AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Ahhh Omar ahhhhh Omar burinmu na ratsa ilimi me kyau zai tabbata,
Zamuyi Tarayya da ilimi a cikin wadatar Ubangiji da rufin asirinsa.”

Wani farin ciki me sanyi dayake fitowa daga qasan Rai yake bayyana a kan fuskar Omar din Yana sake rungume kasim da mamman Wanda yake washe Bakin dole Shima.

Jamilu kuwa gaba Daya hankalinsa baa kwance yake ba idan ba ganin yayi dukiyar zinariyar ya shiga hannuwansu ba sunbar Ashalawa zuwa rayuwar arzikin Dake jiransu a duniyar wajen Ashalawa Dan kuwa Ashalawa kamar duniyar kafiran da ko sunan Imani ba Basu sani bane,
Ashalawa kamar wata qabilace me zaman kanta da Babu kalar zunubin da baa aikatawa a bayyane cikin izgilanci Dan haka shi a matse yake da barinta a yanzu Daya samu Arzikin da zai wadatar da duk zuriar da zai Tara har tsawon lokacinda Bai saniba.

Lameenu duk yanda yakejin murnar nasa samun a farko gabaki Daya ya dakushe Baya murna ko yar kankanuwa,
Daci da nauyi yakeji a zuciyarsa fiyeda yanda yayi tsammani Dan Bai taba dauka zaiji qyashin samun Daya daga cikin seelahs dinsa ba.

Har dare har safe suna aikin cire arzikin zinariyarsu ba har kusan wata yamma kafin suka samu aka gama cireta gaba Daya aka narka aka ajiye a jere wanda nauyinsu ya sake girgiza Ashalawa.

Sai a Daren su kasim suka samu kansu suka dawo rumfarsu bayan sunyi magana da masu Siya,
Na Omar wani bature ne zai Siya,
Na kasim da jamilu kuwa balarabe ne zai Siya Dan haka Basu baro tent na turawan Dake gefen manyan Ashalawa ba dayake da masu tsaron gaske na samudawan Ashalawa.

Karfe Daya da Rabi da wani abu suka shigo rumfarsu inda mamman da lameenu ke kwance suna bacci Dan haka Basu tayar dasu ba suna cikin tsananin farin cikinsu Daya dadu Dan kuwa wannan Daren shine darensu na karshe a Ashalawa washe gari zasu bi turawan zuwa sabuwar rayuwar Dake jiransu Kuma zasu tafi ne da Yan uwansa lameenu da mamman Dan kuwa dukiyarsu ta seelahs ce gaba dayansu.

Jamilu kaf rayuwarsa Bai taba samun kansa a cikin asalin farin ciki ba irin Daren Dan kuwa mahaifansu mata zasu samu rayuwar kulawa da tattalin da mahaifansu Maza Basu samu damar Basu ba suna gurin yawon nema har suka rasu.,
Zai Tara Iyalin kansa su taso cikin Hutu da wadata ba irin tasa rayuwar Daya taso tin qanqani a yawon duniya ba.

Omar da kasim ma kwantawa sukai kusa da juna suna kallan juna kowannensu zuciyarsa kaman zata zage sbd farin ciki da murnan samun rayuwar nutsuwa da Kwanciyar hankali da ilimi da suka Dade suna buqata da fatan samu.

Omar ne me tsananin burin son rayuwar nutsuwa da ilimin dayake tattare da Kwanciyar hankali da rashin damuwa,
Ahankali raayin Hakan da tsananin so da burin Hakan ya shiga kasim sbd tsananin kaunarsa da Omar Wanda sunfi kusanci sosai sbd kasim din Dake matiqar son Omar tin suna qananun kaunar Omar daban take a zuciyar kasim duk da suna son junansu duka su biyar din Amma Omar ya samu qarin matsayin da babu wanda ya samu a Aransa.

Tsakiyar dare guraren karfe uku bayansu da zagayensu yayi tsit Babu motsin komai da kowa sbd runfarsu tana daga baya Baya sosai inda dagasu sai daji.

Dukkaninsu sunyi Nisa a bacci me karfi sbd wahalar dasuka Sha ta shafe kwanaki acikin tsananin zafin Rami da duhu da wahala shiyasa idan ka fito kake bacci sosai sbd wuyar da gangar jiki Tasha.

Ahankali mamman da idanuwansa biyu bacci ba yaji motsi na kusanto runfarsu Wanda motsin yake cikin sanda.

Bude idanuwansa yayi ahankali daga kwancen dayake batareda ya motsa ba Yana sake saurarawa.

Tabbas motsin tahowa ne gurinsu
Tashi zaune yayi ahankali cikin qaramin hasken dayake gurin na farin wata Yana kallan inda lameenu yake kwance Shima idonsa biyu baiyi bacci ba yanajin motsin mamman din.

Wajen rumfar ya juya ya kalla daidai da isowar mutum uku Bai iya ganin fuskokinsu ba sbd ba haske sosai
Sharbebiyar wuqar Dake hannun Daya daga cikinsu idanuwan mamman suka sauka wadda yasan kaifinta Bata fitowa cikin mutum idan an soka batareda ta yanko kayan cikin mutum ba.

Da sauri mamman din ya miqe Yana Ciro tasa wuqar Dake karkashin pilon Kwanciyar sedai kafin yayi yunkurin Isa gurinsu lameenu yayi saurin riqesa daga kwancen dayake Yana kallansa cikin wani irin kallan Daya Saka mamman din kallansa Shima duk da duhu ne.

Zuciyoyinsu bugawa sukeyi sosai da sosai kaman zasu faso kirjinsu daidai lokacinda mutanen sukayi kansu Omar Dake kwance sedai kafin su afka musu kasim ne yafara tashi yayi saurin tarewa Yana ambar sunan Omar da karfi.

A rikice Omar da jamilu suka tashi lokaci Daya suna miqewa tsaye kowannensu na lalabo wuqarsa da wasu irin gora masu qarfin gaske.

Kokawa me qarfi ce ta kaure tsakaninsu suna ambatar sunayen su mamman da Basu ga tashinsu ba Amma Sam Babu motsin su,

Kokarin kashesu mutanen keyi sosai cikin rashin Imani ko kalilan hakama ga duhu basa ganin juna Amma sunqi yadda Dan haka fadan yafara Muni sbd jini ne ke zuba Tako ina a tsakaninsu sbd kaifin makaman hannuwansu bana wasa bane.

Ba qaramar yanka jikin kasim Dana Omar yasha Amma Sam sun qi yadda a kashe su,
Jamilu yanada karfi sosai Dan haka shi Bai jiqata kaman su ba sedai Shima yasha yankan har a fuska.

Mamman da zuciyarsa ke wani irin rawa da jijjiga daga inda yake yasan ko baa fada ba kashe su Omar zaayi to Amma meye amfanin lafewansu Dan akashe Yan uwansu su gaje zinariyar bayan idanma an kashesu din wainda suka kashesun zasu kashesa su tafi dashi su anbarsu a biyu babu an kashe musu Yan uwa Kuma an tafi da zinariyar.

Idan har Yan uwansu zasu mutu to gwara su mutu a hannunsu su su gaji zinariyar Dan kosu da zasu mutu sunfi son su Yan uwansu su mallaketa.

Abinda yake cikin ransa shine yake yawo acikin zuciyar lameenu Dan haka juna suka kalla a lokacinda suke Jin kasim na ambatar sunansu cikin rauni sbd tinanin ko an Riga an kashesu ne basa motsi.

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar
#Arewabooks@Mamuhgee

 

4
Hankalin Omar tashi yayi mummunan yi rashin Jin motsin mamman da lameenu Dan haka ya fara sarewa Dan kuwa idan har an kashe mamman da lameenu anyi musu mummunan raunin da seelahs zasu bace gaba Daya Dan Suma ba tsira zasuyiba.

Jamilu da Shima yafara gabalaita bazai iya taresu ba ya juyo inda su mamman din suke zai ambaci sunan lameenu kawai lameenun ya daga wuqarsa Dake wani irin daukan ido a duhun ya kutsata gabaki Daya a cikin jamilun take jamilun ya dago jajayen idanuwansa da sukai jajir ya Kalli fuskar lameenu,

Shima lameenu jamilun ya kalla tareda zaro wuqar ta sake kutsata a gefen cikinsa tareda cirowa jinin jamilun na gangara a hannunsa har qafafunsa,
Jajir idanuwansa sukayi wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna cika a cikinsu dukkanin jikinsa rawa yakeyi hakama.

Mamman ma tasa wuqar ya Ciro ya daga sama tareda warawa da qarfi zai kutsata gefen cikin Omar kasim da acikin duhun idanuwansa suka sauka akan abinda yake Shirin faruwa yayi saurin karawa da niyar ture mamman din sedai tini wuqar ta kutsa gefen cikinsa ta shige gaba Daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected