AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
“No acan Baya Bata Hakan and Bata firgita cikin bacci and Babu staff dayake da Daman kwana a cikin patients Koda likita ne Amma Kuma duka staffs sunsan password na shigowa kowanne room and babu security cameras a dakunan patients,
To Nima dai bansan Menene asalin abinda yake Sakata wannan halin ba.”
Shiru yayi Baice komaiba Bai Kuma sake kallanta ba yace
“Yanzu time yayi na tafiyanki kenan?
Babu wani abu datake buqata daga Nan har safe?
“Yes doctor”
“Ok,Zaki iya tafiya.”
Daukan wayarta tayi ta juya ta fice daga dakin tareda jan kofar ta nufi dakunansu na nurses tana fatan Allah yasa yauma Dr JEEY din ya tafi da Ameenatou din office dinsa Dan ita dai hankalinta Sam Sam ya kasa Kwanciya Kuma Bata zargin kowa Amma dai tana zargin akwai Wanda yake shiga gurin Ameenatou din kodai da sunan sata ko Wani abin daban.
Bayan ficewan sister Ashley ya dauki mintina a tsaye batareda ya juyoba Yana tinanin dayake Neman nauyaya kansa kafin ya sauke numfashi me sanyi da nutsuwa tukuna ya juyo ahankali ya zuba mata idanuwansa lokacin idanuwanta a rufe suke bacci ya dauketa da alama.
Ajiyan zuciya mara sauti ya sauke tareda Kai idanuwansa ya zubawa dogayen yatsun hannuwanta farare tas babu datti ko kazantar komai a cikinsu kaman dai yanda akewa Yara haka sister Ashley take tsaftaceta bazata taba samun daddi jikinta ba matiqar ba ciwon ne ya tashi ba.
Hannuwan nasu ya kalla tsawon seconds kafin ya zare nasa ahankali tareda mayar da nata gefenta yaja abin rufa ya rufeta ya juya ya fice dakin.
#MAMUH#
#BESTLOVE
#HOTLOVE
#ROMANCE
#MAM SEELAH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
71
Yana fitowa kusan duka rooms na patients din Dake block din ya shiga ya dubasu tareda karantar block din sosai kafin ya fice zuwa office dinsa Dan bayajin yauma zai bar asibitin ayau ma.
Yana Isa office dinsa Kai tsaye hannuwansa yaje toilet ya wanke yayi sanitizing nasu ya fito ya dauki wayarsa ya kira siddeeq tareda sanar dashi gobe da safe a tabbatarda Dr Dee ya isa asibitin da aka tura sa.
Yana ajiye wayar miqewa yayi ya nufi table ya Bude laptop dinsa Dan duba report na Mum dinsa na ranar Dan kullum sai Anturo masa bayanin yanda lafiyanta ke tafiya din a hankali ahankali dan samun nutsuwan zuciyarsa.
Yana gama dubawa ya Nemi doctor din da kusan komai na case dinta na hannunsa suka fara tattaunawa Yana sake masa bayani da Baki tareda shawarwarin yanda zasu ci gaba da lallaba jikin nata Dan har lokacin Bata iya komai da kanta kuzarinta Bai dawo ba na iya motsa jikinta da kanta.
Ya dauki lokaci me tsayi Yana wayan kafin ya gama,
Yana ajiye wayarsa akan table din gabansa dago idanuwansa yayi ya Kalli agogon gabansa ya duba time.
Karfe goma Sha biyu NE da Mintina arbain da shida Dan haka ajiyan zuciya me sanyi kadai ya sauke tareda miqewa ya natsensa ya fice daga office din tareda rufewa ya nufi block A din Yana sake Dan duba time a agogon Dake daure a hannunsa.
A natse ya isa dakin batareda ya Hadu da kowaba ga Wani tsit da gurin yayi baka Jin motsin komai bayan na iskan Daren Dake kadawa..
Bude dakin yayi a natse sbd kada motsi me girma ya tashe ta idan bacci takeyi ya shiga dakin idanuwansa akan gadonta datake can qurya ta dunqule guri Daya tareda qanqame jikinta idanuwanta a rufe hakama ta fita rufan da yayi mata da alama awannin alluran sun qarasa cikewa a cikin Daren ta sake ta tinda ta samu kuzarin motsawa harta hade jikinta guri Daya ta nannade haka.
