsa a kashe suke saida ya iso yake kunnawa yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected