AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
24
Koda suka Isa gida mum tayi magana sosai da Haroon ta sanar dashi matsalan datake shakkan sanar da Jamaal Dan batasan tayaya zai fara ba Kokuma ta Ina zai fara binciken Wanda yayi wannan mummunan aikin na rashin Imani da tsoro tareda rashin tausayin daukan ran Wadda take fama da rayuwarta tin haihuwa.

Shiru Haroon yayi sbd Shima hankalinsa ya tashi da wannan zancen Dan kuwa yafara Jin tsoro da wani irin tashin hankalin na sake shigarsa idan har Jamaal ya tsananta bincike duk da baisan waye yayi wannan aikinba Amma dai Yana shakkar binciken Hakan ya binciko masa abinda zai karasa dagula Rai da kansa bayan yanzu lafiyan fadilan suke tsananin fata Dan itace farin ciki da abinda Jamaal dinsu ke buqata.

Koda Jamaal ya dawo gidan cikin Bai Nemo kowa ba Kai tsaye bangarensa ya nufa ya shige bedroom dinsa ya rufe kansa aciki.

Wanka yayi Yana fitowa sallahn azahar kawai yayi ya kwanta sbd kansa Dake Neman tsagewa da ciwo.

Bacci sosai yayi Wanda yake cikeda mafarkai masu nauyi Dan haka Yana tashi da laasar wani wankan ya sake jikinsa ya sake daga nauyi ya shirya ya fito cikin doguwar jallabiya fara qal Data kwanta jikinsa tayi masa wani irin kyau na nutsuwa.

Masallaci ya fita acan yayi sallah tareda Dad dinsa Wanda yayita Kiran wayarsa Baya samu.

Zuba masa idanuwa Dad din yayi bayan sun gama gaisawa ya tambayesa jikin fadila sbd gobe ne daurin auren nasu Wanda zaayi sa kaman na Wainda suka samu cikin shege sbd kawai yanayin amaryan.

A daidai wannan lokacin da gabar Jamaal din kansa yayi sanyi matiqa tareda shiga wani irin fargaba da tsoro me tsananin gaske.

Kai tsaye bangaren Jamaal din suka nufa hadda Dad din Wanda zaiyi magana da Dr Aleena Dan Basu zauna suka tattauna ba tinda tazo.

Suna shigowa tana zaune Palo tana karanta wasu bayanai ta email dinta da Dr Martinez ya dawo mata dashi Akan matsalan fadilan Data tura masa bayanan da komai nata tin jiyan.

Akan Jamaal idanuwanta suka fara sauka ta rufe iPad din hannunta tareda kifeta gefenta tana mayar da kallanta kan Mam da Shima ita yake kalla cikeda kulawa Dan har cikin ranta Yana Sonta Amma yasan bama zai fara maganar mayar da aurensa da ita ba sbd Jamaal dayaji zafin rabuwarsu fiyeda komai hakama dawo da aurensu Jin yakeyi kaman zata iya sanarda Jamaal wani abin game dashi ne shiyasa bayason zaman Jamaal a hannunta ya dawo dashi hannunsa tintini.

Sannu da zuwa tayi masa cikin sakewa da kulawa tana sake murmushinta me kyau da tsari.

Shima cikin farin cikin ganinta da kulawa yake amsawa yana qarasawa ya zaune kujeran gefenta Jamaal kuwa gefenta ya zauna Yana Saka hannunsa cikin nata sbd samun sassaucin abinda yakeji zuciyarsa na ciki ayau din.

Fira sukeyi sosai tsakanin mum din da Dad da Haroon Wanda ya raba hankalinsa kan firar da Kuma Jamaal Wanda Bai iya furta ko kalma Daya ba Dan Yana cikin nasa tinanin daban.

Abinci mum Atee ta Aiko anan bangaren aka jere musu a dining din Jamaal ta Basu Daman cin abinci a tsakaninsu da ‘yayansu.

Mum da kanta ta takurawa Jamaal cikin kulawa Mai tsananin gaske yasamu yaci abincin yasha ruwa yabar dining din and magrib datai.

Yana barin gurin mum ta bisa da kallo kafin ta dawo da kallanta kan Mam Dan karantar yanayinsa sbd ko kadan batason yasan me suka gano batareda sun fitar da fadilan waje ba.

Sallan magrib sukai suna gamawa Jamaal yabar gidan da motarsa.