Takowa yayi a nutsuwansa tako yaushe ya iso bakin gadon tareda dago fararen idanuwansa ya zuba mata su a hankali kaman mara lafiya Yana kallan fuskanta datake fayau kaman ta baby,
If zai Tina Asalin kamanninta daidai sune na ranar Daya fara yi mata kallan seconds a Nasarawa sai kuma ranar daurin aurenta da Haroon a cikin adonta na jiran zama matarsa batareda sanin ranar ne ranar barinsa duniyanba.
Dauke idanuwansa yayi a hankali tareda matsowa ya Kai hannuwansa duka biyu ya ja abin rufan ya sake rufeta tareda kama kanta ahankali ya mayar mata akan pillow Yana qin kallan fuskanta sbd kusan da sukai sosai.
Hannunsa ya Saka a aljihunsa ya Ciro Wani turarensa me shegiyar tsada da kama duk abinda ya tabasa ko kusantarsa ya nufi jikinta ahankali ya fesa mata tareda Kai hannunsa ya Bude tafin hannuwanta masu taushi ya fesa mata a ciki.
Yana gama rufeta da gyara mata kan nata karfe Daya da minti Daya na bugawa Dan haka ya juya a fice tareda rufe kofan ya fesa turaren a handle na kofan shiga dakin ya juya ya fice daga block din gaba daya.
Yana iso office Kai tsaye bedroom din ciki ya wuce yana zaunawa kan single couch din dakin Yana Dan rife idanuwansa Dan kansa ma ke sarawa.
Karfe biyun dare daidai block A ya dauki qarar Wani firgitaccen ihun Ameenatou me firgitarwa da tashin hankali me girman gaske Dan kuwa ihun duk Wanda ya jisa mummunan faduwa gabansa yakeyi..
Sister Ashley da wasu nurses biyu ne suka fara fitowa a rikice hankalinsu a tashe harma da tsoro suka nufo block din.
Dr JEEY ma dayake zaune Daram a office dinsa Yana jiran Daman shedawa da kansa abinda yake faruwa a block din na Abinda yake tayarda ciwonta da baa saniba.
A kunnuwansa amon ihun da Shirun dare ya debo ya kawo masa ya sauka,
A Karo na Babu adadi ya dago idanuwansa ya duba time Taga karfe biyu da Mintina biyar,
Amon ihun ne me karfi ya sake shiga kunnuwansa Dan haka Kai tsaye ya miqe batareda ya tsaya komai ba ya nufi kofa ya fice zuwa dakin.
Koda ya Isa su sister Ashley da sauran nurses sunata kokarin Riqeta Amma kwata kwata ta haukace gaba Daya ihun takeyi jikinta na Wani irin rawa da jijjiga sbd firgata.
Yana shigowa Kai tsaye gurinta ya nufa din idanuwansa akan wuyan rigarta Daya cakuda ba kaman yanda ya San ya barsa ba Dan kallan dayayi mata Babu abinda Bai riqe yanda ya barsa ba Dan haka Koda ya Isa idanuwansa tini suka sauya take da wani irin zafi da bacin ran Daya Saka Bai tsaya komai ba Yana isa hannuwansa biyu yakai ya kamota gabaki dayanta tareda girgiza ya ambaci sunanta a Karo na farko rayuwansa.
Bata Jin komai Bata gane komai bayan ihun da rawan da jikinta keyi Dan haka duka abin ya sake rikicewa hakama sister Ashley Kai tsaye itama idanuwanta suka Kai wuyan rigar Ameenatou din Da botiran gaban rigar na sama kaman biyu sun fice.
Mummunan faduwa gabanta yayi da sauri ta matsa tana cewa kowa ya fice daga dakin Dr JEEY din da ita datake nurse dinta zasu shawo kanta sbd ganin mutanen ke sake haukatar da kanta.
Shigowan nurse Fahat ne da sauri Yana bayyanarda damuwansa da tambayar jikin ne ya Saka Sister Ashley dakatar dashi tana cewa anason a rage ne sbd duka kowa yasan Taron mutane a gabanta shine babban matsalan ciwonta.
Muryan nurse Fahat ne ya Saka ihun Ameenatou din da rawan jikinta tsananta tana kokarin kwacewa daga riqon JEEY din Wanda shigowan nurse Fahat ya bankado masa da qamshin turaren Daya fesa Dan Hakan.