AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Bai qarasa budewa ba ya dauki kayan yakai masa cikin fridge da wasu manyan roban Greek yoghurts masu kyau da tsada.

Yana ajiyewa ya dawo gefensa ya tsaya Yana sanar masa bincikensa yafara leading dinsa zuwa ga su BB Dan kuwa Wanda Akai masa hanyar ya Siya a gurinsa shine dealer yaron BB ne.

Shiru JEEY din yayi na tsawon mintina kafin ya dago idanuwansa ya Kalli siddeeq din yace

“Kafin ka gama bincikowa zuwa gobe na Saka a Aiko results na Haroon da aka taba yi masa test lokacinda ya samu wannan matsalan ta bleeding da ciwon,
Idan yazo ka hada results din da kwayan ka tabbata sun Isa hannun Dad ta wata hanyar sbd yasan abinda ya kashe ‘dansa kafin accident dinsa”

Gyada kai siddeeq yayi Yana tinanin ta inda Haroon ya Hadu da wannan kwayoyin sbd yasan Bai taba saninsu bama bare shansu Dan haka sanin Dad Mam Kai tsaye zaisa su samu Clue na inda Haroon ya Hadu dasu Dan idan har ta tabbata kwayoyin na kasuwancinsu ne to a qanqanin lokaci zaiyi tracing inda sukai suka Isa ga Haroon.

Patient Dr JEEY yayi dubawa har magrib tukuna ya Samu kansa Kuma harda Ameenatou din ya duba da dubara ya zame ya tafi sallah daga can Bai dawo ba fita yayi wani gurin sai 9 ya dawo lokacin Kiran sister Ashley ya shigo wayansa akan yauma Ameenatou din taqi cin abinci Dan haka Kai tsaye ta kawota office dinsa da ido yake binta lokacinda suna shigowa ta kwance hannunta daga hannun sister Ashley Tayo gurinsa tana murnan ganinsa.

Sister Ashley ficewa ta juya zatai yace ta kawo masa maganin Ameenatou din zai sbd jiya ma bata sha na daren ba.

Juyawa tayi ta fice Dan kawo masa.

Ameenatou kuwa tana zuwa gurinsa ta tsaya gefensa tareda kallansa cikin muryanta me sanyi tace

“Haroon ya dawo ko??

Bai amsaba bayan idanuwansa Dake kanta yana Jin kalman sunan Dan uwan nasa har cikin zuciyarsa da kewansa.

Hannu ya miqa mata batareda yace komaiba ta kama ya dagata cak daga zaunen dayake ya zaunar akan table din gabansa Wani irin qamshinta na shiga hancinsa ya kalleta a natse sister Ashley tayi mata wanka fes ta gyarata kaman babyn gaske qamshinta me sanyin gaske sai tashi yakeyi.
#MAMUH#
#ARFAT SEELAH
#OMAR JDEN
#BABBAH
#HAFIZ BABBAH

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
78
Wani silent numfashi ya sauke ahankali cikin nutsuwa tareda dauke idanuwansa akanta Yana zare hannunsa daga cikin nata ya dauki wayarsa ya turawa sister Ashley text akan ta kawo maganinta akwai Wanda zai sauya mata dasu batareda ya rubuta a cikin file dinta ba.

Babu jimawa sister Ashley ta dawo office da maganin tayi knocking.

Miqewa yayi ya nufi kofar ya Bude tareda juyowa ta shigo ciki.

Ameenatou na ganinta ta sauko daga inda yabarta zaune tayi gurinsa da gudu ta riqesa tareda boyewa gefensa tana kallan sister Ashley da dariya a fuskanta ta fara maqe kafada tana leqo sister Ashley din tace

“Banason sister Ashley,Haroon Ameenatou takeso…..”

Kalamanta na karshen ne suka shigesa Bai juyo ya kalleta ba ya miqawa sister Ashley datake kallan Ameenatou din kafin ya saci kallansa Dan ganin yanda ya amshi zancen Dan ko Haroon Dan uwansa ne akwai sosuwan Rai matarsa ta ringa Kiransa da sunansa.

Maganin ta miqa masa tareda file din Ameenatou din Dan cire sunan wancan maganin acikin file din.