Dad da Haroon ne tareda Dad Lameenu suka dawo ciki.
Kai tsaye office dinsu na gida suka nufa harda Haroon suna tattauna maganar wani aikin dayake hannunsa na fito da yaran BB da tsautsayi yasaka aka kama dayansu sbd wani aikin boyen da yayi musu.

Suna gama maganar dagowa Dad yayi ya Kalli Haroon Yana karantar yanayinsa tsawon mintina kafin yace

“Meyake faruwa ne da Jamaal Bayan gobe ne daurin aurensa??
Akwai wani matsalan ne Daya kamata na sani?
Menene yake faruwa?

Dad Lameenu ma zubawa Haroon idanuwansa yayi Yana kallansa Dan Jin Abinda yake faruwa da Basu saniba.

Dagowa Haroon yayi ya Kalli dad din Yana Jin jikinsa na sanyi,
Numfashi ya sauke ahankali kafin ya sake dagowa cikin sanyin murya yace

“Jikin fadila ne yayi tsanani sosai,
Mum ma ko bayan isowanta jiyan Saida ta dubata sosai karshe ma a asibiti suka kwana akanta Amma dai angano matsalar daga oxygen data amfani dashi yayi mata mummunan illa Kuma abin tashin hankalin shine oxygen da ita kadai take amfani dashi ne aka gurbata da wani abin Amma dai mum tana kan binciken zasu gane Menene”

Dad Lameenu wani numfashi ya hadiye ya koma masa ciki kafin ya Dan juya ya Kalli Mam Wanda Babu abinda yayi
kafin yayi wata magana Mam din ya rigasa da Bude Baki a natse yace

“To shi Jamaal din yasan da Hakan?
Yasan me sakamakon ya bayar?

“No sai sauran results din sun Hadu zuwa gobe mum zata sanar masa”

Wani sanyayyar numfashi Mai hade da bayyanarda alhini da tausayi Dad Lameenu ya sake
Shikuwa Mam har lokacin Bai nuna kowanne irin yanayi ba sai shiru da yayi kafin ya sauke karamin numfashi Yana Mata fatan samun lafiya ya sallami Haroon din ya fice yabarsu.

Tinda ya fita babu Wanda yayi magana a cikinsu sbd zuwa yanzu da suka manyanta kowa yagama sanin tinanin da kowa keyi a kowanne lokaci wani abin ya taso.

Jamaal Bai dawo gida ba sai dare sosai bayan ya baro gidansu fadila jikinsa a matiqar mace Dan yau fadilan da kanta take kuka tana rokon ya mata alluran da zata rasa hankalinta Dan ta Dena Jin Abinda takeji zuwa safe.

Iyayenta kuka sukeyi da Hawaye a gabansa na tausayinta
Duk wata karfin zuciyarsa Saida kukan fadilan ya karya masa shi.

A goben da zaa daura masa aure da ita a goben Inshallah zasu bar kasar sbd komai na tafiyan ya kammala goben ne ranar tafiya.

Mum dinsa ma jikinta mutuwa tayi da yanayinsa Dan haka Bata takurasa sosai ba akan abinci,ice tea ta hada masa kadai ya Sha ya shige bedroom dinsa.

Wanka yayi ya kwanta Kai tsaye Yana rufe idanuwansa wani nauyi na karuwa a zuciyarsa.

Karfe uku na tsakar dare Haroon ya fito daga bangarensa cikin tashin hankali da damuwa me tsananin gaske ya nufo part din Jamaal da wayarsa a hannu yayi knocking.

Knocking yakeyi sosai Amma Sam Babu alaman ma suna jinsa Dan haka ya cikin tashin hankalinsa Dake karuwa ya Kalli wayarsa Dake sake ringing Kiran siddeeq Yana shigowa..

Juyawa yayi kawai da sauri ya koma dakinsa cikin gaggawa da rawar jiki ya Dora jacket babba akan sweatset din Dake jikinsa ya zari keys din motarsa ya fito.

Baiyi wata wata ba ya fada motan ya tayar cikin zafi yayi wani mugun horn dashine ya tayar da Dad dinsu da shi kansa Jamaal din harma da mum dukkaninsu a tare suka tashi zaune suna sake Jin horn din a kunnensu sosai.

Time kowannensu ya kalla cikin mamaki Mai girman gaske.

Ziro kafafunsa daga gadon Jamaal yayi tareda saukowa Yana nufar window na dakinsa ya ware curtain Yana kallan harabar gidan daidai motar Haroon din na ficewa daga gidan cikin wani irin gudu me zafin gaske.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected