AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Wani kyakkyawar murmushi ya sake tareda yiwa babban Saida safe da turanci ya fice Yana amsa wayar.
Itama tana hayewa saman Kai tsaye dakinta ta wuce tayi Shirin bacci ta fito palonsu na saman pages a zauna tana Dan kallo tana duba Abu a laptop sbd abincinta ya narke a Cikinta kafin ta kwanta.
Tana zaune Ashley ta hawo saman tana duba wayarta itama tareda farin Cikin aikinta da zata fara fita Suna dawowa daga Macau din.
Itama sai datayo Shirin bacci ta fito suka zauna Suna firar itama tana Dan chatting da yan uwanta yanzu Dake yawan damunta harda son zuwa gurinta Amma ta dakatar da hakan Amma dai tana Basu kudi sosai shiyasa duk suka haukace mata suke binta.
Sun jima sosai a palon kafin suka shige bacci.
Sanyin AC ta rage sosai sbd yau Arfat Ashley ta kawo mata shi ya kwana gurinta tinda tafiya zasuyi gwara ya kwana da mommansa suji dumin juna.
Shigewa bargo tayi tareda rungumesa tana Jin kewan ‘danta tin batai tafiyanba.
Washe gari jirgin yamma zasu bi Dan haka ba rushing hankali kwance ta wuni tareda iyayenta Bata fita koina ba.
Meeting sukai da Dad dinta anan office dinsa na Cikin gidan itada Hafiz da uncle Ahmed harma da Fatmah da James dayake Dan amanarsu Dad din Shima.
Sun jima Suna meeting din kafin suka gama duk akan aikin da kowannensu zaije musamman na Hafiz dayafi Mahimmancin Kuma Shima dai daga karshe da Fatmah din zasu tafi ita Kuma tareda president din kamfanin gaba daya zatai tata tafiyan da James Dan sai Kuma Ashley datake kaman kaucewa barinta tafiya ita kadai da mazan wanda shi kansa Jamaal share maganar tafiyar tata sbd Jin da Ashley din zata tafi ne Amma badan hakan ba Kai tsaye zai sanar Bai bada izinin tafiyarba Kuma Babu wanda ya isa ya tsallake hakan.
Babbah kaman zai Saka mata aljanun dubiya haka yakeji Amman sanin zataiwa Jamaal Nisa ne ya sakasa Jin nutsuwa da farin Cikin tafiyar daga baya musamman daya ringa nanatawa Ashley karsu dawo saita huta Kona kwana biyu ne bayan aikin sbd kada ta dawo Nan taci gaba da fita aiki batareda ta hutaba.
Karfe 5 na yamma suka fito Hafiz ne da Uncle Ahmed tareda Arfat suka rakasu har airport Cikin wasu lafiyayyun black Rolls Royce phantom.
Suna isa airport Ta rungume Arfat a jikinta tareda kissing gashinsa da gefen fuskansa harma da tsakiyar kansa tana cewa
“My love mommah zatayi missing Dinka,
I Love you Son”
Kissing gefen fuskanta yayi Yana Dan lafewa a jikinta tareda Yin shiru Yana son binta Amma bai Saba rigima ba Dan haka Hafiz Cikin kulawa da tarairaya ya karbesa Yana kwantar dashi jikinsa Yana fada masa maganganu masu dadin da suka sakasa sakin dariya Yana maqale Hafiz din.
Jirginsu karfe 7 na daren ya tashi shi kuwa Jamaal nasa tin safe yabar kasar.
********
Duk wannan lokacin Mam yayi shiru ne sbd yasan Babu abinda zai warware auren ‘dansa kaman yanda yasan a yanzu bazasu bada matar ba Dan haka kaman yanda ya Saba baya komai da garaje Shima lokaci ya bawa Omar da Babbah su gama borinsu Amma auren ya dauru rabuwarsa sai mutuwa,
Kodai Wani daga maauratan ne ya rasu kokuwa da kansa ya aika Wani daga Cikin masu jiran mutuwar auren haduwa da malaikun tambayar kabari.
Dan hakama baya qasar yayi tafiya kusan wata daya sedai Yana can labarin daya riskesane ya sakasa dawowa ba Kai tsaye sbd lameenu daya tashi bayan yasan alluran dayake masa ta kama jikinsa warwarewan jikinsa ba kusa ba.
Shikuwa lameenu qarfin hali da taurin zuciya me tsananin gaske ya Saka ya fara warwakewa baima gama sakewa ba jikin nasa yafara karfin halin magana ya Saka Akira masa BB sedai Koda su BB din suka taho da labarin da suka wayi gari dashi safiyar yau din suka taho masa na rasuwar Ameeenatun datake asibitin mahaukata wadda duk yanda sukaso samun Damar ganinta tinda wannan AM jden din ta bayyana sun kasa samun Damar Dan haka tana rasuwa sukasan dole zaa Nema danginta Dan Basu gawarta.
Su BB na gama sanar da lameenu rasuwar rawa jikinsa ya fara Yana Neman rikicewa sedai bazai yadda ya sake komawa kwance ba batareda yaga gawar wannan Ameeenatou din da Idanuwansa ba Dan haka a yanda yake yace a kaisa asibitin yanason ganin gawar.
BB ne da bullet suka bisa da motarsu tasa motar Tana gaba driver na jansa.
Idan yace zuciyarsa ba tsallen tashin hankali da matsanancin tsoro take Ciki ba to tabbas yayi karya me girma.
Hannuwansa har Wani irin rawa sukeyi sosai kaman yanda jininsa ke rawa Amma ya hana kansa fidda tashin hankalinsa.
Kafin su isa asibitin tini bullet ya sanar da Mam abinda yake faruwa Dan haka daga airport Kai tsaye asibiti shima yace a nufa dashi.
Ya Riga su isa Dan haka Yana isa shine ya fara samun Damar gawar Aliyah datai munin da shi kansa kallo daya yayi mata ya dauke Idanuwansa sbd yanda ta koma kaman qwarangwal sbd mummunan rama da azabar data gama kone duka Wani jininta da tsokar jikinta ta allurai da ake banka mata na masifaffun qwayoyin da suka wuce hankali.
Duk rubuce rubucen da zaayi anyi kafin isowarsu lameenu an basa gawar a ambulance ya wuce da ita gida inda kafin ya isa tini yan jarida Suna mansions din biyu Suna jiransu wanda bullet ne me wannan aikin.
Lameenu na isa asibitin a zauce ya sake juyowa bayan samun labarin waye ya dauko gawar.
Yana isa take Taron Yan jarida suka sufesa tako Ina Suna jeho masa tambayoyin da suka sakasa kusan samun bugawan zuciya da sauri ya dafe kirjinsa Yana Jin attack na kokarin kamasa.
Sake jeho masa tambayar Akai wadda ta Saka BB zamewa daga cikin Taron Yana hada zufa sbd da alama abubuwa sun fita a Lokacinda basa tsammani.
“Alh lameenu seelah shin da gaske ne Kaine kake bibiyar rayuwar ‘yar Omar jaden Ameeenatou jden wanda ya hakan ne ya kawo rabuwar familyn biyu,
Sbd ankama maaikatan asibitin datai zama wainda suka bada tabbacin Kaine kake Basu alluran d suke mata har haukanta tayi tsanani,
Sannan Audio na maganarka da Dr Dee wanda kuke maganar yaci gaba da aikin dayake Yi karshe yanzu an tabbatarda kashesa Akai ba mutuwar da ake tinanin yayi bace,
Meye ne gaskiyar wannan maganganun??
Shin gaskia ne ko kanada abinda zaka fada Akai??
Jiri ne yafara diban lameenun sbd haka securities ne take suka fara korar Yan jaridar Dan shigar dashi gida.
Yana shiga da sauri ‘yarsa daya data rage masa siyam tayi saurin taresa tana karesa daga hotinansu da ake dauka tana riqe hawayenta sbd radadin da zuciyarta ke make harya wuce abinda zuciyarta zata iya dauka.
Suna shiga Kai tsaye gawar datake shimfide a harabar gidan ya dosa kafafunsa na kasa daukansa kaman zai zauce yake Jin kansa da kwakwalwansa.
Kafin ya iso kan gawar Mam dayake tsaye tareda duka familyn SEELAHs din ya Bude gawar wadda ta tashi daga Aliyah ta koma wata halittar daban.
Duk Mai imanin daya kalli gawar Aliyan sai yaji firgita da tsananin tsoron Allah ya kamasa tareda hawayen tausayi me tsananin gaske Dan haka kallo daya Ayesha da siyam sukaiwa gawar suka zube qasa gwiwoyinsu na sarewa Cikin tsananin tashin hankali da Kuka Mai tsananin gaske.
Mum Sarat kuwa kallo daya tayiwa gawar ta tabbatarda Aliyah ce Dan haka bugawa daya zuciyarta tayi take zuciyarta ta buga a gurin.
Lameenu ma zuciyarsa kusan bugawan tayi sbd yanke jiki yayi ya Fadi a gurin baya ganin komai bayajin komai.