Karba yayi ya nufi kujera ya zauna ya bude file din Yana dubawa a natse cikin kamewa,

Sister Ashley hannun Ameenatou din ta kamo ta janyota gurinta sbd barinsa yayi rubutun da zaiyi tana cewa

“Babyn sister Ashley oya zo Nan ki bar Dr yayi rubutu tukuna”

Qwacewa tayi tana maqe kafada ta koma gurinsa da gudu ta haye kafafunsa tayi zamanta harda riqe rigarsa kafin tace

“A a Ameenatou gurin Haroon takeso batason gurin Sister Ashley”

Kallan fuskan JEEY din tayi tareda cewa

“Haroon ma Ameenatou yakeso ko??

Kasa cewa komai yayi sai idanun Daya dago ya zuba mata yana mata Wani mayen kallan Daya Saka sister Ashley Dan dauke Kai sbd Ameenatou tana Neman janyowa kanta abinda bazata iya dauka a wannan yanayin datake ciki sbd zaman datai akan kafafunsa Saida ya Saka pen din hannunsa Dan kufcewa amma Bai bari ya fita daga hannunba ya damqesa.

Mayar da Idanuwansa yayi akan file din zaici gaba da abinda zaiyi ta Saka hannuwanta biyu ta kamo fuskansa da tafin hannuwanta dasuke qamshin Wani fitinanniyar turaren Oud me tsananin qamshi da sanyi da sister Ashley ta shafa mata har a tafin hannuwanta suka shiga hancinsa ya dakata daga karanta komai sbd upside down da rubutun suka koma masa batareda ya motsaba.

Juyo da fuskansa tayi gurinta tana Bata fuska ta sake maimaita masa tambayanta,

Silent numfashi ya sauke a natse kafin ya ajiye pen din dayake hannunsa ya Dora hannunsa Daya akan nata hannun zai janye hannuwanta daga fuskan nasa ta ture hannunsa tana sake matso da fuskanta gap da tasa har numfashinta na shigarsa sosai ta sake maimaitawa akan sai Haroon yace yana son Ameenatou.

Sai alokacin ya Kalli cikin idanuwanta batareda yace komaiba sbd idan har tambayarta Haroon ne to har abada baida wannan amsar dazai Bata ba sbd shi JAMAAL ne ba Haroon ba Dan haka bazai taba amsa tambayar da Bada sunansa tazo ba.

Hannuwanta duka biyun ya kama tareda janyesu daga fuskansa Ya Bude Baki ahankali cikin nutsuwa yace

“Ameenatou pls.,”

Sister Ashley dai Jin tayi duk tana Neman rudewa da tsayuwa a gurin Dan haka ta Dan sake dauke Kai daga kallan gurinsu din tana tinanin dole tafara yiwa Ameenatou fada da koyar da ita kame Kai daga matsewa Dr JEEY din Dan kuwa karta janyowa aikin da bazasu iya daukaba gabaki dayansu.

Wani kukan da basuyi zato ko tsammani bane ta fasa musu a gurin tana dukan kirjinsa tana cewa

“Haroon bayason Ameenatou,
Nidai sai Haroon yace yana son Ameenatou”

Sister Ashley cikin rudewa ta dago tana Ambatar sunan AMEENATOU din tana kokarin tahowa ta janyeta.

Ameenatou na ganin Hakan ta shige jikinsa tareda qanqamesa tana sake fasa kukan batason sister Ashley ta tafi da ita.

Rintse idanuwansa yayi ya Bude Yana rasa abinda zaice ko zaiyi,

Sister Ashley ma dakatawa tayi tana kasa karasawa ta kallesa tace

“Dr kodai zan tafi da ita ne yau din tinda rigima takeji??

Cikin jarumta ya gyadawa sister Ashley din Kai Yana cewa

“Yes pls” sbd yau dai Kam zaiso ta tafi gurin sister Ashley din ta kwana Dan kansa yafara daukan nauyi zaiyi kwana a zaune da ciwon Kai.

Tahowa sister Ashley tayi tana son kamata Amma taqi yadda ta maqalesa fiyeda yanda yayi tinanin zata iya hakama kukanta karuwa yakeyi sosai tana cewa Bata son sister Ashley Haroon takeso.

Sister Ashley na ganin ta rikice ta dakata zatai magana ya dago a kasalance yace

“Ki barta kawai”

Son yake ta dago daga jikinsa ya sallami sister Ashley Amma San taqi dagowa sai kukan takeyi tana cewa Haroon bayason Ameenatou.

Sister Ashley cewa tayi yabar file din idan tazo daukan Ameenatou ta tafi dashi ta juya a silale ta fice tana kasa kallan Dr JEEY din da Ameenatou ke jijjigawa tana dukan kirjinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected